Sashe 9
Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali Aunty ta ja kafafunta d'aya daga cikin bedrooms d'in parlour'n ta shiga, ba bedroom d'in kwanan ta ba, a nan tayi wanka.
ta fito tana shirin yin sallar magriba da aka soma kira.
Daddy ya shigo da Feeryal a kafad'ar sa tana bacci.
"Yau an sauya mana gurin kwana ne dama an jima ba'a sauya ba."
murmushi ta yi "Ba yau ba wanka kawai nayi a nan d'in zan koma can."
"Feeryal tayi bacci tayi ta mita da alama yunwa take ji ko za'a tasheta tasha mama ta koma."
"A'a abarta tayi bacci sai ta tashi, Daddy ka shinfid'a ta a can zanje nayi salla a bedroom ina."
ta nuna kan bed d'in d'akin.
Da sauri tayi waje yana kwantar da ita yabi bayan ta.
"Fad'imatu."
yakira sunan ta tana daf da shigewa d'aki.
taja ta tsaya tare da waigowa gare shi.
yakaraso in da take, idon sa a kanta ya ce
"Wai me ke faruwa ne me ke da min ki? akwai abin da ke damun ki nafi kowa sanin ki."
ido ta d'an lumshe ta bud'e su a kansa sannan ta ce
"Daddy nafara shiga kokonto akan Feeryal, acikin kwanakin nan ina ganin wasu sauye-sauye tare da ita, idan na aje ta naje nayi aiki na sha zuwa nasame ta tana wasa ita d'aya tayi ta dariya kamar wanda take kallon wani da ni bana ganin sa;
da fari ban d'auki hakan akomai ba nasan yaro yakan yi haka, amma yau Feeryal ta bani tsoro!."
da sauri ta waiga jin kamar an wulga ta bayanta.
ido Daddy ya kura mata ganin yadda taja numfashin tsoro.
hannunsa ta rike gam sannan ta ce
"Bakaji kamar an wuce ba?."
kai ya girgiza ya ce
"Banji ba."
sai kuma ya janyo hannunta suka shige cikin bedroom.
a bakin gado ya zaunar da ita yana tsaye a kanta ya dafa kafad'arta, ya dube ta da kyau sannan ya ce
"Fad'imatu, kar dai ace maganar mutane yafara tasiri a kanki? kada ki bari kururuwan jama'a yayi galaba a kanki, ya akayi kika mance da addu'o'in ki, kefa kk tunasar da ni wani lokacin,
duk in da bawa yake shed'an yana nan a gurin, haka aljanu duk in da muka sa kafarmu suma suna gurin, imma shed'anunsu imma na kirkinsu, sai dai mu bama ganin su, akwai hanyoyin da ake bi dan nisanta kai daga sharrin shaid'an ibilis da kuma shaid'anun aljanu, ina sammanin sai dai ki fad'awa wani dan kinsan hanyoyin,
babu abun da shaid'an bazai iya ba ko kin mance wa'azin malam Aminu Daurawa ya ce
shaid'an yakan zuba kasa akan gado, mata tayi shinfid'a tayi komai dan ya had'ata fad'a da mijinta?."
ya karashe maganar da murmushi.
kai ta jinjina ta ce
"Amma Daddy kasan ya na shigo na tadda Feeryal kuwa, gadon ta yana lilo a sama fa tana ta dariya, ina tsaye ina gani kuma gadon ya sauko."
d'an shiru ya yi alamun nazari sai kuma ya d'an dara ya ce
"Da alama dai yau bakiyi Azkhar d'in yammaci ba, idan kikayi salla kiyi, kisa a ranki babu komai gizo ne kawai, sa rai akan abu yakansa kaga abun kamar ya faru, yau she kika fara yarda da maganganun mutane iye Fad'imatu?
kada ki bari maganganun su ya yi tasiri a zuciyar ki,
har yayi nasarar hanaki taimakon rai da kika d'au himma."
"Ban tab'a yarda da maganar mutane ba, ban tab'a jin Feeryal amatsayin aljana ba,
kawai abin da nagani ne yasani shiga shakku."
Nurmushi Daddy ya yi dan son share mata shakkunta yakuma karfafa mata guiwa ya ce
"Gizo ne kawai kinsan wani lokacin haka d'an adam yake musamman wad'an da damuwa tayi musu yawa a kwakwalwa,
yau dai da alama kin shiga sahun su, bari na tafi masallaci kada na rasa salla babu komai Ammie'n Feeryal kiyi addu'a kinji."
Kai ta girgiza tare da sauke numfashi, yafita zuwa masallaci ita kuma tamike domin gabatar da sallah.
Tajima tana addu'o'i har sallar ishe yasame ta kan sallaya.
bayan ta gabatar ta mike ta shirya ta fito, tana jin zuciyarta wasai nutsuwa na shigarta.
D'akin da Feeryal ke bacci ta shiga, ta isketa tana ta baccinta. ta d'auko ta, ta mai da ita bedroom d'in ta.
Washegari da safe bayan Aunty tagama kimsa side d'inta da taimakon Baba Rabi,
kamar yadda suka saba idan Daddy yana gurin ta,
tun kan Daddy ya fito parlour Baba Rabi take shigowa side d'in.
ta gyara parlour zuwa kichin, ta tanadar mata da duk abin da tasan zatayi amfani da shi na breakfast a kusa, sannan ta koma b'angaren su na ma'aikatan gidan.
dan a iya nan aikin ta ya tsaya dan ko gyaran bedrooms d'in cikin side d'in Aunty ke yi da kanta, idan kaga Babaa Rabi tayi girki; to Daddy baya side d'in.
bayan Aunty ta fito ta wuce kichin ta tadda Baba Rabi ta tanadar mata da duk abin da zata bukata kusa, nan ta soma had'a breakfast d'in da tasan Daddy ya fi so.
