← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 167

Sashe 163

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ko kuma ina wasa dake ne?" Ta
an langwabar da kai tace "To ai dai bazan san ba shi bane, since you are having the same height and complexion with him" Yace "I could slap you idan baki fita a gabana ba Malama" Ta wani ta
e baki ta nufi kitchen, irish ta diba ta fere wanda zata yi using, tana yanke yanken veggies da zata soya kwai da shi a ranta tana mamakin Why Ajay is in the house instead of her Housemate, kawai daga jiya zuwa yau ya mata masifa sau biyu, turo baki tayi ta ajiye wukan sai a sannan ta zaro ido ta dau irish dinta ta zuba a man gyada da ta dora don har ta manta da man gyadan, rufe baki tayi da hannunta jin fire alarm din kitchen din ya dau ruri, gaba daya ta mance da shi, don in dai zata yi soye soye wani lokacin lullubesa take da Shower cap dinta ta yanda bazai yi detecting komai ba balle ya fara tona mata asiri yana ruri, ta juya ta fito daga kitchen din tana kallon Ajay kamar munafuka tace "Don Allah ka zo ka min stopping din alarm din ya dena" Ajay yace "A'a ki dai kona masu gida ni ina ruwana, kin zata a Nigeria kike ba" Ta marairaice tace "Don Allah mana, kaga it's very loud fa" Ko kallon inda take bai sake yi ba, ta juya ta koma kitchen din tana kallon inda smoke alarm din yake, ita bata ma san ya ake kashewa yayi shiru ba, ta rage abun girkin zata sake komawa parlor ta masa magana ta kusa cin karo da shi zai shigo kitchen din, komawa gefe tayi tana kallonsa har yayi silencing smoke alarm din sannan ya fita daga kitchen din, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da girkin da take yi, bayan ta gama ta fito daga kitchen din dama iya wanda zata ci da Housemate dinta kawai tayi, tana kallon Ajay tace "Housemate dina fa?" Bayansa ya nuna mata alamar gashi ya goya shi, juyawa tayi ta wuce sama ya bi ta da wani kallo, tana shiga dakinta ta dau wayarta ta zauna gefen gado tayi dialing number Housemate dinta, yana fara ringing ya daga, in his calm voice yace "Good morning Halysaah" Ta
an yi murmushi kamar yana ganinta ta fara wasa da gefen duvet dinta a hankali tace "Good morning" Yace "How was your night?" Tace "Alhamdulillah, naga baka nan" Yace "Yea i went to get something, i will come over later" Tace "I made some breakfast for you" Yace "Really" Tayi shiru bata ce komai ba don har ranta ta so ya ci breakfast din, yace "Ohk give me 30 mins zan dawo sai in ci" Tayi murmushi har sai da dimples dinta ya lotsa tace "Toh Allah ya kawo ka lafiya" Katse wayar tayi sannan ta mike ta fita daga dakin ta koma downstairs, bata ko kalli Ajay ba tayi wucewarta kitchen ta ajiye ma Housemate dinta nasa breakfast din ta dau nata ta fito, hada ido suka yi ta sauke idonta har zata wuce sai kuma ta
an kallesa tace "There is everything available in the kitchen, idan kana son kayi making breakfast for ur self" Ya juya ya kalleta yace "Kee, ki shiga hankalin ki, ni ba Jay bane" ita dai tayi tafiyarta sama bata ce masa komai ba.

