← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 167

Sashe 55

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ke ce dai baki ganesa ba har yanzu, AJ is nice just that yana da son girma ne kuma baya son raini, which i understand him because that's our heritage, kinga ke ko gaishesa baki yi" Tana wasa da straw din lemonade din gabanta tace "To ai nasan ko na gaishesa bazai amsa ba, saboda na ta
a gaishesa bai amsa min ba" Jay dai yayi murmushi yace "In kin ci gaba da gaishesa ae zae amsa" Tace "Ur frnd doesn't like me at all, he prefer my frnd" Jay yace "Who told you he is my frnd?

AJ is my cousin bro Halysaah" Khaleesat ta daga kai ta kallesa tace "Da gaske?" Yayi murmushi yace "Ba ma kama ne?" Khaleesat ta buda hannu tace "Ni ban wani san yanda fuskarsa yake ba ai, ban ta
a kallonsa sosai ba" Jay yayi dariya, a hankali yace "To cousin brother dina ne, His dad is my father's junior bro" Khaleesat tace "To amma dai ka girmesa ko?" Jay na murmushi yace "Not at all, just 3 months ne tsakaninmu, we will clock 34 next year" Khaleesat tace "Shi ne yace ya haifeni?" Jay bai san sanda yayi dariya ba sosai, sai kuma yace "Zolayarki fa yake, but how old are you?" Ta sauke idonta kasa kamar bazata ce komai ba, sai kuma a hankali tace "I am 20" Jay ya wara ido yace "Waw, you are still a Baby Halysaah" ta wani kallesa, yana murmushi yace "To ai in AJ mace ne kuma an masa auren wuri ya isa ya haifeki" Yana dariya ya kare maganar, Khaleesat dai taki cewa komai still playing with the straw in front of her, a hankali Jay yace "Are you angry?" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma tayi murmushi ta girgiza masa kai still looking at him, Jay ya kwantar da murya yace "U misunderstood AJ, yana da kirki sosai, kuma yana da tausayi, just that he is a no nonsense kuma baya son raini, sannan truly yana da girman kai na sani, but that doesn't make him bad, kuma da kinsan wanene shi zaki san yana ma da saukin kai" Khaleesat ta karasa shan lemonade din gabanta taki ce ma Jay komai, Jay ya kalli agogon wrist dinsa yace "Let go for horseback riding before it gets late" Khaleesat ta zaro ido tace "A'a ni dai bazan hau doki ba" Yana murmushi yace "To mu je dai" Shi ya fara tashi sannan ita ma ta mike suna tafiya a tare, satan kallonsa tayi suka hada ido ya ciro wayarsa yace "Let's take some pictures with this beautiful view" A hankali tace "Ok" Tana tsaye kusa da shi yayi masu hoton da wayarsa, yana kallon hoton da yayi masu ya ta
a hancinsa yace "Ya naga hancinki yafi nawa tsayi, ya naga kamar kin fi ni kyau" duk lokaci daya ya jero tambayar yana sake kallon hoton da kyau, ita dai Khaleesat tayi murmushi tace "Uhm is that an irony?" Jay yayi dariya yace "I am serious Halysaah" Wata er Africa ce ta zo wucewa ya mika mata wayarsa politely yace ta masu hoto pls, yarinyar ta amshi wayar zata masu hoton, yanda Khaleesat taji ta uncomfortable kusa da shi, shi ma dai kamar hakan ne cause he left a little gap between them, yarinyar ta masu hotuna masu kyau kuwa, ita kanta yarinyar sai kallon hoton take kafin ta mika ma jay wayarsa tana kallon Khaleesat admiringly tana murmushi tace "You are so Beautiful" Khaleesat ta sauke idonta tace "Thank you" Yarinyar ta daga masu hannu ta bar wajen, bayan Jay yayi mata godiya, kallo daya yayi ma hotunan ya mayar da wayar cikin aljihunsa yace "Let go for horseback riding Housemate" Wani park din ya kai su daban da ake hawa doki, duk yanda yayi da Khaleesat ta hau doki bayan ya biya masu kudi taki wai ita bata iya ba tsoro take ji, daga karshe ta marairaice tace "Ni dai kawai ka bani wayarka in dinga maka video sai kai ka je ka hau" Yayi murmushi kawai ya mika mata wayarsa yace "To ai shikenan" Khaleesat was so impressed with his horse riding skills kamar irin dama ya saba din nan, sai murmushi take masa, mutanen wajen ma suna ta kallonsa, Khaleesat's eyes were glued to him all through, tana yi tana masa video, sai after 7 suka bar wajen, tana kallonsa kafin su shiga mota tace "Where did you learn to ride horse confidently?" Yayi dariya yace "Back home" Tana murmushi tace "To ka ta
a zuwa nan ne?" Jay yace "Tab ai nan wajen zuwan AJ ne, kawai dai of recent ne muka dena zuwa" Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, sai da ya fara biyawa African Restaurant ya siya mata abinci, ganin leda daya ya mika mata yace "This is for you" Tace "Kai fa?" Yace "No, i am taking tea and bread this night" A hankali tace "Ohk, thank you" Bayan sun isa gida yayi parking, ta juya tana kallonsa a hankali tace "Thank you so much, Allah ya saka maka da alkhairi, i appreciate you" Without looking at her yace "Amma nace ki dena min godiya ko Housemate?" Tayi shiru, ya bude motar ya sauka sannan ita ma ta sauka, yana gaba tana biye da shi har suka shiga gidan, AJay na zaune parlor yana shan fruit salad yana kallon kwallo, ya juya ya kalleta don shi bai ma san bata gidan ba, suna hada ido abinda Jay yace mata daxu ya fado mata, ta sunkuyar da kai, kamar munafuka tace masa "Good evening" AJ ya gyara zama yana kallonta yace "Kin saba gaisheni ne zaki ce min Good evening??" Khaleesat ta
an kalli Jay da ya karasa cikin parlon, Jay yace "Good night Halysaah, if you need anything you call my line" A hankali tace "Thank you" Daga haka ta wuce sama, Jay na kallon AJ yace "Ba don na mata magana ba kana tunanin zata gaisheka ne dama?

