← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 167

Sashe 84

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Ni wallahi ban yarda wa ennan samarin basu san inda Khaleesat take ba, kina fa ganinsu kin ga 'ya yan masu kudi, dubi suturan da suka sa wa, ji motocinsu, sannan kalli fatarsu kalan ta yan hutu, in
fa muka yi sake Shatu bakin ciki ne zai kashe mu a gidan nan muna ji muna gani" Mama Shatu tace "Ke ma dai wallahi kin fiye gaggawa, sai kace kin manta me Malamin yace mana, duka duka ba yau muka kai masa kudin ba, to mu zuba ido ya fara aiki mana tukun" Mama Zubaida tace "Duk da haka dai gwara mu ma mu dinga yin namu ta bayan fage Shatu, kada mu sakankance mu bar malami da aiki shi kadai, ya kamata tun wuri mu san yanda za mu yi mu ankarar da Abdul abinda ke faruwa a gidan nan, don gaskiya na sha jinin jikina da wa ennan zaratan samarin, ke ki ga tulin kudin da suka ba Islam, sannan kalli uban kayan abincin da suka jibge jiya daga karshe don walakanci aka biyo mu da kwano uku uku da taliya bibbiyu da man gyada da manja, sai maggi leda bibbiyu ga mayunwata, ke kiji wai yau Zahra'u ce da tsam mana kayan abincin da aka jibge mata, bayan haka Allah kadai yasan nawa suka bata a daki tunda ba gaya mana zata yi ba, ga Nenne ma a gaban mu aka bata rafar kudi yan dubu dubu, anya bamu shiga uku ba Shatu?

Ni fa jikina yayi sanyi hankalina ya tashi, meye hadin su da Khaleesat din da har suke wannan hidima haka a kanta, mu ga 'ya yanmu a zube har yau babu mataya sai talla suke, ni fa wallahi ko tsirara zan yi yawo gwara inyi da dai Zahra'u da zuri'arta su ji dadi a duniya" Mama Shatu tace "Yanxu dai Gwaska za mu samu ya raka mu gidan su Abdul din tunda yace yasan gidan uban sa, nasan Abdul din zai taka ma yan iskan burki har ma ya bamu makudan kudi fallasa asirin abinda ke faruwa da mu ka yi" Mama Zubaida tace "Atoh dai tun wuri my gaya masa abinda ke faruwa, zuba ido ba namu bane wallahi, amma sai dai jibi kenan za mu je gidansu Abdul din don Gwaska ya tafi dambatta daxu uwarsa ke gaya min yaje kai kaya can" Mama Shatu tace "Ai jibin kamar gobe ne, kin ga gobe dama mu gama girkin mu da wuri mu tafi inda wannan matar ta mana kwatance daxu a gidan Malam" The next day wajen karfe biyar da rabi na yamma Sha'awa tayi sallama bakin kofar dakin Umma dake yi ma yan biyun ta gyaran gashi, babu kowa gidan don duk yan matan gidan basu dawo talla ba, kananun yaran kuma sun tafi gantali, tun Sha'awa bata shigo dakin Umma ba take cewa "Umma yanxu Ladingo ke sanar min an sako Gaje, wai daxu taje unguwan taga ana ta shiga gidan yi mata jaje" Umma ta sake gashin Noor ta mike da sauri tace "Da gaske Sha'awa?" Sha'awa tace "Wallahi kuwa Ladingo bazata min karya ba Umma, tace Gaje dai ta dawo gida ga yan unguwa na ta tururuwan shiga yi mata jaje tun daxu" Umma ta jawo Hijab dinta tace "To bari in je gidan Allah ya sa da gaske ne dai" Sha'awa tace "Da ina da kudin mota ai da mun je tare Umma, kusan kwanan ta biyar fa a kulle, don ma akwai kanwarta da zata kula da jikokinta tunda uwarsu na can Libiya ta tafi aikatau, ubansu kuma yayi watsi da su, banda haka da yaya makomar jikokin nan nata fisabilillahi?" Umma bata tanka ta ba ta gama saka hijab dinta ta daura nikab ta dau purse zata fita, Noor da Islam suka marairaice wai za su bi ta, ganin in ta tafi