← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 167

Sashe 148

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

I am sorry i should have knock" Ta girgiza masa kai kawai ba tare da ta kallesa ba, yace "Are you sure you are okay Housemate?" Zame hannunta tayi daga fuskarta tana kallonsa, a hankali yace "Sorry Halysaah, i forgot my phone shi ne na dawo dauka..." Mika masa wayar tayi ya amsa yana kallonta, ita dai ta sauke idonta, bude mata kofar yayi ta fara fita sannan shima ya fita, ta mika masa makullin apartment din ya amsa ya kulle sannan suka nufi motarsa har a lkcn bai daina waigawa yana kallonta ba to be sure she is okay har suka iso garage, ita dai bata sake yarda ta kallesa ba, ya bude mata gaban motar yana kallonta,
an murmushin karfin hali tayi still not looking at him murya can kasa tace "Thank you" Sannan ta shiga motar, tana shiga ya daga mata veil dinta da ya fito waje ya daura kan cinyarta yana kallonta, sae a sannan ta daga manyan idanuwanta ta kallesa ya sakar mata murmushi, ita ma murmushin tayi har sai da dimple dinta ya lotsa ta sunkuyar da kai tana wasa da gefen veil dinta, ya kulle motar ya zaga ya shiga driver seat yayi igniting motar, bayan sun yi nisa ya
an kalleta murya can kasa yace "Are you sure you are okay Halysaah?" Khaleesat ta
an bude ido tace "Sure..." Don tabbatar masa da hakan tayi kokarin creating conversation tace "Ya Junaid fa?" Jay ya maida dubansa kan titin gabansa yace "Ba kuna magana da shi ta waya ba" A hankali Khaleesat tace "A'a, sai if there is something important" Without looking at her yace "Something important like?" Tace "May be idan ya kawo min abu apartment" Yace "Abu kamar me?" Khaleesat ta juya ta kallesa tace "Grocery shopping" Jay ya gyada mata kai yana ci gaba da driving dinsa, har suka isa school babu wanda ya sake cewa komai a cikinsu, ita kam Khaleesat ta tafi duniyar tunanin da take.....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788
, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
https://chat.whatsapp.com/I5vo38MH2jH8pDvzVF0Q4w
Bayan Jay yayi parking a school din ya juya yana kallonta, zata bude motar ta sauka yayi kasa da murya yace "Halysaah" Ta juya tana kallonsa, yace "What happened?

Why the sudden change of mood?" Khaleesat ta
an bude ido, sai kuma tayi murmushin karfin hali ta girgiza kai tace "Ba komai fa" Yace "Are you sure?" Ta sauke idonta tace "Sure" Yace "Yaushe za ku gama lectures din?" Tace "Lecture daya kawai za mu yi" Yace "Zuwa 3pm kun gama kenan?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk, i will pick you then" A hankali tace "To Nagode" Murmushi kawai yayi mata yana kallon idonta, ta bude motar ta sauka ya bi ta da kallo, sai kuma ya dau wayarsa, Lkci daya ya gane ta shigar masa wayar cause yasan yana da miss calls din Hadeeyah da message a gaban screen, swiping yayi ya bude wayar yaga alamar ta shiga har cikin message din bayan call logs dinsa, jinginar da kansa yayi a hankali jikin kujeran motar with different thoughts running his mind.

Har Khaleesat suka gama lectures bata ga Safiyyah ta shigo school ba ranan, tana zaune inda suka saba zama tana ta kokarin kiran Safiyyah tun daxu amma numberta baya shiga, lkci lkci take bin inda take zaune da kallo as if wanting to figure out something, at some point she became confuse and afraid at the same time don wasu memories that are not welcome in her heart ne suka hau dawo mata kai, Student sai harkan gabansu suke a vicinity din babu ma wanda yake kallon inda take zaune, tana kokarin tashi ta bar wajen kawai sai ga kiran Safiyyah ya shigo wayarta, Khaleesat ta koma ta zauna tayi picking call din ta kai wayar kunne, Safiyyah tace "Kin ga ban shigo school ba shine ko ki kirani matar nan?" Khaleesat tace "I have been trying ur line tun daxu baya shiga, hope you are fine?

Why are you not in school today?" Safiyyah ta kyalkyale da dariya tace "Ke da ba sai dai in kira ki ince maki Surayya ta rasu yau ba" Khaleesat tace "Me ya faru?" Safiyyah tace "Ni dai wallahi har na fidda rai da ita in gaya maki kawata" Khaleesat ta hade rai tace "Don Allah ki gaya min me ya same ta?" Safiyyah tace "To wani azababben zazza
i ne ya damke ta har tana suma, sai ga Surayyan ki har da kamo hannuna yau tana neman agaji duk ta ruda ni, yanxu haka tana can an bata gado a asibiti, ni kuma ina gida saboda Aslam shi yasa ma ban shigo school yau ba, Aslam din da ko kusa da ni bata bari ya zo, kinga in ni mayya ce ai yau da babu abinda zai hanani cinye mata
a" Khaleesat tace "To Allah ya sauwake, Allah ya bata lafiya, wani asibitin ne?" Safiyyah tace "Oho ni dai ba an bar ni da baby sitting ba, Housemate dinki fa?

