← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 167

Sashe 88

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sam ai ba a shige ma talaka duk yanda yake kuwa, tun asali zuri'ar da yake son in hada da wancan barawon mutumi ba wai nayi na'am da hakan bane, kawai bani da yanda zan yi da Abdallah ne" Momy ta gyara zama zuciyarta na tafarfasa tace "Atoh dai, har na gaji da nanata wannan sentence din da kayi Alhaji, ai ba a abun arziki da talaka don tun asali dama a tsiyace ya zo duniya kuma a tsiyace zai koma, kana zaman zaman ka gashi Abdullah ya ja maka asaran makudan kudi har da su taran kotu, wai kai da aka zalunta kai ne kuma da biyan tara saboda rashin adalci, ai Abdul bai kyauta mana bai duba mana ba, ace shi bazai dau maganata a matsayina na uwarsa ba?

Babu yanda banyi discouraging dinsa kan tsinanniyar yarinyar nan ba na nuna masa ba ajinsa bace yaki saurarata wallahi, kyanta ne kawai ya rudesa wato kyan
an maciji, har tayin er aminiyata nayi masa amma firr yaron nan yaki, to ga dai abinda ya ja mana" Meemah tace "Ni duk ba wannan ba Momy, kawai so nake in san wasu 'ya yan shegun ne suka tsaya mata haka har suka maida case din kotu?

Sannan ga auren ma suna kokarin kotu ta rabasa ta karfi da yaji, kun ga kenan mun tashi a tutar babu, kuma babu tantama duk yanda aka yi ma su suka boye yarinyar, su waye en iskan nan ne?" Alhaji Musa na safa da marwa a parlon yace "Don kotu ta kori karar nan ba shi ke nufin na bar wannan mutumi da ya salwantar min da dukiya ba, mu zuba mu gani da shi, sai na lahira ya fi sa jin dadi wallahi" Daga haka ya bar parlon kamar zai tashi sama, Momy ta sauke wani ajiyar zuciyar takaici tana girgiza kai tace "Abdallah bai duba mana ba wallahi, ya kaskantar da mu a idon duniya kawai, wai yau talaka ne ya ci nasara a kan mu a kotu, this is a big slap to us, kuma ko uban menene dalilinsa na dinga kashe waya ba a samun sa oho?

Ni taran da aka ci Alhaji ne ma yafi
ona min rai wallahi, ga mari ga tsinka jaka, ki sake kiran wayarsa kiji ko zai shiga" Meemah tace "Baza fa a samesa a waya ba Momy, mu da ganin Abdallah sai ya cika burin dake ransa kema ai kin san halinsa, gwara ma ki saka ma ranki salama mu bi sa da addu'a kawai" Momy ta kalleta tace "Wato kin san inda yake kenan?" Meemah tace "Ke dai kawai ki bi sa da addu'a Allah ya basa nasaran abinda ya saka a gaba Momy, amma shegiyar yarinyar nan ai kamar ta shigo gidan nan ne babu me hana hakan, don baza mu yi biyu babu ba" Momy ta tabe baki tace "Har ga Allah ni so nayi kawai ya hakura da er matsiyatan nan Meemah, kada tsautsayi ma yasa a hada iri da ita mu shiga uku, hada iri da talaka ai ci baya ne Meemah, don ni har cikin raina naki jinin talaka wallahi balle in hada zuri'a da su" Meemah tace "To ai dama bama fatan a hada iri da ita Momy, personally bazan ma bar hakan ya faru ba trust me, kawai ta shigo gidan ta gane Allah daya ne, ke kuma ki fara masa fafutukar wani auren da wuri wuri" Momy dai tayi shiru, can ta tabe baki tace "Allah ya sa ya saurareni to" Meemah tace "Haba dai zai saurareki, da kaina zan masa magana, a samar masa yarinya dai dai class dinsa" Momy tace "To ai shikenan, yanxu tracing din matsiyaciyar yarinyar ya sa a masa kenan?" Meemah tace "Ko ma dai menene mu dai mu zuba ido mu bi sa da addu'a kawai Momy" Mikewa Momy tayi tace "Bari in je in lallaba babanku, na dade ban ga ransa ya baci irin haka ba, haba ai abun da bacin rai, wai ace talaka yayi nasara akan ka a kotu bayan kai ne me gaskiya ai abun da ciwo" Daga haka ta wuce sama, Meemah ta dau wayarta tayi dailing number da take samun Abdul da shi ta tashi ta shiga dakin dake parlon.

