Sashe 115
Halysaah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ba karatu a Amurka, ba Miji, ga zawarci, wannan asara da yawa take ni Aisha, wannan shi ne ga koshi ga kwanan yunwa, an ga samu an ga rashi, ina Zahra'u zata saka ranta ta ji dadi" Mama Zubaida tace "Ke baki ga haka ya korota daga ita sai kayan jikinta ba, ko er jakar hannu da ake saka waya fa bata taho da shi ba, dama a haka ya dauketa, kuma kinga ko tsinke ba a kai mata ba dama" Duk suke kwashe da dariya har da kyakyatawa, Mama Shatu tace "Sai a dawo a ci gaba da alalan da aka watsar, don ita kanta Faridan Allah ya sa
an zaman da ta dawo suka yi ba a cinye jarin nata ba, nan nan a gabanmu aka yi ta hade haden garin
anwake da su kuka da kubewa za a kai ma Khaleesat ashe ashe korota zai yi, ni anjima ma zan shiga a tsam min garin danwaken don naga da yawa suka yi" Tana dariya ta kare maganar, Mama Zubaida tace "Ae wallahi ko tsirara zan yi na gwammace inyi da dai Zahra'u taji dadi da 'ya yanta, in ke kin manta irin cin
ashin da Malam ya dinga mana bayan ya aurota ni ban manta ba, duk muka zama bora a gidan nan, baya ganin kowa sai Zahra'u tunda da asirinsu na buzaye ta shigo gidan, banda dai dama tun asali idonmu ya bude da Malamai ai da tuni ya sake mu tun bai samu karayar arziki ba, hatta kayan dakin da ya siya mata sai da na zaga na koma kasuwa na tambaya aka ce min nata duk yafi namu tsada, gashi yaranta su ne 'ya yan so barin Khaleesat din nan ai mun sha bakin ciki iri iri Shatu, Ita fa har Umra tayi sannan ga Hajji, mu kuwa iya Hajji kawai muka je mu ka yi tsabar ya maida mu 'yan iska" Mama Shatu ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Ki bar tuna min wannan takaicin Zubaida, banda a tsaye muke ai da wani labarin ake yanxu ba wannan ba, haka mu ma muka yi ta hadata da Malam da taimakon asiri, amma shegiyar bata yi zuciya ta koma kasar su ba da ya fara cin ubanta a gidan, in sha Allahu yanxu ta fara ganin bala'i ita da zuri'arta su da jin dadi ko farin ciki har abada, hatta yan biyun nan ya kamata mu fara mi
a sunansu yanxu kar lokaci ya kure, don naga wani farin jinin jama'a da suke da shi, duk inda suka shiga sai an tankasu ayi ta nan nan da su" Shigowar Nenne gidan yasa suka yi shiru, duk suka gaisheta ta amsa ba tare da ta kallesu ba ta nufi dakin Umma da er ledanta a hannu, duk suka ta
e baki suna bin ta da kallo har ta shiga dakin, Umma da Aunty Farida suka gaida Nenne bayan ta shigo dakin, Nenne ta amsa bayan ta ajiye ledan hannunta tace "Ina Khaleesar take?" Aunty Farida tace "Ta shiga wanka" Nenne tace "Atoh dai, dama ina zata tsaya bakin cikin shege ya kasheta, harkar gabanta kawai zata ci gaba da yi kamar babu abinda ya faru, da auren wannan gansamemen mutumin da rashin aurensa ai duk daya, kuma mu muka cusa mata shi ba sonsa take ba wallahi, yanxu banda ni da ku waye yasan tayi wani gantalallen aure ko da wani ya fito yana son ta, banda dai gulma tayi ma jama'ar Mariri katutu, ai kawai ce ma Ali zan yi ya siyar da gidan nan da nawa gidan mu koma ko Rijiyar Lemo ne" Dukawa tayi ta kwance ledan da ta ajiye tace "Gashi nan, kasuwa na aiki almajirina ya siyo min kayan ciki me kyau nayi mata farfesu ta sha ta mance abinda ya dameta, saki ai ba kanta farau ba, mu ma duk ai an ta
a sakin mu, uban Ali saki nawa ne bai min ba, sai da igiya daya ya rage mana sannan muka nutsu muka zauna har mutuwa ta raba" Wata mata ce tayi sallama bakin kofar dakin Umma, Umma ta amsa mata, matar ta shigo tana gyara yakunannen gyalenta, ganin Nenne ta duka har kasa ta gaisheta, Nenne ta amsa tana rufe farfesun da ta kawo ma Khaleesat kar matar ta barbade farfesun da gyalenta, Bayan matar sun gaisa da Umma tace "Ashe abinda ya faru kenan Ummansu Khaleesah?" Nenne ta juya ta kalleta tace "Me ya faru?" Matar ta langwabar da kai cikin rashin jin dadi tace "Mutuwan auren Khaleesah Nenne" Nenne ta mike tsaye tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, mutuwar auren wace Khaleesar?
