← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 167

Sashe 144

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko dai dama akwai abinda ke damunki kike son kiyi kukan amma sai yanxu kika samu sarari?" Khaleesat ta girgiza mata kai, wasu hawayen na taruwa idonta tace "Gida wai ya siya ma Abbana" Safiyyah ta bude baki da mamaki tana kallon Khaleesat, can ta dafe kirji tace "Gida fa Khaleesat?" Khaleesat ta kasa cewa komai wasu hawayen na sauka idonta, ta bude wayarta ta shiga chat dinsu da Aunty Farida ta tsaya dai dai wajen videos din ta mika ma Safiyyah wayar, Safiyyah was speechless for almost 2 minutes bayan ta gama kallon videos din gidan, wato gida ne har gida irin na zamani that is well furnished, a hankali Safiyyah tace "I am short of words too Khaleesat, wallahi ban san me zan ce ba, but just know that ur Housemate is one in a million Khaleesat...." Khaleesat ta fashe da kuka, Safiyyah ta rungumeta soothingly tace "It's something to be happy about ba kuka za ki yi ba, yanda ya saka iyayenki farin ciki Allah Ubangiji ya dawwamar da shi cikin farin ciki na har abada, Allah ya saka masa da mafificin alkhairi, ya biya masa duk bukatansa na alkhairi, yanxu kina komawa gida sai ki nutsu ki kirasa" Cikin kuka Khaleesat tace "Ko na kirasa baya picking" Safiyyah tayi shiru, can tace "May be he have his reasons Khaleesat, just compose a text for him sai ki tura masa ta WhatsApp, and i will also thank him via WhatsApp on ur behalf, duk wani abun farin cikin ki nawa ne nima...." Ita dai Khaleesat ta kasa cewa komai but she is soo emotional, ta kasa daina kukan da take, a haka driver ya zo daukanta, Safiyyah ta rakata har inda yake parking ta bude mata back seat tace "Don Allah kar ki je gida kina wannan kukan, wannan ai abun farin ciki ne ba na bakin ciki ba da zaki yi ta kuka har haka" Khaleesat ta gyada mata kai kawai tana share hawayenta, Safiyyah ta daga mata hannu tace "Anjima zan kira ki in sha Allah" Nan ma dai kawai kai Khaleesat ta gyada mata a haka drivern ya ja motar suka bar wajen.

Bayan sun isa gida Khaleesat ta bude kofar parlor ta shiga da sallama can kasa, kanta a kasa ta gaida Ajay da ta gani zaune parlor da Salem, sannan ta wuce sama, sau daya Ajay ya bi ta da kallo sai kuma ya dauke kansa, after some minutes yana kallon Salem yace "I am going up to get some rest, will you still be around?" Salem yace "Ohk i will wait har ka sakko" Mikewa Ajay yayi ya dau wayarsa sannan ya saka House Slippers dinsa ya wuce sama, kofar dakin da take ciki ya tsaya yayi knocking, Khaleesat da ta kwanta gefen gado ta dora kanta saman pillow feeling so emotional ta mike zaune tana kallon kofar, yana bude kofar ta fara goge sauran hawayen idonta, ya shigo closing the door behind him yana kallonta yace "What happened?" Sauke idonta tayi bata ce komai ba, yace "Ba kya ji na ne?" Girgiza masa kai tayi a hankali tace "Ba komai" Yace "Bakomai zaki shigo ma mutane gida kina kuka?" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, yace "Sake kula ki yayi a school din ne?" Ta daga kai ta kallesa ta girgiza masa kai cikin sanyin murya tace "A'a, kawai kaina ne ke min ciwo" Daga sama har kasa ya kalleta sannan yace "Kukan ya baki magani" Daga haka ya juya ya fita daga dakin....

Wajen karfe biyar Khaleesat ta farka daga baccin da ya dauketa tun bayan da Ajay ya bar dakin, da yake ba sallah take ba, mikewa zaune tayi ta jawo handbag dinta a hankali ta bude ta ciro wayarta, number Housemate dinta da bata kara saving ba har sannan tayi dialing hoping he will pick her call today, amma har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, to yanxu me ma zata ce masa ta WhatsApp, words failing dinta kawai za su yi in ma tace tayi masa magana ta can, bata ma san ta yaya zata fara ba,
aga kai tayi ta kalli kofar dakin jin ana knocking, sai da aka sake knocking din sannan ta sauka daga kan gadon tana tafiya a hankali ta tafi ta bude kofar, daya daga workers din gidan ne rike da tray din abinci, mamaki tayi don tun zuwanta gidan babu worker din da ya kawo mata abinci har daki, infact ita ce ma ke girka abinda take ci a gidan, ta dai amshi tray din cikin sanyin murya tace "Thank you" Sannan ta juya ta koma daki, bayan ta ajiye tray din ta bude plate din dake rufe a kai taga Jollof rice ne yana tiriri alamar yanxu aka gama girkin, ga wani aroma me dadi na tashi, ta bude wani plate din taga full chicken laps biyu anyi grilling dinsu, sai kuma bowl din veggies da dressing dinsu a gefe, with 2 bottles of water and a glass cup da can drink, still a kan tray din taga maganin ciwon kai, a hankali ta dau spoon ta goge sa da tissue din da aka yi wrapping dinsa sannan ta fara cin abincin, kuma sosai abincin yayi dadi, ya kuma yi yaji kamar a Nigeria aka yi, ta dai ci abinda zata ci ta ajiye sauran for dinner.