Bayan ta gama ta kwaso hadaddun breakfast data shirya wajen kala uku ta kawo su kan dinning.
ko da ta koma bedroom ta tadda Daddy ya farka,
ta wuce bathroom ta had'a masa ruwan wanka.
bayan yafito ya shirya yafito parlour.
a tare suka yi breakfast cikin plt d'aya kamar yadda suka saba.
Bayan sun kammala Daddy ya dawo parlour yana kallon labarai.
Aunty ko na kichin tana wanke kwanukan da suka b'ata.
kukan Feeryal da tajiyo ne yasa ta fita da sauri tana fad'in
"An tashi ke nan."
Daddy da ya mike zuwa d'auko ta ganin fitowar Aunty yasashi komawa ya zauna.
Da sauri ta kara cikin d'akin ta d'auke ta tana jijjigata.
"Ya isa ayi shiru antashi ne yunwa ake ji ne?."
tana fad'i tana bubbuga bayanta.
ta zauna bakin gado sai da ta rarrasheta tayi shiru,
sannan ta mike ta aje ta a kasa tana fad'in
"Nasan hali zauna a kasa bazan aje ki a kan gado ki fad'o ba, ba'a iya rarrafe ba sai rawar kai, zauna muzo muyi wanka, yau muyi anan ba sai munje bayi ba."
ta shige bayi ta had'o ruwan wankan a bawo mai d'an girma ta fito.
Feeryal na zaune a gefe tana ta wasa da abin wasan da ta saka mata shi a gabanta.
d'an gajeren tsaki Aunty taja, tuno da bata d'auko sabulu ba ta mike ta koma bayin.
Ta fito d'auke da sabulu turus taja ta tsaya bakin kofar bayin tana kallon Feeryal da ta ganta cikin bawon wanka, ga kuma kayanta a gefe an cire mata, tana zaune cikin ruwa sai wasa take tana dariya.
tana mika hanu kuma alamun a d'auketa tana kuma kallon gabanta tana cigaba da dariyar da kuma mika hanun ma wanda ita bata ganinsa.
Bin cikin d'akin tayi da kallo tana tunanin ko wani ne ya shigo ya tub'e mata kayan ya sata cikin bawun d'in.
babu kowa cikin d'akin babu wani alamar da ya nuna wani ya shigo daga d'an shigarta bayi d'aukar sabulu zuwa fitowarta, da bai wuce second 40 zuwa minti 1 ba.
ta kuma san ba Daddy bane dan shi bazai barta a cikin ruwa mai yawa haka yafita ba.
Numfashi taja sai kuma ta d'an saki murmushi ya yin da take karanto wasu addu'o'i cikin ranta,
tana fata idan abin da take tunani hakan ne to surabu da ita lafiya dan ita bada niyyar cutarwa ta d'au ko ta ba.
ta karaso in da take tana fad'in
"Nab'ata lokaci wajen d'auko sabulu ko? bari nayi miki wankan ki ko Baby'n Ammie'n ta."
kamar wacce ta fahimci abin da take fad'a tashiga bubbuga hanunta cikin ruwan tana yin irin yadda yara suke idan suna cikin ruwan wanka suna wasa da shi.
da karfin addu'ar da take taga ma yi mata wanka, kana ta shirya ta cikin kaya masu kyau da tsada.
sannan ta d'auko ta suka fito parlour bayan ta gyara in da suka b'ata.
Daddy na ganin su ya mika hanu itama ta wage baki ya karb'eta yana cillata sama, tana kyakyata dariya.
Aunty ta bisu da murmushi.
har Daddy ya fita batayi masa hirar abin da tagani ba, dan tasan yanzun ma ce mata zai yi gizo ne...
Da yamma Aunty na kichin tana aiki, Feeryal kuma na parlour tana wasa a zaune da kayan wasanta.
lokaci zuwa lokaci take fitowa duba ta.
ta kwaso kulolin abinci kan babban tray tanufi dinning da shi.
tun kan ta karaso dinning d'in take kallon ikon Allah.
Feeryal ce zaune a tsakiyar dinning hannunta biyu cikin bama tana sha tana kwab'awa, ta kwab'a bakinta da fuskanta gaba d'aya,
sai ta kwamulo shi ta mika hanu alamun tana mikawa wani sai a karb'a sai dai bata ganin mai karb'ar sai dai taga babu komai a hannunta.
A hankali Aunty ta juya ta dawo parlour ta dire tray'n kan table d'in parlour,
sannan ta koma kichin da sauri bata bari ta ganta ba.
suka cigaba da gyara kichin d'in tare da Baba Rabi.
bata fitoba sai da suka gama komai suka fito tare da Baba Rabi.
Abin mamaki a zaune a tsakiyar parlour in da ta aje ta da fari tana wasa, agurin yanzu ta tarar da ita, zaune tana wasa, jikin ta tsaf babu d'in komai.
kallon saman dinning tayi shima a kimtse komai na zaune a gurin zamansa.
Baba Rabi tayi wa Aunty sai da safe tayi waje bayan ta gama yi wa Feeryal d'in wasa,
har Aunty ta juya zata wuce bedroom sai kuma ta juyo ta dawo inda take ta mika hannun zata d'auke ta ba shiri ta cire hannunta a cikin ta tayi wani irin mikewa ta ja da baya da sauri jiki na rawa.........!
Mommyn Twins ce
🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ?*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇ðŸ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*Bismillahirrahmanurrahim*
🅿�5