← Book details Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 167

Sashe 50

Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ko
an uwan nan nasa da kike complain a kai kece baki iya siyasar zama da shi ba, ba gashi ni yana kulani ba har da tambayata ya exams, gaskiya ki canza hali Khaleesat, ya ci ace kin yi koyi da ni akan abubuwa da yawa" Khaleesat dai bata tanka ta ba, Safiyyah tace "Duk sai kika sa kunya ya kama ni tsamo tsamo, yanzu zata su kuma wa ennan en kauyen daga ina" Safiyyah ta dau jakarta tana ciro wayarta taga miss calls din Mustapha tace "Ahaf ai na sani" Tsaki ta ja ta fara kokarin order din ride din da zai maida ta gida.

AJ ya bude kofar dakinsa jin ana knocking, tana kallonsa daga inda take tsaye ba tare da taje kusa kusa da kofar ba tana
an kame kame tace "Ya Ajay, naga wasu mata ne a gidan, kun yi baki ne?" AJ ya gyara tsayuwarsa yace "Ohk, su nawa?" Ta
an bude manyan idanuwanta tace "Su biyu" Ya gyada kai yace "Good, you saw the fair Slim one that is like yellow pawpaw?" Yarinyar tace "Sure" Yace "To sabuwar budurwar saurayinki ce, all of a sudden ya tattaro ta ya dawo da ita gidan nan suke zama tare, when i said i am reporting him back home he threatened me" The lady look totally speechless and confuse, a hankali tace "Budurwarsa kuma Ya Ajay?" Ya wani hade rai yace "Ina wasa da ke ne balle in maki karya?" Shiru tayi bata ce komai ba ta sauke idonta kasa, yace "She's been in this house for 3 weeks now, ya kai ta school ya dawo da ita" Yarinyar ta sake daga ido ta kallesa, AJ ya daga kafada ya kulle kofarsa, juyawa tayi tana tafiya a hankali ta bar wajen.

Har waje Khaleesat ta raka Safiyyah bayan ta takurata ta rakata, sai ma da suka jira Lyft din ya karaso sannan Safiyyah ta shiga ta mata sallama, Khaleesat ta daga mata hannu sannan ta juya ta koma cikin gidan, zaune ta ga yarinyar daxu a parlor, suna hada ido Khaleesat ta sauke kanta sai ta kasa wuce sai da tace mata "Hi, i am Khaleesat" Ido kawai yarinyar ta zuba mata tana kallonta babu yabo babu fallasa kuma babu alamar zata amsa mata, hakan yasa Khaleesat ta fara tafiya ta wuce sama, lkci daya jikinta yayi sanyi ta shiga dakin da take ciki ta kulle.

AJ ya fito dakinsa zai sauka downstairs kenan sai ga Jay ya hauro sama fixgosa yayi a fusace yace "Are you out of ur senses Junaid, what did u just do?" AJ yace "Ban gane what did i just do ba, Hadeeyah came, she requested to know the lady she saw in this house, kai kuma baka isa inyi karya saboda kare ka ba tunda ba tsoronka nake ji ba, when i told u to look for another alternative for the brat ai mayar dani mahaukaci kayi" Bude kofar wani daki aka yi sai ga Hadeeyar ta fito da Handbag dinta, Jay ya sake AJ, ya bi ta da kallo yace "Hadeeyah" ko juyawa bata yi ba ta ci gaba da sauka downstairs, ita dai tasan AJ ba wasa yake yi da ita ba balle yayi mata karya, yaushe ma ya sake maka fuska balle ya maka karya, Jay yace "Look Hadeeyah, ko da wasa kika ce zaki ma people back home wannan magana i won't take it likely with you, and that will be the end between me and you, cause u never gave me a listening ear" Sai a sannan ta juyo tace "And so effing what?

Wannan ne dalilin da yasa all this days baka da lokacina dama ko Ya Jawwad?

I am not surprise" Tana kai wa nan ta sauka ta nufi hanyar fita gidan, Jay ya kalli AJ da ya daga kafada shima yana kallonsa.

