Sashe 39
Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da yamma Khaleesat ta gama shiryawa bayan Safiyyah ta isheta da kira wai taje ta mata kitson, Khaleesat ta dau handbag dinta da mukullin gida bayan Uber din da tayi order ya iso sannan ta fita daga gidan ta kulle, tana hanya kiran Safiyyah ya shigo wayarta, ta daga tace "Ina hanya fa" Safiyyah tace "Allah in baki zo ba sai dai gashinki yayi ta zama haka bani da lokacin maki wani kalaba kuma idan aka fara jarabawa" Khaleesat dai tayi murmushi, tasan kawai Safiyyah so take ta je gidan, karfe hudu da yan mintuna ta isa gidan ta sauka Uber sannan tana tafiya a hankali ta nufi apartment din, tsayawa tayi bakin kofa ta danna bell, lkci daya aka bude kofar, sai da gaban Khaleesat ya fadi ganin Surayya ce ta bude mata kofa, ta sauke idonta tace "Ina yini?" A takaice Surayya tace "Wa kike nema?" Khaleesat ta daga kai ta kalleta tace "Wajen Safiyyah na zo" Bluntly Surayya tace "To bata nan, sai ki juya ki koma inda kika fito" Khaleesat was just looking at her babu ko kiftawa, sai ga Safiyyah ta fito daga daki fuuu, tana huci tace "Wajenta kika zo da zaki tsaya sauraronta baki bangajeta ba kinyi shigowarki?" Khaleesat ta bude baki tana kallon Safiyyah, wato ta bangaje matar gida ta shigo tsabar neman jifa'i, Surayya ta juya a fusace tana kallon Safiyyah tace "Tunda gidan na ubanta ne ko naki uban sai ta shigo mu ga" Safiyyah tayi cilli da wayar hannunta ta fige dankwalin kanta tace "Wallahi kar ki ga na raga maki daxu saboda yaya, to yanzu baya nan cin kaza kazanki zanyi la'ada waje" Khaleesat was shock, ta kasa rufe baki tana kallonsu, Surayya ta nufi Safiyyah tana kunduma mata zagi kamar dai yanda tayi mata few hours ago a gaban cousin brother dinta, instead sai cousin din ya dinga ba Safiyyah hakuri without taking any action, dama Safiyyah a wuya take, sbda bakin ciki ne ma yasa ta dinga kiran Khaleesat ta zo gidan, Khaleesat ta zaro ido ganin yanda Safiyyah ta finciko Surayya cikin zafin nama, ba ayi wata wata ba suka fara tikar dambe a wajen, Khaleesat ta karasa ciki da sauri tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, meye haka kuke yi Safiyyah?
Don Allah ku bari" Yaron Surayya dake kan kujera sai tsala ihu yake, Khaleesat tayi kokarin rabasu taga an cillar da ita gefe har sai da ta kusa faduwa, bata sake gigin zuwa kusa da su ba, ta bude wayarta da sauri ta fara neman number Mustapha, tana kokarin kiransa taga Surayya na harin fixgo wani flower vase zata buga ma Safiyyah a kai, hakan yasa Khaleesat ta tafi da sauri ta dauke Vase din daga inda yake, Safiyyah tayi using opportunity din ta fixge vase din a hannun Khaleesat ta maka ma Surayya a goshi, sai ga jini kuma hakan bai sa sun fasa damben da suke ba, ko da Khaleesat ta kira Mustapha ashe yana hanyar dawowa, cikin few minutes sai gashi ya shigo gidan, sai shi ne ya rabasu bayan sun yi ma juna laga laga, Surayya bata daddara ba tayi kukan kura tayo kan Khaleesat zata cafkota tana cewa "Kika bata Vase ta buga min, wallahi kema sai na ci kaza kazan ki" A nan ne Mustapha ya sauke mata mari ya fincikota yace "Ko kin fara hauka ne Surayya?
Me kike son mayar da ni a kasar nan ne?" Ita dai Khaleesat ta tsorata sosai, Safiyyah na huci tace "Shegiya bayerabiyar banza kawai jaka jahila..." Bata rufe baki ba ita ma Mustapha ya kai hannu zai gaura mata mari ta kauce da sauri tana harare harare tana huci, Surayya dake kuka wiwi ta figi
an ta zuwa sama tana cewa "Wallahi sai dai ka zaba ko ni ko Safiyyah a gidan nan yau, in ko ba haka ba ni zan bar maku gidan kayi zaman auren da ita" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya ko ba komai dai ta fasa mata kai hankalinta ya kwanta ta kuma ji dadi, Mustapha ya zauna saman kujera ya dafe kai, juyawa Khaleesat tayi sum sum ta fita daga parlon wishing dama bata zo gidan ba kilan da haka bai faru ba, da tasan bala'in da za ayi kenan babu abinda zai fara fitowa da ita daga gida, Safiyyah ta figi dankwalinta zata bi ta, Mustapha ya mata tsawa yace "Kar ki kuskura ki fita daga gidan nan" Safiyyah ta fashe da kuka tana bubbuga kafa tace "Ni wallahi yaya na gaji, na gaji kuma haka, na gajiiii, dubi cin mutuncin da matarka ta min daxu kace in kyaleta, yanzu kuma daga kawata ta zo wajena in mata kitso shikenan sai ta fara kunduma mana zagi ta kamani da dambe??" Yace "Wuce dakin ki nace" Ita dai Khaleesat tuni ta kara gaba ta bar gidan.
