← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 167

Sashe 154

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

To ya zo ya dokeni tunda ni statue ne, ina ga shi ko gidan dambe bai ta
a zuwa ba, ki je ki tambayi wanene ni a Lagos..." Khaleesat ta maida box din zobenta cikin jaka sannan ta mike ta amshe wayar Safiyyah dake hannunsa, ta dau jakar Safiyyah da nata ta fara janta su bar wajen, banda zagi babu abinda Safiyyah ke kunduma ma Abdul idonta rufe tana cewa "Munafuki kawai algungumi, wato saboda ka san tana da tausayi shi ne ka dawo sumui sumui da kai kamar na Allah zaka kara yaudaranta ka cuceta, har kana cewa ta rufa maka asiri, to kuwa sai na tona asirin nan naka wallahi, shegen duka za ayi maka da zai sumar da kai, in ka farfado ka siya ticket ko koma gida kayi jinya, tsabar baka samu daman ci gaba da musguna ma kawata ba har da rama sai da kayi kamar me ciwon Aids, to wallahi in baka fita harkar Khaleesat ba sai nayi maka abinda har ka koma ga Allah bazaka manta ba, mugu azzalumi kawai" Gaba daya attention din mutane ya dawo kansu a wajen, Abdul yayi wani murmushi yace "Sai kinyi regretting duk kalaman nan naki wallahi, sai na sa an lalata maki rayuwa i promise you this...." Khaleesat dai ta samu ta ja Safiyyah suka bar wajen gaba daya, banda rawa babu abinda jikinta yake yi don tsoro, Safiyyah ta warce hannunta tana kallonta a fusace tace "Kin dai ga
an iskan da kike tausayi ko? ashe da sabon salo kawai ya dawo don ya samu attention din ki, ke kuma ga sarkin masu tausayi, to kuwa rabon a karyasa yasa ya dawo Amurka don wallahi Ajay karyasa kawai zai yi" Khaleesat ta zauna ta rufe fuskarta da hannunta tana kuka a hankali, gaba daya ta gama tsorata, ta ma rasa wani irin tunani zata yi, zaman apartment din nata ita kadai ya fara bata tsoro kuma, can ta kalli Safiyyah dake ta bambami cikin rawan murya tace "Sophie ko dai in ma Ya Musty magana da kaina ki dawo apartment dina da zama tunda exams za mu fara?

Wallahi bazan iya zama ni kadai ba kuma a gidan nan Sophie, i am afraid..." A fusace Safiyya tace "Ai baki zama afraid ba tunda har kika iya boye kasungumin
an daba a gidanki ya kwana, Abdul har abun yarda ne bayan duk mun san
an iska ne shi?

Wani dadin baki zai maki har ki yarda da shi?

Kin dai ga abinda yayi min ai yanxu, dama kuma me hali baya ta
a fasa halinsa" A hankali Khaleesat tace "To ko dai in yi ma Ajay bayanin abinda ya faru jiya kar ya zo ya gano yaji haushina?

Wallahi i am so confuse Sophie" Safiyyah tace "To nima naji haushin ki balle Ajay da yayi gadin ke da Abdul ku ka sharbi baccin ku? ai wallahi kin cuce Ajay kuma sai Allah yayi masa sakayya" Khaleesat ta goge hawayen gefen idonta tace "To amma sai dai inje can gidan nasu in masa magana ko?

Don kar yaje yayi misinterpreting dina ta waya idan na kirasa, i want to explain to him ta yanda zai gane" Safiyyah tace "Dama ai gwara ki samesa face to face kiyi masa bayani, sannan kar ki kuskura ki ce masa a gidan Abdul ya kwana don daga nan zai fatattake ki ya kora ki, ko ya hadaki da karensa ya kora ki, inda Ajay ke burgeni kenan wallahi, no nonsense Man kike ji, sam baya daukan wargi, tsayayyen namiji kenan, kawai ce masa zaki yi kin shiga kitchen zaki zuba abinci sai kika ga kamar Abdul a jikin window din kitchen dinki yana kallonki, shi ne duk kika rude kika kirasa jiya da daddare, daga baya kuma kika ga wajen wayam ba kowa, amma da ya zo sai baki gaya masa hakan ba tunda baki tabbatar ba kin zata hallucination kawai ki ke yi don dama kanki na ciwo jiyan, sai ki ce masa yau kina department muna zaune ni da ke kawai sai ga katon a gabanmu, ashe jiya shi din dai kika gani a jikin window, kinga ai maganata tayi making sense akan ki ce masa ai boyesa kika yi a daki jiya...." A hankali Khaleesat tace "To bari inyi order din Uber zuwa gidan" Safiyyah tace "Sannan idan kin je gidan ki fara masa godiyan gadin ki da yayi jiya ya hana kansa bacci, don nasan ba hankali gare ki ba kina iya zuwa ki fara maganar da ya kai ki kanki tsaye...." Khaleesat ta ciro wayarta za tayi order din Uber da zai kai ta gidansu Ajay, kafin tayi order din ta kalli Safiyyah tace "Ko zaki rakani mu je mu biyu?" Safiyyah ta rike ha
a tace "Wa??