Jay wasn't even that bordered kamar babu abinda ya faru, amma gaba daya ya fita harkan AJ a gidan, ko kallon inda yake baya yi, ya canza code din kofar dakinsa ta yanda ma bazai shigo masa daki ba, yasan ba lallai ma Hadeeyah ta gaya ma yan gida komai ba, she won't even dare try that, amma still yaki ko da kiranta a waya, dama ita ce me kiran nasa, daga Oxford University take kuma bata ma ce masa zata shigo Maryland ba she just came without notice, ita ko Khaleesat bata ma san abinda ke faruwa a gidan ba amma abinda Hadeeyah ta mata ya tsaya mata a rai.

Ranan friday Khaleesat suka yi second to the last exam dinsu, na karshen kuma za su yi ranan talata, gaba daya ta kagu su gama ta bar kasar zuwa sannan hankalinta yayi gida, she just want to go home, duk da tasan Housemate dinta zai ce zai siya mata flight ticket amma gani take she is just a burden to him, for weeks now hidima kawai yake da ita, ya kai ta schl, at times ya jira ta gama jarabawa ya maidota gida, wani lkcn dab da sanda yasan zata fito exam zai koma schl din don daukota, he really tried for her during this period and he is always making sure that she is fine, bata ma san ta inda zata fara appreciating din shi da Safiyyah ba, they where by her side all through, ba don su ba da bazata iya jarabawan ba ma, yau kam tunda ta tashi take jin ta wani iri tana dai kwance da tunani iri iri a ranta, ji take kamar ta jawo monday.

AJ na zaune reading nook din dake parlor yana kokarin hada references dinsa a laptop dinsa, ga textbooks kaca kaca a gabansa, gaba daya Jay ya bi ya goge duk wanda ya tura masa ta WhatsApp, infact duk wani abu da Jay yasan AJ zai karu da shi na bangaren PhD da suke sai da yabi ya goge tas, shi da AJ bai nuna masa ma yasan abinda yayi ba, shi yasa ya dukufa tun asuba yake reading nook,
aga kai yayi bayan yayi perceiving din wani turare da ya gauraye ko ina na parlon, he was a bit shock ganin wanda ya shigo parlon tare da wasu mutane biyu suna biye da shi, ya sauke idonsa, he was surprise and shock, sai kuma ya mike ya dawo cikin parlon, ya
an dukar da kansa yace "Sannu da zuwa Abba" Wanda ya kira da Abba yace "Ya karatun?

Ina Ahmad?" AJ yace "He is upstairs, Abba surprise visit ka mana" Zaunawa Abban yayi saman kujera yana amsa gaisuwan da ma'aikatan gidan ke masa cike da ladabi sannan ya kalli AJ yace "I just branched to check on u both, daga England mu ke munje wani taro" AJ dai ya sunkuyar da kansa, sai kuma ga wata mata da bazata wuce 50 ba cikin shiga ta alfarma ta shigo parlon da wata yarinya that is 16 years old, AJ dai ya shafa kansa don shi abun ma dariya ya fara basa, ya dai gaisheta ta amsa, yarinyar ta tafi ta rungumesa tace "Ya AJ naga ka zama kato, are you going to the Gym?" Matar da suka shigo tare ta nemi waje ta zauna tace "Allah sa karatun yake" Wani kallo ya mata ta gefen ido ya wuce sama su kuma masu aikin gidan suka tafi dauko bottle water da lemo, direct dakin Jay ya nufa a dai lkcn da Jay ya bude kofar dakinsa ya fito, AJ yayi wata dariyar bosawa yace "Wallahi ga Abba da Aunty a parlor" Jay ya dinga kallonsa babu ko kiftawa, can yace "Abba da Aunty kuma?" AJ couldn't stop laughing, Jay ya
an leka downstairs yaga da gaske ne, buda baki yayi yana kallon AJ da ya kasa daina dariya, Jay ya sauke ajiyar zuciya ya jawosa yace "Look, let's talk pls Ajay...." Ajay yace "Talk about what?
Chapter 50 · 0% Book details