← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 167

Sashe 132

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To naji zan je amma ni ko minti talatin bazan yi ba a wajen" Safiyyah da fuskarta ke daure har lokacin tace "Naji, mu tafi gidan naki mu shirya" Khaleesat tace "Meye da kayan jikina da bazan je da shi ba?" Safiyyah tace "A'a wallahi a gan ki tun safe da kaya anjima kuma a sake ganinki wajen get together da shi?

Ni ma ga kayana da zan canza cikin jakan laptop dina, bari in mana order din Uber mu tafi gidan naki" Khaleesat dai ta tabe baki bata ce mata komai ba, Safiyyah ta gama order din ride din sannan ta mike har sannan tana rike da Khaleesat, Khaleesat tace "Ikon Allah, to ki sakeni mana ko guduwa zan yi?" Safiyyah tace "Na san maki?" Dariya kawai Khaleesat tayi a haka suka tafi inda za su jira Lyft dinsu, wajen karfe hudu suka isa apartment din Khaleesat, sai da suka yi sallan azahar sannan suka shirya, Safiyyah har da make up, Khaleesat dai ko powder bata yarda ta shafa ba, Safiyyah ta kyaleta da ba
in halinta don lallabata take kar ta canza mind dinta, a haka dai suka bar gidan wajen karfe biyar saura.
[7/8, 9:34 PM] khaleesat Haiydar
: Tun da suka iso gidan Coursemate dinsu Clara da aka yi organizing Get together din Khaleesat ta nemi waje a parlon ta zauna tayi isolating kanta totally daga cikin mutane don sun tarar har an fara taron ana ta nishadi, yawanci duk turawa ne sai few Africans da kuma student from other Continent, simple girke girken turawa da snacks iri iri ne a parlon sai drinks with so many chocolate, sannan ga tea with cookies, tuni Safiyyah ta shige cikin Coursemate dinsu ana ta shagali dama duk ta saba da su unlike Khaleesat da ba kowa take hulda da shi a department din nasu ba, lokaci lokaci Khaleesat ke kallon Safiyyah don a rayuwa idan akwai abinda ke saka Safiyyah farin ciki da nishadi bai wuce Chilling da partying with friends ba, har mamakinta Khaleesat take ko gajiya da harkar party bata yi, tana son life sosai ba kadan ba, bata ki a gayyaceta wani partyn gobe ba tsaf zata je, Khaleesat dai wayarta kawai take dannawa tana yi tana kallon agogo don dama tace minti talatin kawai zata yi, sai ga Safiyyah ta nufo tana washe hakora da glass din wine ta mika mata tace "Haba Khaleesat ki tashi ki shiga cikin jama'a mana ayi shagali da ke, sai tambayata suke if you are okay, ke in baki kunyata mutum ba baki ji dadi ba, ni dai ga glass din wine na kawo maki" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "A'a ni bazan sha ba, thank you" Safiyyah ta hade rai tace "Ke Non-alcoholic wine ne fa, sai kace ban san abinda nake ba, it's non alcoholic" Khaleesat tace "Na sani, kawai bana sha ne, kema kinsan drink ba wani damuna yayi ba" Safiyyah ta kyabe baki ta juya ta koma cikin yan ajin su, ba iya Coursemate dinsu kadai bane a wajen har da few masters student, wa enda suke Pursuing masters dinsu a course din da su Khaleesat ke Degree din sa, tun da Khaleesat suka shigo parlon dama ta lura da wani mutumi dake zaune shi ma yayi isolating kan sa a gefe yanda ita ma tayi, shi ma kuma wayarsa kawai yake ta dannawa da glass din wine a hannunsa, tana ganinsa ta gane bahaushe ne amma ta fuske a inda take a zaune, lokaci lokaci yake kallon direction dinta, kawai mistakenly ta daga kai suka hada ido da shi, ta maida kanta kasa tana danna wayarta with full concentration, mikewa yayi ya nufota har sannan yana rike da glass din wine, tana ganin alamar ya nufo inda take taki dago kanta har ya karaso wajenta, jingina yayi da bango daga gefen inda take zaune yana kallonta yace "Good evening" Ba tare da ta dago kanta ba a takaice tace "Ohk" Ya mayar da wayarsa aljihunsa yana kallonta yace "African?" Ta girgiza masa kai kawai, yace "But Safiyyah is your friend" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa a karon farko babu yabo babu fallasa tace "So???" Ya
an bude ido yana murmushi yace "Safiyyah that i know is from Africa, Nigeria precisely" A takaice tace "I don't know what you are talking about pls, because Safiyyah is my frnd doesn't mean we have to be from the same continent" Fuska daure ta kare maganar ta, calmly yace "Not at all, you sound provoked, sorry if u feel offended..." Mayar da wayarta tayi jaka with the intention of leaving the house gaba daya, sai ga Safiyyah ta nufo su da plate din cake a hannunta zata kawo mata, tana ganinsa tace "Ohh Aymaan, i didn't even notice you here, ashe ka zo" Ya gyada mata kai yace "Yeah, good evening Safiyyah" Tana murmushi tace "Evening Aymaan" Yace "Ya sunan kawar taki ne?" Safiyyah na murmushi tace "Ohh, her name is Khaleesat" Ya gyada kai yace "Ta ce min daga wani Continent din daban take not Africa, i saw she was sitted alone, shi ne na zo nan so we while away time together, but she took it personal, i think i wilk take my leave" Yana fadin haka yayi murmushi ya fara tafiya zuwa inda yake zaune, Safiyyah ta kalli Khaleesat tayi kasa da murya tace "Na shiga uku, yanxu kenan baza ki ta
a canzawa ba Khaleesat, ke baza ki koyi siyasa ba a rayuwar nan?