Ni?

Salon inje ya koro ni mutumin da ba kirki ne da shi ba, a'a wallahi bazan je ba, ko kadan bai ta
a burgeni ba dama ni, tun farko tamu bai zo daya da shi ba don na tsani mutum fitinanne, da dai Housemate ne sai in bi ki mu je, kuma banda ma yafi Housemate zafi me zai sa ma a sako sa cikin wannan case din, to tsorona muna iya sako Housemate yaje ya fara ba Abdul din hakuri kinga ai lamari ya lalace kenan, babu dai yanda muka iya Ajayn zaki je ki sama duk da mugun halinsa, ayi mutum ace bai son mutane kullum yayi ta daure fuska yana fushi shi kadai" Khaleesat na kallon Safiyyah cikin sanyin murya tace "Ko dai kawai in gaya ma Housemate in kyale Ya Junaid din?" Safiyyah ta wani hade rai tace "Wani Housemate, hakuri kike son ya tafi ya ba Abdul din kenan yanda zai ji dadin ci gaba da iskancinsa, ai karki kuskura ki gaya ma Housemate he won't help matters at all, gwara Ajay no nonsense, tsaf zai mana maganin Abdul, amma Housemate ai har durkusawa sai ya iya yi ya ba Abdul din hakuri yanda suka yi ma Aymaan shi da Ya Musty, Ajay ai shi ne namiji" Khaleesat dai bata ce mata komai ba tayi order din ride din, Safiyyah ta zaro ido tana kallon hannun Khaleesat tace "Ina zoben naki?

Mun shiga uku ko dai Abdul din ya kwace?" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace "Ga fa shi nan a jaka" Safiyya tace "Atoh, don ni yanda na gansa wujiga wujiga anya karayar arziki bai fada masu ba kuwa, kamar wanda yake yunwa duk ya rame sai idanuwa da hanci, da kyar idan ba talauci a tattare da shi" Khaleesat dai bata tanka Safiyyah ba, Safiyyah tace "To ki saka zoben mana, ko jere zaki yi da shi a gaban madubi?" Khaleesat ta bude ido sosai tace "Ina zan je da zan saka zobe Sophie?" Safiyyah tace "Ke dai kin ki wayewa a rayuwarki Khaleesat, ba don gayu ya siya maki ba dama?" Warce jakar tayi ta ciro box din zoben tace "Dalla ki saka" Khaleesat tayi murmushi ta amshi zoben ta saka tana kallonsa admiringly, cif ya zauna mata ta kalli Safiyyah dake ta murmushi ita ma kamar bakinta zai yage tace "It's sooo cute, gaskiya Housemate is so romantic, har na hango kun yi aure, wallahi kashe ki zai yi kawai da soyayya, in soyayya ne a bar ma Housemate kawai, in kuma kwato hakki ne a bar ma Ajay" Dariya sosai ta ba Khaleesat, kawai ta mike bayan ta maida wayarta da empty box din zoben cikin jaka, Safiyyah ta rakata har zuwa inda Lyft dinta ke jira, ta bude motar ta shiga, hannu ta daga ma Safiyyah dake ta murmushi tana kallon zoben yatsanta dake ta kyalli, a haka Lyft din ya bar wajen, tun da suka kama hanya Khaleesat ke ta waige waige to be sure babu motar dake bin su a baya, don ita kam yanxu duk a tsorace take, tunda har Abdul ya iya gano apartment dinta to babu kuma abinda bazai iya yi ba, har dai suka isa bata ga alamar ko wani mota dake biye da su a baya ba, ta sauka daga lyft din tana tafiya a hankali ta shiga compound din, it's almost 4pm na yamma, motar Ajay ta fara gani a parking space din gidan, sannan ta ga motar Jay ma alamar duk suna gidan, walking slowly ta karasa har entrance din parlon dai dai sanda aka bude kofar parlon, ta
an koma baya tana kallon Housemate dinta dake kallonta da mamaki, cikin dubara ta boye zoben finger dinta da veil dinta kar ya gani, tana kirkiran murmushi a hankali tace "Good evening" Yace "Evening Housemate, come in" Ta sauke kanta kasa ta bi bayansa har zuwa cikin parlon, ta zauna kan kujera shi ma ya zauna yana kallonta hoping all is well don sai yaji gaba daya hankalinsa ya tashi ganinta a gidansu, jin tayi shiru yana kallonta yace "Hope all is well Housemate?" Tana murmushi tace "Alhamdulillah, babu komai, Ya Junaid yana nan?
Chapter 154 · 0% Book details