su kadai zata bari a gida yasa tace su saka hijab gaba daya, haka nan duk suka saka Hijab suka fita daga dakin Umma na biye da su, kusan kullum sai Umma taje gidan Gaje sau biyu ta duba ko ta dawo amma sai taga akasin haka sai dai ta samu kanwarta Iya a gidan, jiki a sanyaye take juyawa ta koma gida don Iya na ganinta take fara masifar ita ta saka er uwarta a uku, Umma zata fita gidan tare da yan biyunta sai ga su Mama Shatu da Mama Zubaida sun shigo wujiga wujiga da su, kana ganin fuskokinsu kasan a gajiye suke likis, ga wuyan hijabinsu duk yayi jagab da zufa, kafafuwarsu kuwa kamar wa enda suka dawo daga gona, Umma dai tayi masu sannu da zuwa kawai ta fita daga gidan su Islam na biye da ita, ai ko tana isa gidan Gaje taga da gaske an sako Gaje, Gaje na ganin Umma tayi kamar bata ta
a saninta ba a duniya, yanda take amsa gaisuwa da jajen masu shigo mata haka ta amsa ma Umma kamar ranan ta fara ganinta, ita dai Umma na zaune tayi shiru ta ma rasa me zata ce, su Islam na zaune gefenta, Gaje bata sake kallon direction dinta da yaranta ba, duk wanda ya shigo haka take sanar masa yanda Maman Fu'ad ta ci amanarta tace ma yan sanda ita bata ta
a ganinta ba ma balle wata Khaleesat, In tayi bayanin sai ta rushe da kuka tace "Ban ta
a tunanin Sadiyah zata min butulci haka ba duk alakar da ke tsakanin mu wai bata ta
a gani ba, kaji tsoron Allah kaji tsoron mutumin yau kawai, duk kyautata ma yarinyar nan da nake amma ta barni ni kadai raina a cikin matsalar da na tsoma kaina" Ita dai Umma tayi tagumi tana sauraron duk abinda Gaje ke cewa.
[6/9, 7:26 PM] khaleesat Haiydar
: Sai bayan da aka yi sallan Magrib Umma ta bar gidan Baaba Gaje da yan biyun ta, kuma har ta bar gidan Gaje bata nuna ta ta
a saninta ba don casually ma take amsa mata kamar yanda take ma kowa da ya shigo mata jaje, Umma dai a sanyaye ta baro gidan, tana isa gida taga mutane tsattsaye a kofar gida kowa da abinda ke fitowa bakinsa, sosai taji gabanta ya fadi gashi ta kasa fahimtar akan me ake ta surutu haka, can dai ta dubi wata makociyarsu dake tsaye wajen tace "Munnira me ke faruwa?" Munnira tace "Wallahi Umman su Khaleesah nima fitowa ta kenan da naji hayaniyar tayi yawa, amma wai kamar wasu mutane ne da ba a san ko su waye ba suka shiga gidan naku suka yi aika aika, ance a katuwar mota suka zo...." Umma ta kasa cewa komai tana kallonta, da kyar take jan kafa tana rike da su Islam ta shiga gidan har sannan gabanta bai daina faduwa ba, Su Mama Shatu da Mama Zubaida ta gani tsaye da 'ya yan su duk sun yi cirko cirko a tsakar gidan da makota ana ta maida magana, tsakar gidan dai cike yake da jama'a kowa na fadin albarkacin bakinsa, Umma ta dake tace "Wai me ke faruwa ne a gidan?" Mama Zubaida ta wani kalleta a walakance tace "Ina kuwa za mu san me ke faruwa tunda mu dai muna zazzaune sai ga wasu kattin gardawa sun kusa goma babu annuri a tare da su sun shigo mana gida da makamai suna tambayar dakin Malam, basu tsaya iya dakin Malam ba hatta sauran dakunan gidan nan sai da suka shiga..." Sai a sannan Umma ta lura da bakin kofar shiga dakin Malam Ali, gaba daya yayi kaca kaca da takardun da ta mayar daxu bayan su Jay sun dau wanda za su dauka, har kayan cikin dakin sai da aka watso su waje har da er katifarsa da akwatin kayan sakawan sa da butar alwalansa, Umma ta juya tana bin tsakar