← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 167

Sashe 18

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

If you are not interested in my cousin brother ba sai kin ta corner corner ba kina kawo zancen da hankali ma bazai dauka ba, meye hadinki da wata Surayya da zaki bar halal don kunya?" Khaleesat tace "Ni dai don girman Allah ki ma bar wannan zancen, Ya Mustapha kuma kiyi ma Allah ki gaya masa i am engage, ni bazan daga kiransa ba" Safiyyah tace "Wa
llahi bazan fada ba ai kina da baki ki gaya masa da kanki, ke da wa aka yi engaging da zance masa u are engage?

Ai as far as i am concern ni ban san wannan batun ba, kawai nasan kina da wanda baki da wani option sai na aurensa, but as time goes on ke kanki zaki san kina da option, za kuma ki ji baza ki iya auren ba sai dai duk abinda zai faru ya faru" Khaleesat ta ta
e baki tace "Kin ga ni yunwa nake ji zan tafi gida, sai gobe in mun hadu" Safiyyah bata tanka ta ba ta ci gaba da tafiya ta bar ta tsaye a wajen, Khaleesat ta bi ta da kallo, to wai ma ta yaya zata daga kiran Ya Mustapha, ita a rayuwarta abinda tasan in an mata bazata ji dadi ba ko by mistake ne bata yi ma wani, ita Safiyyah in ita ce a shoe din Surayya ya zata ji, wannan ai son zuciya ne ma kawai, bin bayanta Khaleesat tayi tace "Ni dai tunda ba mu da aji mu je gida pls ki mana girki i am very hungry and at the same time tired from yesterday's journey" A haka ta samu ta lallaba Safiyyah dake jin haushinta suka kama hanyar gidanta, suna sauka daga Uber ta nufi apartment dinta tana kallon Garage taga babu motar Housemate dinta, does this mean a bude ya bar kofar tunda makullin na hannunta, tana murda kofar taji sa a kulle, to ina ya samu key? ko dai magana yayi aka basa wani makullin, bude jakarta tayi ta ciro key ta bude kofar suka shiga cikin living room din tare da Safiyyah dake biye da ita, Safiyyah ta dinga bin parlon da kallo ta lumshe ido tace "Kai amma wannan turaren Housemate din naki ba dai dadin kamshi ba, the perf is so cool" Khaleesat dai bata ce mata komai ba, ta ajiye jakarta da mayafi ta zauna saman kujera tana ciro wayarta a jaka, Safiyyah ta zauna ita ma kan kujera tace "To kun hadu da Abdul din a Nigeria?" Khaleesat tayi shiru cause kawai taji ita ko maganar Abdul ma bata son ana mata yanzu, ganin yanda Safiyyah ta tsareta da ido, a takaice tace "Eh... me zaki dafa mana pls, wllhi yunwa nake ji" Safiyyah ta mike tace "Toh bari in je in ga what is available in the kitchen" Daga haka ta mike ta nufi kitchen, tana shiga bayan few minutes sai ga ta ta fito, tana kallon Khaleesat da mamaki tace "Kee wai Housemate din naki ne ke maku restocking abubuwa a kitchen haka?

Look how ur kitchen is stocked up with costly food items, where is he getting the money to buy all this from?" Khaleesat tace "Baza dai kiyi girkin ba kenan in zo inyi?" Safiyyah tayi dariya tace "No wallahi mamaki nake naga abubuwa masu tsada yake siya, don ni dai nasan kudin da Abdul ke turo maki bazai ta
a siya maki wnn uban abubuwa dake kitchen din nan ba, anya bazan dawo gidan nan ba kuwa Khaleesat?

