← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 52

Sashe 35

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk in da Maryam zata je da ita take zuwa duk wanda ya gansu tare kuwa sai ya tambaye ta a ina ta samo ta, idan ta ce dasu d'iyar Aunty ta ce suyi ta shan mamaki.
Wad'an da suka san Aunty'n nata kuwa da mijin da take aure sukan gaskata hakan a take, dan sanin ko waye mijin Aunty'n nata.
dan cewa suke kud'i zai iya komai wata kila akwai dangantakar nesa da kud'i ya iya janyo sa.
ma'ana ya na da dangi da suka shafi wata kabilar ba hausa ba, wan da har ya kaiga samun d'iyar da ta yiyo kamarsu.

Satin FEERYAL guda a Abuja a ka samar mata makaranta ta fara zuwa.

Lagos

Tun da Ajeemal ya sami labarin barin FEERYAL gidan gaba d'aya yaji ba dad'i.
Miemie ma har kuka tayi ta kaurace wa sashin kakan nasu, ko wani abin tab'awa Ammah ta bata ta kai wa Hajiya, sai dai ta je ta kaiwa Ameerah ko Sahla ko Nabila ta ce su kai mata, inji Ammah'n ta.

Ajeemal ne zaune a parlor'n Mommy yana cin abinci.
Mommy na hakimce a kan kujera tana kallon TV.
su Ameerah da Sumayya suka shigo da uniform a jikin su dawowan su daga school ke nan.
tun kan su karaso parlour'n Sumayya ta ce
"Mommy kiji wai Ameerah zata zana paper a primary 5, na ce ta bari next year muma sai da muka kai 6 kafin muka zana, wai ba wanda ya isa ya hanata, dan taga kawayen ta sunce zasu zana this year."
baki Ameerah ta murgud'a mata cikin tsiwa ta ce
"Sai na zana sai ki hana ai ina ruwanki da ni 'yar sa ido."
Mommy tayi saurin cewa
"Ina ruwan ki da ita Sumayya in tace zata zana,
kinsan dai Ameerah ba jahila ba ce kwakwalwar ta na ja,
ko a primary 4 take tace zata je JS kinsan dai zata iya ko, babu abinda 'yan JS d'in zasu nuna mata."

Ajmal daya bi Ameerah da harara ya ce
"Mommy wannan ce me kwakwalwar, dan baki tab'a zaunar da ita bane, in banda rashin kunya babu komai a kanta,
ai mai ƙwaƙwalwa sai FEERYAL yarinyar akwai ilimi har mamaki basirar ta yake bani."
da sauri Mommy ta katse shi ta hanyar buga masa tsawa
"Rufamin baki ita FEERYAL d'in kanwar uwarka ce ko kanwar uban ka,
sai taje can ta karata da kwakwalwar ta mara amfani dan da uba ake ado, mun jefar da kwallon mangoro mun huta da kuda,
kada ka sake ambata min sunan mayyar aljanar can,
ni harma na mance da ita,
shine bari ka tuno min da ita kana so ka b'ata min rai,
to kafita idona na rufe kada na sake jin sunan 'yar nan a bakin ka, bare har ka danganta min ita da 'ya'yana!."

Kai ya girgiza ya ce
"Allah baki hakuri Mommy."
ya mike ya d'au plt d'in abincin sa ya yi waje.
ta bisa da harara tana fad'in
"Ai ba'a barka banza ba, sai na mike tsaye a kanka."

Zaune Daddy ya ke cikin parlour'n sa yana kallon labarai a TV, kira ya shigo d'aya daga cikin wayoyin sa da suke zube kan table d'in gaban kujerar da yake kai.
Dr Omar sunan daya bayyana kan screen d'in wayar kenan.
ya janyo wayar tare da picking na call d'in,
ya kai wayar kunne tare da yin sallama.
da sauri cike da girmamawa Dr Omar ya amsa sallamar yana d'aurawa da fad'in
"Barka da warhaka ranka shi dad'e, ya gida ya kokari ya ji da jama'a."
"Alhmdulillah, Dr Omar ya aikin ya masu jiki?."
"Alhmdulillah gashi nan muna ta fama kam sai godiyan Allah, guri ya kacame, Alhaji dama akan batun mu na rannan ne na kuma kiran ka, Allah yasa dai ban matsa da yawa ba,
a gafarce ni dole ne yasa ni hakan,
dan Allah Alhaji a taimaka a sake mana magana da Dr mu asibiti tana bukatar sa."

Daddy ya gyara zama tare da sauke idanunsa kan kofa. inda yajiyo muryar Aunty da ta shigo da sallama kana ya ce
"A'a wai har yanzu bakuyi magana da shi bane, dana ji shiru ai na d'auka kun rigada kunyi magana."
"Kwanaki munyi magana da shi har ya amsa min kan cewa zai dawo, to ganin shiru sai na sake tuntub'arsa da batun,
to dai har yanzu ban sami kwakkwaran amsa a gurin sa ba, kasan mutumin namu sai ana had'awa da lallami, idan ya baud'e bazamu iya karkato shi ta dad'i ba,
yanzun nan muka fita mitin all Doctor's gaskiya na fahimci irin gudunmawar da zamu samu 100%
idan yana cikin mu, gaba d'aya mitin d'in nan a kansa ya kare, na tayaya zamuyi ya dawo cikin mu,
kwanaki munyi taro a government house mai girma Gwamna da kansa sai da ya tambaye sa,
a ranar ma sai da na kirasa na sanar masa,
sai dai is not serious ni nasan baya bukata dama can ni nayi ta tirsasa masa,
da bibiyar sa har hospital d'in sa,
kafin ya yarda ya fara zuwa general hospital,
ni da kaina na shigar da takardun sa badun yaso ba,
dan Allah Alhaji a samana baki cikin lamarin muna bukatar sa."