Washegari still haka aka kawo mata breakfast har daki, bacci ma take tunda ba school zata je ba ta sauka kan gadon ta saka hijab sannan ta bude kofar, bayan ta amshi tray din ta kulle kofar dakin ta tafi ta ajiye breakfast din don sai ta fara wanka....

Wajen karfe biyar din yammacin ranan Ajay na parlor tare da Salem aka bude kofar parlon, tun da ta shigo Ajay ke kallonta da wa enda ke biye da ita a baya, wato jakadiyarta da aminiyarta Hajiya Usaina, sai er aminiyarta da bazata wuce 25 years ba, Salem ya mike tsaye yana welcoming dinta da ladabi, ta amsa masa sama sama without looking at him, sai da ta zauna parlon bayan jakadiyarta tayi saurin gyara mata throw pillow sannan Ajay ya gaisheta, ta amsa cike da isa tace "Daga Massachusetts Boston mu ke, mun je convocation din Afrah a Havard University, we will be passing the night here before leaving for Nigeria tomorrow" Ajay dai bai tanka ta ba, ya gaida aminiyarta warce convocation din er ta suka je a Havard din, Afrah dake ta kallonsa ta gaishesa, ya amsa without looking at her sannan ya mike ya nufi sama, shi dai Salem ya juya ya fita daga parlon, Ajay na haurawa sama direct dakin da Khaleesat take yayi knocking sannan ya bude kofar.
[7/15, 9:49 PM] khaleesat Haiydar
: Khaleesat dake karatu da Laptop dinta ta juya tana kallonsa, a takaice yace "Don't look at me that way, ki dau duk wani abinda zaki bukata yanxu zaki koma dakin Jay don muna da baki a gidan...." Ko rufe baki bai yi ba aka bude kofar dakin, ta madubin dakin yake kallonta don tsayuwa tayi bakin kofa tana kallon Khaleesat with mouth agape, Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "Ina yini...." Aunty ta karaso cikin dakin da mamaki tana kallon Ajay tace "Junaid?

Wacece wannan kuma?" Ba tare da Ajay ya juya ya kalli inda take ba a takaice yace "Kanwar Salem" da wani expression Aunty tace "Kanwar Salem?

Me take yi a gidan nan?

Kuma a cikin daki zaune a saman gado?" Sai a sannan Ajay ya juya, looking at her in the eyes yace "The apartment she was staying was sold out yesterday, and she is homeless, so she is here for today before moving to her new apartment tomorrow...." Aunty tace "Da iznin wa kayi hakan?

Dama gidan ka ne nan din da zaka yanke hukunci kanka tsaye kamar me gidan?

I can't remember his Highness saying this house is urs in anyway Junaid, baka da right, sannan iyayenta da suka turota karatu basu nema mata wani alternative ba sai kai sarkin Hausawan Nigeria dake Baltimore?

Beside ban ga ta inda take kama da Salem ba, Salem da yake baki me ya hadasa da wannan farar yarinyar? karya kake yi daya daga matan banzan da kake iskancin ka da su ne a kasar nan, ka zata duk bamu san abinda kake yi ba ne?" Calmly Ajay yace "You can say whatever, kawai dai ni dai i also can't remember Abba saying we are to share this house with you and ur visitors, saboda ni da Jawwad Abba ya siya gida a garin nan ba don kowa ba, don haka ban ga dalilin da za ki dinga zuwa da wasu mutane can babu notice ba ki maida mana gida gidan saukan baki, kaf Massachusetts babu hotels da dole sai kin taho Maryland za ki samu masauki?

Beside all this... u are not even in the rightful place to tell me what to do and what not don da sunana da na Jawwad Abba ya siya gidan nan, don haka babu ruwanki da duk wanda zan kawo gidan, since you can't do without intruding, ki zo kiyi intrusion dinki in peace kiyi tafiyarki without questioning me...." Aunty da ta bude baki tana kallonsa tace "Zagin nawa da ka saba zaka yi Junaid?

Ni kake gaya ma bakaken magana?
Chapter 144 · 0% Book details