Kinga wasu tsadaddun cookies da drinks da na gani, even the table water in this kitchen ba na yara bane wallahi, the fridge is full to the brim" Khaleesat taki tanka ta tana danna waya, hakan yasa Safiyyah ta juya ta koma kitchen tana kara jaddada anya bazata dawo gidan ba kuwa, Lafiyayyen girki Safiyyah ke yi a kitchen din komai baja baja malam, Sallah kawai Khaleesat tayi a daki ta dawo ta kwanta kan 3 seater tana danna wayarta waiting for the food to be ready, kiran Abdul ne ya shigo wayar hannunta, sosai gabanta ya fadi lkci daya mood dinta ya canza ta hade rai, ta dinga kallon screen din wayar fuskarta babu fara'a tana jiran sai ya kusa katsewa kafin tayi picking call din, dai dai nan taji alamar ana bude kofar parlon, ta mike zaune tana gyara scarf dinta sai ga Housemate dinta ya shigo parlon, sallama yayi ganinta zaune living room din, ta ajiye wayar hannunta ta fasa picking call din Abdul din ta amsa sallamar House mate din nata, yana cire takalman kafarsa yace "Good evening" Ta sauke idonta tace "Ina yini" Yace "Alhamdulillah, bakuwa kika yi?" Double foot wear da ya gani bakin kofar yasa yayi tambayar, tace "Um she is my course mate" Yace "Good" Daki ya nufa, sai a sannan ta kalli wayarta taga kiran Abdul har ya katse tuntuni, she wasn't bothered at all kuma bata yi attempting bin kiran nasa ba ta ajiye wayar kawai, mikewa tayi ta wuce kitchen, tare suka fito kitchen da Safiyyah bayan Safiyyar tayi dishing masu abincin a plate daya, Safiyyah na bin parlon da kallo tace "Ko dai Housemate din naki ya dawo ne kamshin turaren nake kara ji a parlon" Khaleesat ta dau spoon ta fara cin abincin tace "Ko dai kin san sa ne Safiyyah?" Dariya Safiyyah tayi tace "Ina kuwa na san sa, kawai so nake in gansa ne wallahi, irin wannan kayan alatu a kitchen haka, where is he even getting the money shi da ya zo ta scholarship" Khaleesat dai cin abincin gabanta kawai take taki ce mata komai, Safiyyah ta dau spoon ta fara cin abincin ita ma, basu jima da fara cin abincin ba sai ga shi ya fito daga dakinsa, bai kalli direction din da suke ba ya nufi kofa rike da laptop dinsa, Safiyyah ta bi sa da kallo kamar idonta zai fita ya bi sa, ita dai Khaleesat kallo daya tayi masa ta ci gaba da cin abincinta har ya fita daga parlon ya kulle masu kofa, Safiyyah ta ajiye spoon din hannunta tace "To fa, shi kuma haka yake?

Ji wani
aga shoulders da yake ko kallon inda muke bai yi ba, haka yake maki a gidan dama?" Khaleesat tace "You can be funny Safiyyah" Safiyyah ta hade rai tace "No like seriously haka yake feeling kansa?

Ko don abincin da yake ajiye maki na yan gayu a kitchen ne ya ja haka?

Ta yaya zai wani wuce mu babu ko Hi, ni fa bana son harkan walakanci" Khaleesat tace "Look Safiyyah ni ba shi ya ajiye min duk abinda kika gani a kitchen ba, shi baya ma zaman gidan nan, jifa jifa kawai nake ganinsa, beside ai mun gaisa da ya shigo kina kitchen, to kuma kallon me zai yi mana don zai fita?" Safiyyah zata yi magana wayarta ya fara ring, mikewa tayi ta dauko wayar, ta
an buda ido tana kallon Khaleesat tace "Ke Abdul ne ke kirs" Sosai gaban Khaleesat ya fadi ta ajiye cokalin hannunta ta dinga kallon wayar Safiyyah, Safiyyah ta rike ha
a tace "Ikon Allah, ko ya kiraki baki daga bane?

Let me pick dai inji me zai ce" Da sauri Khaleesat ta kamo hannunta zuciyarta na bugawa tace "Safiyyah kar ki ce masa naje Nigeria plss cause bai sani ba wallahi" Safiyyah ta saki baki tana kallonta hangangan, da mugun mamaki tace "Ban gane bai sani ba?

To wa yayi sponsoring tafiyar taki?

Ina kika samu kudin tafiya" Sosai hankalin Khaleesat ya tashi a lkcn, tana girgiza ma Safiyyah kai tace "Just don't tell him pls, nace maki bai sani ba" Safiyyah da mamaki ya kasa barin ta tace "Ai kiran nasa ma ya katse" Khaleesat taji gaba daya abincin ya fita ranta, sai ga kiransa ya sake shigowa wayar Safiyyah, Safiyyah ta gwalo ido tace "Abdul ne da kirana har sau biyu?

Anya lafiya" Khaleesat tayi gathering courage tace "Just pick, in ya tambayeki ni kawai kice masa bani da lafiya yanzu ma kika baro gidana" Safiyyah tace "Ohk" Picking call din tayi ta saka handsfree, ita ta masa sallama ya amsa yace "Ya kike?" Safiyyah tace "I am good" yace "Are you together with Khaleesat?" Babu bata lkci Safiyyah ta sanar masa exactly abinda Khaleesat tace ta gaya masa, ya dan yi shiru at first, sai kuma yace "Tun yaushe ne bata da lafiya?" Safiyyah ta kalli Khaleesat, da sauri Khaleesat tayi mata alamar sati daya da fingers dinta, Safiyyah tace "Yau ina jin sati daya kenan" Daga daya bangaren yace "Sati daya?
Chapter 18 · 0% Book details