That same day wajen karfe biyar da rabi sai ga Safiyyah ta zo gidan Khaleesat, Khaleesat ta zauna gefenta bayan sun shigo parlor tana kallonta tace "Ban ji dadin abinda ya faru ba yau Sophie, da na sani da ban je gidan ba ma wallahi" Safiyyah tace "Ai abun duniya ne ya dameni kamar in hadiye zuciya shi sa nayi ta kiranki ki zo daxu, wai fa bayan na gama yi maki gyaran gashi na koma gida matar nan kamar jirana take ta kama zagina ta uwa ta uba a gaban mijinta wai don me zan zubar mata da sauran miyarta dake kitchen, kuma fa kar kice da miya a tukunyar Khaleesat, wallahi ba komai ciki sai wani guntun miya da yayi tsami sai bugawa yake, ni kuma na wanke na dafa indomie na ci kafin in taho nan daxu in maki gyaran gashi, Ya Mustapha ya hanani cewa komai ya bani hakuri na wuce daki, a banza tunda dai shi ma har uwayensa ta zaga, shine bata daddara ba da kika zo zata sake hadamu ta zage ga yan iska sai muyi shiru muna kallonta, ni wallahi so nayi ace ma na cire mata hakora biyu ta dawo wawulo, amma dai a juri zuwa rafi wallahi sai na mata illar gaske kafin in gama karatu a kasar nan, dama tun 3 weeks ago da muka zo muka kawo maki abinci da ni da Y Mustapha ta kara kullatata ta kara tsanata tunda har yau tayi tunanin da akwai wani abu tsakaninki da Mustapha, ko ga maciji fa bama yi da ita a gidan" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannunta tace "Ki dai dinga hakuri plss Sophie wataran sai labari, da ni ce ke ma wallahi bazan dinga biyeta ba a gidan nan" Safiyyah tace "To ai ba kowa ke da matattciyar zuciyar da kare ya lashe irin taki ba, amma wallahi tayi kadan in ki biye mata, tana ce min kule zan ce mata casss don ubanta, an gaya mata ita ta isa ta shiga tsakanina da Mustapha?
Cousin dina ne fa, Uwarsa ce ta sha nono ta bar ma uwata, Babansa kuwa Cousin din babana ne halaq malaq, ina ga bai ta
a zaunar da ita ya mata bayanin nan dalla dalla bane, kuma ya ci sa'ar bana kai karar abinda matsiyaciyar matarsa ke yi min gida, don wallahi da tuni an dau mataki, amma dai bari mu yi hutu in koma Nigeria" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Zancen gaskiya ke ma fa kina da naki Safiyyah, babu ta yanda za ayi kina zaune da mata ko
an wanke wanken nan da shara baza ki ke taya ta ba a gidan, Abinda fa idan an mana mun san baza mu ji dadi ba to kar mu yi ma wani, she is also human, kuma at times bacin rai ne ke triggering wani mugun halin mutum, kece kika yi triggering din halinta a gidan, babu ta yanda zaki ji dadi wataran kanwar mijinki ta zo gidanki ta zauna bata taya ki aikin komai sai dai in kinyi girki ta deba ta ci ta ajiye maki plate, ki duba wannan lamarin fa, mu mata muna da son kanmu wani lkcn..." Safiyyah ta dakatar da ita tace "Ohh wato goyon bayanta ma kike kenan Khaleesah? you are trying to say duk abinda take min yayi dai dai ko??
To nagode, dama ke baki ta
a goyon bayan mutum a duk halin da yake ciki, in dai mutum zai kawo maki damuwarsa to ya kara dulmiya kansa cikin damuwa ne, ni kuma ban ta
a kin supporting dinki ba no matter the situation, ko Abdul da nake zagi kullum kamar
a na nake goyon bayanki an gaya maki kema baki da naki ba
in halin ne wani lkci?
Dama mistake nayi ma na zo gidan nan asirina a rufe da gidan Sandra na wuce da ba a kara bata min rai ba" Tana fadin haka ta mike ta figi jakarta ta nufi kofa kamar zata tashi sama, Khaleesat ta mike tace "Safiyyah" Banza da ita Safiyyah tayi har ta fice daga parlon ta kullo mata kofa, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna, a hankali tace "Ae shikenan"
07087865788
[5/15, 7:17 PM] khaleesat Haiydar
: Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6
HALYSAAH
By _Khaleesat Haiydar_
19....