Da yammacin ranan Khaleesat na kitchen tana stew taji an danna bell, fitowa parlor tayi amma ta kasa karasawa gun kofar gabanta na faduwa, kaddai Abdul ne ya biyota, tunawa da tayi Ajay na gidan sai kuma taji hankalin ta ya kwanta, amma dai bata karasa gun kofar ba tana tsaye inda take, sama ta kalla ganin Ajay na saukowa downstairs, bai kalli inda take ba ya nufi kofar ya bude, Safiyyah ta koma gefe ganinsa ta fara kame kamen yafa mayafinta tace "Yaya Ajay ina wuni" A takaice yace "Lafiya" still kuma bai bata hanya ba, yana tsaye bakin kofar, Ta
an sosa kai tace "Kwana biyu nace ko laifi nayi maka da ban sani ba Yaya Ajay" Kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace "Kin ta
aga hannu ke kin mari namiji da har kika zuga kawarki tayi hakan?" Safiyyah ta gwalo ido ta cire handbag dinta a kafada tace "Na rantse da Allah ba da sanina tayi haka ba, ta yaya zan zugata? yanxu ma wallahi zuwa nayi zan mata fadan abinda tayi bata kyauta ba, ita Khaleesat bata jin magana kwata kwata ne, ko ni bazan daga hannu in mari lukeke irin Abdul ba, i am trying my best in dinga sakata a hanya amma abun yaci tura, ka tambayeta wallahi ni bani nace ta maresa ba" Ajay yace "Daga ke har ita za ku san yanda za ku yi da shi duk ranan da ya cafke ku a kasar nan..." Yana kai wa nan ya juya ya bar bakin kofar, Safiyyah ta tura masa maki, sai kuma ta shiga parlon tana gwale ido, ganin Khaleesat a tsaye a parlon sai kuma ta washe baki, suka zauna a nan parlon Khaleesat na tambayarta daga inda take ganin uban gayun da ta ci, kasa kasa take bata labarin Birthday din karen wani coursemate dinsu da taje da yanda masu karnuka ke ta zuwa da nasu ita kuma bata da ko mage balle kare, can tace "Da na sani na su Housmate na ara na tafi da shi wallahi" Khaleesat don takaici ma ta kasa ce mata komai sai kallonta take, Safiyyah tace "Har hotuna fa sai da muka yi da karnuka gwanin ban sha'awa in gaya maki" Khaleesat ta ta
e baki ta mike ta tafi duba stew din da take yi, bayan ta fito ta ajiye ma Safiyyah drink din da ta dauko mata ko zaunawa bata yi ba Safiyyan tace "Me jarababben nan ke yi a gidan ki, ina Yaya Housemate din mu?" Khaleesat bata san sanda ta fashe da dariya ba don Ajay yana bakin stairs a tsaye, kamar Safiyyah ta sani ta juya da sauri tana ganinsa ta sinne kai kamar munafuka, dai dai nan Housemate ya shigo parlon, Yana shigowa Ajay ya nufi kofa ya fice alamar dai shi yake jira dama, Safiyyah ta gaida Housemate da fara'arta tana masa sannu da zuwa, ya amsa ya karaso ya zauna parlon yana kallonta yace "Social function kika je ne haka" Tayi dariya har da tafe hannu tace "Eh wallahi birthday din karen wani coursemate din mu na je" Jay yayi murmushi yace "To sannu da dawowa" Tace "Shi ne nace bari in biyo ta nan, kwana biyu ban san me nayi ma Cousin dinka ba sai yayi ta
aga min hanci idan ya gan ni...." Jay ya shafa kansa yace "Don't mind him, wani lokacin haka yake" Safiyyah ta ta
e baki tace "Gaskiya abun nasa ba kyau..." Jay ya
aga ido ya
an kalli Khaleesat dake tsaye parlon tana kallonsa kamar ranan ta fara ganinsa, suna hada ido ta tura masa baki ta juya tayi wucewarta kitchen ya bi ta da kallo, duk Safiyyah na kallonsu tana
an murmushi, sai kuma ta rataye jakarta a kafada still smiling tace "To ni zan koma gida Housemate, kafin yayana ya fara kirana" Jay ya maida dubansa kanta yace "Kin jima da zuwa ne?" Tace "Ai ko minti goma ban yi ba, Cousin dinka ne ya bata min mood dina don ban ji dadin abinda yayi min ba, kawai albarkacin ka ya ci yasa na danne zuciyata, har fa da ce min ni nake zuga Khaleesat a America, abun nan ya min ciwo wallahi" Housemate na murmushi yace "Kiyi hakuri, but kinsan me Safiyyah....
Chapter 163 · 0% Book details