gidan da kallo taga har dakinta an fito da kaya an yi watsi da su waje, da kyar Umma ta karasa kofar dakin Malam Ali ta leka ciki taga basu bar komai ba, dama ba wasu abun kirki ke cikin dakin ba, can ta juya tana kallon Kishiyoyinta amma ta ma rasa me zata ce, Mama Shatu ta kyabe baki tace "Ni takaicina dakunan mu da suka shiga wai ina takardun da Malam ya ba mu ajiya, ni ko nace mu muka san wasu takardu mu da bamu yi karatu ba ta yaya Malam zai bamu takardu mu ajiye ai sai dai ko ya ba er sa da aka kai turai karatu daga karshe tayi ma wanda ya kai ta karatun butulci wai bata son sa kuma, amma ina mu ina ajiyar takardu mu da muke jahilai" Umma bata tanka ta ba ta duka tana tattara takardun dake watse bakin kofar su Islam suka je suna tayata, a haka duk ta maida kayan Malam Ali cikin dakinsa, su Mama Zubaida sai hararanta suke, can Mama Shatu ta kyabe baki tace "Mu dai mun san ko ma wani takarda suke nema bazai wuce yana da alaka da er ki ba kilan kotu za a shiga, tun da kika haifi yarinyar nan muke shiga jarabawa munana a gidan nan, ko kuma muce tunda aka auro ki, mu da bamu san wani talauci ba balle wahalar rayuwa, daga auro ki karayar arzikin da ba a ta
a yin irinsa a tarihi ba ya samu Malam, sannan gashi sanadin er da kika haifo ga abinda ya samu Malam a karo na biyu, daga ke har 'ya yanki babu wani abun alkhairi a tare da ku sai masifa, ina ma Malam zai yada kwallon mangwaro ya huta mu ma mu huta ki tattara ki koma can kasar ku ki auri buzu
an uwanki" Sha'awa dake tsakar gidan wanda tana daga cikin mutanen farko da suka shigo bayan Mama Zubaida da Mama Shatu sun kurma ihu, amma fa sai da gardawan suka fita sannan suka samu bakin ihun neman agaji su da yaransu, Sha'awa tace "Haba Mama Shatu, wannan wani irin magana ce kike yi haka don kin ga Ummansu Khaleesah bata tanka ku a gidan nan, wannan ai cin fuska ne, kar fa wataran ku kureta ayi dauki ba dadi a gidan nan, don mai hakuri bai iya fushi ba wallahi" Wani zagi Mama Shatu ta kundumo mata a fusace, Sha'awa ta rama tace "Wallahi ba dai ubana ba, sai ko in naki uban me gyaran keke dake kabari" Ganin fada na kokarin kaurewa a tsakar gidan Umma da wasu mata suka fitar da sha'awa dake kunduma ma Mama Shatu zagi ta uwa ta uba, ga su Labeebah na kokarin dambe da Sha'awa dake zagar masu uwa su ma duk aka rirrike su, a haka dai aka fitar da Sha'awa dake gyara daurin zaninta da ya kusa faduwa gashi babu komai kasan zanin, tana huci take cewa "Shegu en kutumar uba masu bin bokaye, ko jiya sai da aka bani labarin kun je wajen wani boka na kuma san warce ta raka ku, kun ga kuwa Umman Khaleesah ta fi ku ko a wajen Allah tunda bata san hanyar zuwa gun Malamai ba" A haka dai aka fitar da Sha'awa daga gidan, Umma dai jiki a sanyaye ta tafi kofar dakinta ta tarar su Islam suna ta maida kayan cikin dakin da aka watso waje bayan sun kunna er fitilar dake ba dakin hasken, Noor na kallon Umma tace "Umma kinga babu kayan abincin a inda suke" Umma ta kalli inda Maman Salame ta ajiye mata kayayyakin abincin da su Jay suka kawo taga wayam, tsayawa tayi tana kallon wajen babu ko kiftawa tsabar mamaki yasa ta kasa cewa komai, muryar Nenne taji a tsakar gidan cikin fushi tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, meye haka aka cika gidan nan kamar ana taron farin ciki?
Chapter 84 · 0% Book details