Wallahi naji haushi da bazan samu zuwa in masa sannu da zuwa ba, ai sai ya zata ma walakanci ne ya dawo naki zuwa" Khaleesat tayi murmushin da bata yi niyya ba tace "Ni dai sai anjima, har mun gama lectures din" Safiyyah tace "Don Allah ni dai in ya je apartment din naki anjima ki kirani ki gaya min, ko goyo Aslam ne sai inyi in taho, kin ga ba dadi ace ban masa sannu da zuwa ba har zuwa yanxu" Khaleesat ta dake don bata son tayi dariya tace "Till we speak Sophie, sai anjima...." Safiyyah tace "Ke dalla ba cewa zan yi ina son sa ba, kowa yasan Housemate ai naki ne duk wanda yace zai maku shisshigi ma ai sai dai ya mutu, kilan ma har ya tambayi baba aurenki baba kuma ya basa bamu sani ba" Bude baki Khaleesat tayi a bit shock, don she never saw those words coming from Safiyyah, Safiyyah tayi dariya tace "Atoh, mu ba mu ki gobe a daura auren ba ma wallahi, Uztax Ajay sai ya bada sadakin yayansa, shi kuma Housemate kawai ya tare a nan apartment din naki Ajay da Salem su rakasa, in kayan mata ne sai in debo maki na Surayyah don a kitchen ma take jerasu don in gani, Ghana must go dinsu ake aiko mata daga gida, kin ga kawai sai in debo maki kina da gwangwanin madara da yoghurt abun ki, yanda dai zaki dawo babu banbanci da warce bata ta
a aure ba" Khaleesat bata san sanda ta katse wayarta ba ta kife a kafarta kamar warce taji wani mugun abu daga bakin Safiyyah, tafi minti goma zaune a yanda take kamar an dasa ta, taji wayar hannunta ya fara vibrate, a hankali ta juya wayar taga number Housemate, at first ta kasa daga call din nasa, sai da taga ya kusa katsewa sannan tayi picking ta kai kunne tayi shiru kamar munafuka, daga daya bangaren yace "Are you done Halysaah?" Ta gyada masa kai tace "Um" Yace "Ohk, i am waiting for you" A hankali tace "To" Sannan ta katse wayar ta mayar cikin jakarta, ta mike ta fara tafiya zuwa inda zata samesa.

Har ta shiga motarsa bata yarda ta hada ido da shi ba, shi dai kallonta kawai yake, Bayan ta kulle motar a hankali tace "Ina yini" Calmly yace "Lafiya lau Halysaah, ya lectures din?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Frnd din ki ta tafi ne ita?" Khaleesat ta girgiza masa kai tace "Bata zo schl yau ba, matar brother dinta bata da lafiya" Yace "Allah ya bata lafiya" Daga haka ya fara driving zuwa gidanta, sai da suka kusa apartment din nata ya kalleta speaking slowly yace "Do you mind going out for dinner with me later Housemate?" Sai a sannan Khaleesat ta dan kallesa, suna hada ido ta sauke idonta a hankali tace "Alright" Yayi mata murmushi ya ci gaba da driving dinsa, Yana parking gaban apartment dinta ba tare da ta kallesa ba tace "Thank you so much" Yana kallonta yace "You are welcome Housemate..." Ta bude motar ta sauka sannan ta
an kallesa suka hada ido, murmushi tayi ta daga masa hannu sannan ta juya ta nufi apartment dinta, shi dai ya bi ta da kallo har ta shiga.

Tun da Khaleesat ta ga karfe bakwai na yamma yayi ta zama tense, ta rasa dalilin da yanxu kuma take jin nauyin Housemate din nata sosai, duk da ba yau ta saba fita dinner da shi ba, amma yau gaba daya sai take jin wani nauyi na musamman, har lkcn kuma bata shirya ba tana dai zaune saman darduma after praying, karfe bakwai da minti goma kiransa ya shigo wayarta, ta jawo wayar a hankali tayi picking ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yace "I am on my way now Halysaah" A hankali tace "Ohk, Allah ya kawo ka lafiya" Sai bayan da ta ajiye wayar ta mike ta fara duba kayan da zata sa, har ya iso apartment din nata after 15 minutes bata gama shiryawa ba, sai da ya jirata for another 10 minutes sannan ta fito, ta gansa tsaye jikin motarsa ya rungume hannu yana jiranta, sauke idonta tayi har ta karaso inda yake tsaye, yayi mata murmushi yana kallonta ya bude mata front seat, ita dai taki yarda su hada ido ta shiga motar, yana kallonta yace "Housemate" Sai a sannan ta daga idanuwanta ta kallesa, kamar me rada yace "You look cute" Rufe fuskarta tayi da veil dinta tana murmushi, ya kulle motar ya zaga ya shiga driver seat.

The ride was silent, tunanin da take yi daban a ranta shi ma haka, bayan sun isa wajen cin abincin after offering her a seat ta fara zama sannan shi ma ya zauna opposite dinta, ya dau menu din eatry din yana mika mata yana kallonta, ta sauke idonta tace "I am okay with anything u order" Yace "Are you sure?
Chapter 148 · 0% Book details