Meye ne don ya zo ya sameki? kin zata cewa zai yi yana son ki?

Ai shi kuma Aymaan ba haka yake ba, Masters dinsa ma yake shi yasa baza ki wani san sa a department din ba, he is the son of the Deputy governor of a state in Nigeria" Khaleesat ta wani kalleta tace "So??" Safiyyah tace "Maida wukar, nan da kika gansa ma ba lafiya garesa ba, chronic ciwon zuciya yake battling with, you think he have time for any relationship aside friendship?

Beside iyayensa ma sun masa aure yana da mata haka da kika gansa, kawai don ya gan ki zaune shi ne ya zo to keep you company amma ba wani abu ba, kuma da aka yi inviting dinsa get together din ma yace bazai zo ba, nasan Nora ce ta takurasa ya xo, ita wai son sa take kamar zata yi yaya, ko me zai yi da baturiya, ke kuma ki sha kurumin ki ba cewa zai yi yana son ki ba he is Married..." Khaleesat dai bata ce komai ba, can ta kalli Aymaan din taga ya koma inda yake zaune yana danna wayarsa kawai sai taji wani iri a can kasar zuciyarta, sai take jin kamar bata kyauta ba yanda tayi shunning dinsa kamar jiransa take dama, Safiyyah ta tabe baki ta mika mata plate din cake din hannunta tace "Ni dai ga shi, kuma ki taso za mu yi hotuna, in shi ma din baza kiyi ba sai mu ji...." Khaleesat ta amshi plate din ta ajiye duk da ba ci zata yi ba amma kawai jaraban Safiyyah ne bata so yasa ta amsa.

Haka nan Khaleesat babu yanda ta iya ta tashi za su yi hotuna da Coursemate dinta, yawancin su duk shakkar interacting da ita suke don ko murmushinta baka gani a department balle dariyarta, bata kuma kula kowa sai dai gaisuwa shi ma sama sama saboda Safiyyah, tunda Safiyyah kowa nata ne, yawanci duk hotunan da suka yi Ayman yana ciki shi ma kuma sai da aka je aka gayyatosa ya zo ayi pictures, daga karshe ya mika ma wani abokinsa wayarsa yace yayi masu hoto da Safiyyah, ita dai Khaleesat na tsaye gefe kamar bata ma san abinda suke yi ba nan kuwa slightest opportunity take nema da zata fita daga parlon ba tare da Safiyyah ta lura ba, abokin yayi masu hoto da Safiyyah tana washe hakora as usual, sosai kuma hoton yayi kyau, sai kuma ya mika ma Safiyyah wayar tasa yace "To yi min da kawarki, Khaleesat ko?" Safiyyah na murmushi ta amshi wayarsa da yake mika mata tace "Eh, her name is Khaleesat..." Komawa yayi kusa da Khaleesat ya tsaya yana kallonta yace "Let take a snap Khaleesat" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, amma da ba don abinda Safiyyah ta gaya mata a kansa ba da babu abinda zai sa ta tsaya wani yin hoto da shi, fuskarta babu yabo babu fallasa take kallon Safiyyah da ta saita waya zata masu hoton, Safiyyah ta wani kankance ido tana kallonta alamar ta saki ranta mana, kamar irin uwarta din nan haka tayi mitsi mitsi da ido tana kallonta, Khaleesat bata sanda tayi dariya ba don ba karamin dariya Safiyyah ta bata ba, Safiyyah tayi using wannan Opportunity din tayi snapping dinsu pictures kusan biyar tare da Aymaan, shi dai Aymaan kallon Khaleesat yake don bai zata tana dariya ba, abokansa biyu ma suka yi joining hoton, da wasu turawa, a haka Safiyyah ta gama masu pictures din ta mika masa wayarsa, yayi murmushi yace "Thank you Safiyyah" Safiyyah tace "Bari in sa maka numberna ka min sending pictures din pls" Ya bata wayar yace "Alright" Take away Safiyyah tayi ma Khaleesat ganin bata ci komai ba a wajen, Khaleesat dake ta kula da agogo tana ganin karfe bakwai da kusan rabi tayi ordering ride da zai maidata gida ba tare da Safiyyah ta sani ba, ride din na isowa cikin dubara tayi sneaking ta bar parlon without letting Safiyyah notice her.
Chapter 132 · 0% Book details