← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 167

Sashe 90

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Khaleesat na zaune at the far end of the large room ta hade kanta da gwiwa, zuwa sannan ta hakura da kukan da take don ba ma ta da strength din kukan amma tana jin zuciyarta na mata zafi ga wani azababben ciwon kan da take ji da kishin ruwa da ya dameta, tafi awa sha biyu zaune a dakin ba ci ba sha, don tunda aka shigo da ita har zuwa sannan babu wanda ya sake zuwa dakin, infact bata ji motsin kowa a gidan ba alamar ita kadai ce a ciki, bandakin dake cikin dakin take shiga tayi alwala ta fito tayi sallah duk da ba sanin lokaci tayi ba kawai tana amfani da instinct dinta ne, at this point in time tasan bata da wani sauran gata sai wajen Allah, domin kuwa tasan Abdallah ne kawai zai sa a zo ayi mata irin wannan daukan, wasu hawaye masu zafi suka zubo idonta tana tausayin rayuwarta, all she could remember vividly was that tana bakin rijiyan dake kusa da gidansu Aunty Farida tana diban ruwa wasu mutane biyu suka zo a mota, lokaci daya kuma suka yi leading dinta zuwa motar tasu, at first turje masu tayi ta fara kokarin raising alarm tana ihu, yaran dake bakin rijiyan duk suka gudu suka shige gidajensu, tana kururuwa daya mutumin ya rufe fuskarta da wani Handkerchief da sauri, taji ta sha
i wani abu kamar dust, lkci daya kuma ya cire handkerchief din a fuskarta, daga nan kuma ko kokarin ihun bata sake yi ba cause she became weak, ita dai tasan all through the ride she was conscious but not fully, gashi ta kasa tabuka komai don duk jikinta ya mutu, kanta yayi mata nauyi idonta suka dinga juya mata....

Da sauri Khaleesat ta dago kanta ta mike tsaye jin ana
arin bude kofar dakin ta waje da makulli, gabanta ya dinga bugawa da karfi idonta na kan kofar har ya bude ya shigo, she wasn't expecting anyone but him dama, ta sauke kanta bayan sun hada ido, wasu sabbin hawayen suka fara zuba idonta, muryarsa taji ya daki kunnenta cike da isa da gadara yace "Har yanxu Body guards din naki basu biyo bayanki bane?

Ai yaci ace sun iso zuwa yanxu don naga It's almost 12 hours now, how comes basu zo cecen ki ba duk capacity din su" Sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kallesa cikin rawar murya tace "Ka ji tsoron Allah...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da matsanancin kukan takaici, shi dai yana tsaye yana kallonta da wani murmushin mugunta kwance fuskarsa, ta dago kai da sauri jin yana takowa har zuwa inda take tsaye, mannewa tayi da bango tana jin kamar bangon ya tsage kawai ta shige gabanta na bugawa da karfi, sai da ya zo dab da ita cikin kwantar da murya yace "Me kika ce?" Ta girgiza masa kai da kyar gabanta na ci gaba da faduwa muryarta na rawa tace "Kaji tsoron Allah Ya Abdul, kaji tsoron...." Bata rufe baki ba taji saukan lafiyayyen mari a fuskarta wanda sai da taga taurari, ta dafe kuncinta tana kallonsa babu ko kiftawa, cikin husky voice dinsa yace "You still have the guts to repeat what u just said saboda baki da kunya ko?

Ni zaki gaya ma in ji tsoron Allah?

To tsoronki zan ji ko tsoron uban ki dake Mariri idan ban ji tsoron Allah ba?" Da kyar Khaleesat ta dake tace "Ka zageni amma kar ka sake zagar min uba" Still bata rufe baki ba ya sake sauke mata wani wawan marin a other side of her face, this time around sai da dakin ya juya mata don ba marin wasa yayi mata ba, ya fixgota yana mata wani irin kallon da ya gigitata don tuni idonsa yayi jajur yana huci yace "Ina magana kina mayar min how dare you poor wretched girl?" Ta fashe da matsanancin kuka tana jin dama Allah ya dau ranta kawai ta huta a wannan lokacin, zata durkusa kasa ya hadeta da bango yace "Yau ina body Guards din naki dake goya maki baya kina min iskanci?

Tell me where they are today?

Da aurena a kanki kike hulda da wasu banzayen gardawa saboda ke jahila ce warce bata san me take ba" Tana kuka sosai bata san sanda tace "To wai ana aure dole ne dama Abdul?

Nace bana son auren, bana son ka, gwara kawai ka kasheni duk mu huta" Da karfi ya bugata da bango har sai da taji numfashinta ya dauke na few seconds, yana mata wani mugun kallo yana huci yace "Dama ke baki san aurena wajibi ne a gare ki ba ko kina so ko ba kya so?

Dama shi ubanki bai gaya maki hakan ba ko mantawa kika yi saboda kin fara bin maza?

Wallahil Azeem kin ji rantsuwar musulmi ko?
Chapter 90 · 0% Book details