Sashe 65
Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
fita daga layin, driving kawai AJ yake idonsa a kan titi, gaba daya he look speechlesss, tunda ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba, ita dai Khaleesat ta rufe fuskarta da Hijab dinta saboda hasken rana dake damun idonta kuma tana tsoron kar ace su hadu da Abdul dan motar babu Tint, har sannan bata daina kukan tashin hankalin da take ba, after driving for 20 mins AJ ya kalli wayarsa dake vibrate, Number Jay ne ke kiransa, hakan ya sa ya rage tafiyar da yake ya gangara gefen titi yayi parking sannan ya dau wayar yayi picking ya kai kunne a hankali yace "Jay" Khaleesat ta zame hijab dinta daga fuska jin sunan da ya kira ta juya ta kallesa, Calmly taji yace "I am cool" tambayarsa Jay yayi ko ya bar Kano, AJ yace "Am still around, when are you leaving Maryland?" After few seconds AJ yace "Alright, we will talk later" Daga haka ya katse wayar ya ajiye ya jinginar da kansa jikin kujerar motar ya kafe titi da ido for almost 2 mins, can ya sake daukar wayarsa don duba available flight to Abuja ranan, yaga jirgin karfe uku kuma saura just few seats, National ID card dinta da passport dake motarsa tun ranan da suka dawo US da drivern su na Lagos ya amsa a wajenta don mata booking ticket to kano, ticket ya siya mata immediately na zuwa Abuja sannan ya ajiye wayar, Aunty na nan gidansu na kano sun zo biki shi sa ma bazai fara kai ta can gidan ba, juyawa Khaleesat tayi da kyar ta kallesa tana dafe kanta pleadingly tace "Kanwar Ummata tana Lagos, don girman Allah ka taimakeni i want to go to her plss" Shi dai kallonta kawai yake, Calmly yace "Where in Lagos?" Tace "Zan kira in tambayeta, amma bani da numberta ne" Ya ga alamar gaba daya she is confuse and in fear, yace "Ta yaya zaki kirata baki da numberta?" Wayarsa ta dauka da sauri ta shiga call logs dinsa tana duba number Baaba Gaje, dialing tayi yana fara ring Baaba Gaje ta daga, da sauri Khaleesat tace "Baaba Gaje don Allah number Aunty Farida za a duba a wayarki sai a turo ta wannan layin" Baba Gaje tace "Har kun je wajen kare hakkin an Adam din?" Khaleesat tace "Ki dai turo min don Allah yanxu Baaba" Baaba Gaje tace "Toh bari in je makota kin san ban san kan wayar ba ai" Khaleesat ta gyada kai da sauri tace "To ina jira" Katse wayar tayi ta jinginar da kanta jikin kujera tana sauke numfashi, wani dishi dishi take gani tsabar kuka, Shi dai Ajay idonsa na kan titi alamar dai kansa ya gama kullewa, ya kalli agogon wrist dinsa yaga karfe biyu ya gota, driving motar ya ci gaba da yi da tunani iri iri a ransa ya nufi wani eatry ya sauka ya shiga ciki, Khaleesat ta dinga bin haraban wajen da kallo sai kuma ta rufe fuskarta da Hijab dinta da sauri zuciyarta na bugawa, incident din jiya ne kawai ke dawo mata a kai as if she is hallucinating, sai taga kamar yanzu incident din ke faruwa yanda Abdul yayi parking ya fita daga mota ya shiga eatry, kan kace me ko ina na jikinta ya fara rawa taji kamar numfashinta zai dauke, ba a dau lokaci ba Ajay ya fito daga gidan cin abincin da leda a hannunsa, yana shiga motar ya ajiye ledan da sauri yana kallonta yace "Me ya faru??" Ta dago kanta hawaye caba caba a fuskarta, sai kuma ta kamo hannunsa gam tace "I just want to leave here plss, don Allah mu bar nan" Gaba daya ta dawo kamar warce ta zauce, ya fara bin area din da kallo tunaninsa ko Abdul din ta gani, can ya sake kallonta bayan ya zauna cikin motar, cikin nutsuwa yace "Look, stay calm....