← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 167

Sashe 54

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dama addininku ya yarje maku da haka?" Jay ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace "Kayi hakuri ka gafarce mu Abba, she will be rounding up her exam on Tuesday, and she will leave in sha Allah" Abba yace "Kaga da ba don nasan baza ka min karya ba Ahmad i won't listen to you, da Junaid ne ya tsaya mun wannan bayani bazan yarda da shi ba, and my plan was to start making arrangement na samar masa mace da zan aura masa a kai masa ita can
asar, tunda ka min wannan bayanin naji na kuma yarda amma daga kai har shi sati biyar na baku kacal ku gabatar min da macen da za ku aura, ita kuma i will send you some money to sort out her House rent" AJ ya daga kai yana kallon Jay bayan yaji abinda Abbansa yace, sai kuma ya mike kamar zai tashi sama ya bar wajen, shi dai Jay was speechless this was the least thing he was expecting to hear from Abba, jin Abba ya katse wayar ya zuba ma screen din ido, ya basu 5 weeks?? jay ya fi minti goma zaune a wajen kafin daga karshe ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya dau wayarsa ya shiga cikin gida.

The next day Khaleesat suka gama jarabawansu na karshe and she was so happy amma kuma da ta tuna wasu abubuwa kawai sai mood dinta ya canza, suna zaune tare da Safiyyah a cikin makarantar ganin yanayinta da yanda ta sauya lokaci daya tayi shiru, Safiyyah ta kalleta tace "Why are you like this Khaleesat?" Khaleesat ta daga kai ta kalleta, a hankali tace "I don't have the means of going back to Nigeria Sophie, the burden i am placing on my Housemate is too much ba shi ya kawo ni kasar nan karatu ba, he knows nothing about me, don me zan yi ta dora masa nauyina har haka?" Safiyyah tace "To ya za kiyi Khaleesat, tunda ba ke kika rokesa ya maki ba ai kawai addu'a zaki masa Allah ya saka masa da alkhairi, he is ur God sent Angel, ba gashi with or without Abdul kin gama jarabawanki lafiya ba" Khaleesat ta sauke idonta jin hawaye ya ciko mata, Safiyyah ta hade rai tace "To meye na kuka kuma?" Muryarta na rawa tace "Ni dai bana son yace zai sake kashe min kudi masu yawa in koma Nigeria, i am feeling guilty" Safiyyah ta wani kalleta, can tace "Kya rube a kasar nan kuwa, ke kina da hanyar komawa ne?

Ko kuma aikatau zaki nema a kasar ki tara kudin komawa Nigeria?

In ba dai kudaden Abdul dake account dinki zaki yi using ki biya kudin jirgi ba" Safiyyah na kai wa nan ta kyalkyale da dariya tace "Ko ya kwashe en kudaden nasa ne?" Ita dai Khaleesat tayi shiru taki ce mata komai, Safiyyah tayi dariyarta me isarta sannan tace "Allah ba batun wasa ba, ya kwashe kudaden nasa ne?" Khaleesat ta girgiza kai a hankali tace "Suna nan" Safiyyah tace "Miliyan nawa ne ma?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Almost 9.5 Million" Safiyyah tace "To kawai ki siya Ticket abunki tunda dai yasan ba uban wani gareki a kasar ba da zai baki kudin komawa Nigeria ba, bayan shi kawo ki, in nice ke ma har shopping sai nayi na komawa Nigeria a cikin kudin wallahi, ai bazai san kin ta
a ba tunda ba shi ke ganin alert ba" Safiyyah na dariya ta kare maganar, ita dai Khaleesat bata tanka ta ba, Safiyya tace "Naji kinyi shiru ko baza ki ta
a ba?

Wallahi yanzun nan in raka ki shopping mu fatattake kudin" Khaleesat tace "Ai ba nawa bane da zan fatattake su" Safiyyah ta kwashe da dariya tace "To ai sai kiyi ta zama a kasar, dama gulma ce yasa kika kawo maganar ba wani abu ba don nasan Jay kike saka ran ya biya maki ticket" Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take ta kasa ce mata komai, amma ita kadai tasan abinda take ji a zuciyarta, Safiyyah tace "In kuma in ma Ya Musty magana to, don dai Economy class ticket da zai siya mana bazai ce ya gagaresa ba" Da sauri Khaleesat tace "A'a, zan yi amfani da kudin account dina" Safiyyah tace "Atoh dai" Khaleesat ta gaya mata haka ne kawai don bata son taje ta ma Ya Musty magana....