Daddy ya jinjina kai ya ce
"To ba damu insha'allah zamuyi magana da shi."
Dr Omar ya yi ta masa godiya kana ya yi masa sallama ya kashe kiran.

Daddy ya maida hankalin sa kan Aunty data karaso ta zauna gefen sa.
ta tsiyaya masa had'in lemun da ta had'a da kanta cikin kyakkyawan cup, ya yi sanyi kuwa amma ba sanyi mai cutarwa ba,
ta tad'ago ta mika masa.
ya gyara zamansa da kyau ya karb'i cup d'in yana binta da murmushi sannan ya ce
"Nagode Ammie'n FEERYAL."
murmushi tayi masa tana rufe ragowar lemun.

Ya kai cup d'in bakinsa ya kurb'i lemun ya lumshe ido yana jin dad'in sa na rasa cikin bakin sa.
kana ya bud'e idanun nasa a kanta ya ce
"Ya yi dad'i sosai fa, kunyi waya da FEERYAL yau kuwa? nayi ta gwada lambar hajja Umma baya tafiya, Alhaji kuma ya ce min yana Kano yau sai gobe sai koma."
"Kafin na zo nan munyi waya da ita a wayan Maryam, nima na kira wayan Hajja Umman bai tafi ba, Maryam take ce min wai FEERYAL d'in ce ta cinye cajin wayar nata da game."
dariya Daddy ya yi ya ce
"Da kyau mana, gobe zansa a kai mata sabuwar waya,
sai tayi ta buga game ta barwa Hajja Umma nata."

Murmushi Aunty tayi tare da mikewa tsaye, tana jin kewar d'iyarta, damma kullum suna tare a waya suna kallon junan su ta video call.
Daddy ya yi saurin fad'in
"Ina kuma zakije Fad'imatu?
ki zauna mana ki tayani hira."
"Daddy ka shanye lemun nan duka akwai wani a fridge zan karo maka, anjima ka shigo kaci abinci dan naga alamun kafara jin yunwa."
tayi maganar tana son kawar da nasa batun, dan tasan yanzu haka Umma Karima tana hanyar zuwa side d'in nasa, dan itace da shi, kuma tana da tabbacin taga shigowar ta, dan takan aje 'ya'yan ta a hanya suna mata gadi.
tayi saurin nufar kofa tun kafin ya dakatar da ita.

Aiko tana sa kai sukayi kicib'us da Umma Karima.
kallon tuhumar me ya kawo ta sashin baran kwanan ta ba Umma Karima ta bi Aunty da shi.
itako batama bi ta kanta ba tayi gaba a binta,
tana jin miyagun maganganun da Umma Karima take aika mata su bata ko waiga ba.........!

Mommyn Twins ce

🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺

*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*

( _Book 1_)

*~Free page~*

*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

🅿�16

Rayuwa mai shud'ewa, mai tafi a sanu a sannu.
bayan wani lokaci mai tsawo....
rayuwa mai kyau da tsafta FEERYAL take gudanar da shi yanzu, babu tsangwama bare kyara,
tsantsar kauna da soyayya mai had'e da kulawa Abba da Hajja Umma da Maryam da duk wasu danginsu suke nuna mata.
in banda su da suka san wace ce ita babu wani baren da yasan asalinta,
abinda kowani bare ya sani shine ita 'yar Hajiya Fatima ce kuma d'iyar Alhaji Abubakar Fiya jika ga Tahir Abbas.

Sannu a sannu FEERYAL nakara girma da wayo ya yin da kyawunta ke dad'a karuwa yana tsole idon duk mai kallonta, wanda hakan yake son zamowa barazana a rayuwar ta.
dole Alhaji Tahir Abbas ya samar mata da security bayan direban da yake kaita makaranta ko kaisu unguwa idan zasuje da Maryam.
security na tare da su sabo da harin da wasu fitsararrun maza suke kawo mata.

Lagos
Da misalin karfe 1 da rabi na dare.
(Zero Club)
baka jin ko mai sai tashin sautin kid'an daya karad'e ciki da wajen Club d'in.
maza da mata ne a cakud'e, suna ta tikar
rawa cike da fitsara suna rungumar junan su.
gaba d'ayan su 'ya'yan manya ne, 'ya'yan masu kud'i masu fad'a aji.

Wasu kuma suna zaune suna ta aikin bushe-bushen shisha ya yin da 'yanmata ke makale a jikinsu, suna ta badakalar su.

Zaraddin dake zaune ya baje kafa,
ya yi doguwar mika, kana ya aje mabusar shishar dake rike a hannunsa yana aikin busawa,
ya janye budurwar dake rungume da shi, tana ta aikin shafa shi.
ya mike yana duban agogon dake daure a hannunsa kana ya ce
"Beb zan shiga gida 2 saura yanzu nasan sunyi ta kiran wayoyi na ma suna mota."
mikewa tayi ta sakalo hannayen ta a wuyansa ta narke murya tare da kashe masa ido irin na gogaggun 'yanmatan bariki.
"Din wai yaushe ne zaka waye kana babban yaro ace kamar kan nan wai har yanzu ba'a dai na sama ido a gida ba,
me zai hana mu kwana a nan kawai."
hannunsa ya tura cikin rigarta yana wani sakin murmushin gefen baki, sannan ya zaro hannun ya d'an ture ta a jikin sa.
Chapter 35 · 0% Book details