Da asuba ko sallah ba ayi Malam Ali ya fito da er jakar da yake tafiya da shi bayan ya mulke jikinsa da basilin saboda sanyin da ake, bin dakunan matan nasa yayi duk ya kwankwasa masu kofa, Mama Zubaida da Mama Shatu suka fito suna kallonsa da mamaki suka ce "Lafiya Malam?" Mama Zubaida tace "Ko tafiya kauyen ne ya taso?" Shi dai bai tanka su ba ya dinga goge takalminsa da yayi
ura, Umma ce karshen fitowa ita ma ta tsaya tana kallonsa ta kasa cewa komai don tasan manufarsa, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya tsabar yanda hankalinta ya tashi, Nenne ce ta shigo gidan yafe da zaninta tana ganin Malam Ali tace "Yauwa ko sallah kar ka jira kayi idan kaje tashar kayi a can Ali, ga er soyayyiyar nama da gurasa na kullo maka ka ci a hanya" Mama Shatu tace "Tafiya zai yi ne Nenne?" Nenne tace "Babu ruwan ku, ku dai ku yi masa fatan Allah ya kiyaye hanya" Malam Ali ya amshi kullin nama da gurasan da Nenne ke mika masa, yana kallon matan nasa yace "Toh sai Allah yayi min dawowa" Mama Shatu tace "To ai shikenan, Allah Ubangiji ya tsare Malam" Mama Zubaida ma tace "Allah ya tsare duk da muna da hakkin ka sanar mana inda zaka je da asuban fari Malam" Nenne tace "Bazai sanar ba Zubaida, uban me sanin inda za shi zai kara maki?" Mama Zubaida ta juya ta koma daki, Mama Shatu ma ta tabe baki ta koma dakinta, Nenne ta kalli Umma tace "Wato ke ce isasshiyar da bazata yi masa Allah ya kiyaye ba ko Zahra'u" Shi dai Malam Ali tuni har ya fice daga gidan, Nenne na nuna Umma tace "Mugun abun ku zai kare maku da ke da er ki wallahi, babu wanda ya isa ya salwantar min da
a na lokacinsa bai yi ba" Daga haka ta bi bayan Malam Ali da sauri zata rakasa bakin titi ya samu adaidaita sahun da zai kai sa tasha.

That same day bayan an idar da sallahn asuba Jay ya shigo parlorn Mai martaba da sleepy face ta dalilin kiran da yayi masa, ganin irin zaman da Abba yayi kamar yana fadarsa ya gane serious issue Abban zai yi discussing da su kenan, ya kalli Ajay dake parlon zaune shi ma alamar kiran sa Abban yayi, Aunty ma na zaune parlon, Jay ya sauke kansa ya karasa kusa da Ajay ya zauna kasan lallausan carpet din parlon, dabi'ar Abba ne sai ya iya minti biyar zuwa goma kamar me nazari kafin ya fara magana in ya tara ku, Jay ya sunkuyar da kansa ya lumshe ido, Ajay ya
an kallesa sanin sai ya iya bacci a haka, ai ko yaga baccin yake, Ajay ya
an tunkudesa da elbow dinsa, Jay ya bude ido da sauri yana gyara zama, shi dai Abba kallonsu kawai yake, At last Abba yayi gyaran murya cikin nutsuwa yace "First of....
Chapter 88 · 0% Book details