Ni ne nan na saka ta, sai me kuma in baka amsa ba?" AJ yace "Zamana take a gidan da zata gaisheni" Jay dai yaki tanka masa.
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
[5/26, 9:45 AM] khaleesat Haiydar
: Washegari Wednesday da yamma Jay na zaune parlon dake sama tare da AJ da ya maida parlon wajen kwanansa, don tun da Khaleesat ta kwana dakinsa tsakaninsa da dakin kawai ya shiga ya
dau kaya, ko bandakin dake dakin baya shiga, Jay dake kallonsa yace "Yanzu dai zan iya dawowa dakinka kenan tunda ka tashi a dakin?" AJ yayi banza da shi yana ci gaba da hada few kayansa da yake yi a tsadadden box dinsa da zai yi tafiya gobe, Jay yace "To wai kayi booking flight din ne da naga kana hada akwati?" AJ yace "Bana son Airline din da na gani jiya, anjima zan siya Ticket din Turkish Airlines" Jay yace "How many hours connection time for the layover?" AJ yace "Baya wuce 2 to 3 hours, ko ma bazai kai haka ba" Jay yace "Will you mind travelling same plane with my Housemate?

I just remembered I will be meeting my Mami at the UK, tare za mu koma Nigeria da ita daga can" AJ yace "Of course I will mind Jawwad, because my OCD will never allow me board the same plane with her, ga Airline kala-kala ka nemi wani ka siya mata ticket mana, what is my business with her da zaka hadani da ita sai kace ni na kawota America, there is this Airline na mance sunansa Economy class ticket dinsu naga is just 600 dollars, you can get her the ticket as the Good Samaritan that you are" Mikewa Jay yayi bai ce masa komai ba ya bar parlon.
Chapter 55 · 0% Book details