A ina kika ji auren Khaleesah ya mutu?
Na shiga uku na lalace, wato matan Mariri baza ku canza halin ku na tsugudidi ba ko?
To daga ke har wanda ya gaya maki kun ci kaza kazan ku yan iska kawai shegu, tashi ki fita ki ba mu waje, sai dai ki ga mutuwar aure a dakin ki ko na uwar ki, kaji min mata dai munafuka, uban mutuwan auren Khaleesah, fita ki bamu waje" Da sauri matar ta fita daga dakin ta saka takalmi wari da wari ta bar bakin kofar, Nenne na huci ta kalli Umma tace "Ke kuma Las spika ki ka dauka kike shelan an saki Khaleesah?" Aunty Farida ta tabe baki tace "Ina fa Nenne, mu ma kawai gani muka yi ana ta shigo mana tun da gari ya waye, wai an zo Jaje, wa enda suka fitar da labarin ai su ne babban munafukai" Nenne na share zufan goshinta tace "Shatu da Zubaida kenan, babu me fitar da zancen nan sai su" Tana kai wa nan ta fice daga dakin, kafin ta fito dama su Mama Shatu duk sun shige dakunan su da sauri bayan sun ji abinda Nenne tayi ma matar da ta fita daga gidan, nan tsakar gida Nenne ta tsaya babu abinda ta manta bata gaya masu ba, zagi kam sun sha har sun gode Allah, Allah ya isa shima tayi masu kwando kwando, daga karshe tace "Kuma in har Ali ya dawo gidan nan anjima bai dau matakin fitar masa da sirrin gida da ku ka yi ba wallahi sai dai ya zaba ko ni ko ku, da dai in zauna da surkai magulmata munafukai gwara in sallame ma duniya Ali in shi bazai sallama maku ba, to ai ita Khaleesar ta samu mashinshini har tayi auren ta fito, ku kuma da naku 'ya yan ke zube kaman gwanjo babu mataya fa?
Dama nace ma Ali in har bazai bada su sadaka ba to ni a dena nuna su ace jikokina don kunya nake ji, ko kuma in tattara in bar masa Maririn in har bazai samar ma narka narkan 'ya yanku mafita ba, yanxu in na Jera da Labeebah ba sai ace ita ta haifeni ba, sannan kwata kwata basa wuni a gidan nan ban san inda suke zuwa ba, sai mutum ya shigo sau dari bai gan su sau biyu ba" Khaleesat ta fito daga bandaki tana rike da Shower gel dinta ta nufi dakin Umma, Nenne ta bi ta a baya tana cewa "Kin fito Khaleesah, mu je ga farfesu can na maki" Sai da suka shiga dakin sannan Khaleesat ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace "Kar fa ki ce zaki sa damuwar shegen a ranki kin ji?
Allah ne ya dubemu ya rabu dake cikin aminci bai maki wata illa ba, dama kuma ance min uwarsa har tsafi take yi, kinga hada zuri'a da irin wannan mutane ai abun tsoro ne, kar ki saka komai a ranki, rabuwan shi ne mafi alkhairi a gare ki dama an gaya min" Khaleesat dai ta zauna gefen gadon Umma tana shafa cream dinta, Nenne na kallon Umma tace "Ke kuma duk wanda ya shigo maki jaje baki koresa ba Allah ya isa kema, ai mutum daya na shigowa kika rufe ido kika koresa komawa zai yi ya sanar ma sauran, shikenan babu wanda zai sake shigo maki, ni kin ga tafiyata inje in nemi abinda zan ci da rana" Daga haka ta fice daga dakin.