Jay ne ya zo daukansu a schl din as usual, sai da ya fara dropping din Safiyyah sannan ya kama hanyar gida da Khaleesat, daxun nan yaga Abba ya sako masa dala dubu goma wai na House rent dinta, da ya gaya ma AJ sai cewa yayi ya masa transfer din Dala dubu biyar shi ma ya rike dubu biyar din tunda ba su suka kawota kasar ba, shi da Jay bai tankasa ba, Jay dake driving ya
an kalli Khaleesat jin shirun yayi yawa, yaga alamar tayi nisa tunanin da take, sai a sannan ya kula da idonta da yayi ja, a hankali yace "Halysaah" Juyawa tayi ta kallesa trying to look alright ta
an yi murmushi tace "Na'am" Yace "Are you okay?" Tayi yake tace "Na gaji ne kawai" Jay yayi shiru, bai sake ce mata komai ba amma yasan ba gaskiya ta fada masa ba, a
an few months din da yayi da ita har ya gama studying dinta gaba daya, he knows when she is happy, sad, bored, disturbed, and even tired, wannan karan yaga damuwa ne karara a fuskarta, ya dai ci gaba da driving dinsa har suka isa gida, bayan yayi parking ya juya yana kallonta, a hankali yace "Me ke damunki Halysaah?" Duk kokarinta na ganin ta nuna masa ba komai hakan yaci tura, don kawai ita ma gani tayi kuka ya taho mata, Jay ya jinginar da kansa da kujeran motar bai ce mata komai ba, kwana biyu ya huta da kukanta don a sanda ya dawo da ita gidan rana daddaya ne bata kuka don ma Safiyyah na taka mata burki kuma ya ga tana
an jin maganar Safiyyar wani lokaci, sai da tayi kukanta me isanta sannan yace "Sauka mu shiga ciki to" Ba musu ta bude motar ta sauka tana goge idonta, shi ma ya sauka, yana gaba tana biye da shi suka shiga cikin gidan.

Khaleesat na kwance da yamma ta shiga Hisnul Muslim dake wayar Jay sai ga kira ya shigo wayar, a hankali ta mike zaune tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren taji yace "Kin tashi?" Tace "Uhm" Yace "Kin yi sallah?" Tace "Nayi" yace "Ohk will you mind going out to the park with me?" Khaleesat tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Ohk, thank you" Yace "You are welcome, i will be waiting for you at the parlor downstairs" Tace "Ohk" After almost 15 mins Khaleesat ta sauko downstairs cikin shiri, sosai kayan jikinta yayi mata kyau sai dai ta rame sosai, shi kadai ne zaune parlon yana jiranta, tun da suka hada ido ta sunkuyar da kanta, ya mike ya jira har ta iso parlon yana kallonta, a tare suka fita zuwa parking space din gidan ya bude mata motar, ta
an kallesa tayi murmushi tace "Thank you" Ya bude ido yace "No thanks" bayan ta shiga ya kulle motar sannan ya zaga ya shiga driver seat, one of the best park na state din ya kai ta and she love everything about the park, the view was so fascinating and breathe taking, she felt so refresh and relieve taji kamar bata da wani damuwa a lkcn, Jay ya siya masu Wraps da fresh lemonade, wannan karan bata ji kunyar cin abinci gabansa ba, lkci lkci yake daga kai ya kalleta, ita dai ta dinga kallon feral horses dake park din from a far distance, can ta kallesa tace "Su ba a hawansu ne?" Yayi murmushi ya girgiza mata kai yace "Ba a hawa" Tace "And nobody is controlling them?" Yace "Sort of, they are just on their own with no supervision, ko kina son in kai ki inda zaki hau doki ne?" Er dariya tayi ta girgiza masa kai kawai, ya
an kalleta, kana ganinta kasan tana cikin farin ciki a lokacin, ta kalli wraps dinsa da bai karasa ci ba tace "You are not eating?" Yace "Za ki ci ne?" Tayi murmushi tace "A'a, na koshi, kawai naga baka ci da yawa bane" Yace "Na ci abinci daxu ne, i am full" Ta kalli lemonade din gabansa tace "To in dauka?" Yace "A karo maki wani kenan?" Ta girgiza kai da sauri tace "Aa fa, i just don't want it to waste ne" Ya dauki sauran lemonade din nasa ya ajiye mata a gabanta yana kallonta, ta dau straw din ta fara shan lemonade din a hankali, dauke ido yayi daga kallonta, wayarsa ya fara ring yana dubawa yaga AJ ne ke kiransa, yayi picking ya kai kunne, ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, after few seconds Jay yace "Ni sai next week probably, ban gama abinda nake ba, do not book with me" Ajiye wayar yayi bayan AJ ya katse, ya kalli Khaleesat yace "Zaki jira har next week mu tafi Nigeria, or you will leave before then?" Khaleesat tayi shiru at first, a hankali ta sauke idonta tace "Yanda kace" Yana murmushi yace "Ko zaki bi AJ, he is leaving soon, yanzu ma ticket zai yi booking" Ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, sai kuma tace "He that dislikes me shi ne zan bi sa?" Jay yayi dariya yace "How will you say he dislikes you Halysaah?

He dislikes you shi ne yaje har apartment dinki yayi rescuing dinki?
Chapter 54 · 0% Book details