← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 52

Sashe 4

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Daddy ya girgiza sannan ya ce
"Adai canza mata wani gurin dai-dai ta huce, ta ya za'a ce a maida ta cikin ruwa kisan kai ke nan zamuyi,
yarinyar nan ba aljana ba ce mutum ce, imma aljanar ce iyayen ta suzo su d'auke ta anan ba sai an kaiga cutar da rayuwarta ba,
sannan idan aka rabata da Fad'imatu itama an cutar da rayuwarta,
dan yanzu tamkar mai sabuwar jego take."
"Yaya to kayi wani abu dan Allah dan gujewa fushin hajiya."
cewar Abbieh, kai Daddy ya girgiza kana ya ce
"Insha'allah."

Aunty na zaune tayi jigum Daddy ya shigo, ya zauna gefen ta.
da sauri ta dube shi jiki a sanyaye ta ce
"Hajiya bata hakura ba ko?
dan Allah Daddy kar a rabani da Feeryal wlh ina son ta."
takarashe maganar da damke hannunsa murya a marairaice tamkar zata zubda kwalla.

Hannunta yakuma rikewa cikin nashi kana ya ce
"Insha'allahu baza'a rabaku ba nayi miki alkawari."
wasu hawaye ta share ta ce
"Nagode Daddy." murmushi mai sauti ya yi tare da jan hancinta
"Ammie'n Feeryal a kwantar da hankali haka a daina damuwa da yawa."
kai ta girgiza tana mai da masa murmushin.

A sashin Hajiya bayan fitar su Daddy da d'an jimawa, Hajiya ta cewa Farida taje ta duba mata aljanar tana nan har yanzu ko an tafi da ita.
ko da Farida taje sashin Aunty'n a kulle yake tadawo ta shaidawa Hajiya.
Hajiya tayi kwafa dan a zaton ta sun tafi mai da jaririyar in da suka d'auko ta ne.
ta gyara zama ta soma cin abincin da kulu mai aikin ta takawo mata yanzu,
tana fad'in
"Iya shegen banza da raina da lafiya ta ina gidan wai sai abin da Fatima ke so za'a yi,
rashin haihuwa hauka ce, da zata fara bin teku tana d'iban 'ya'yan aljanu tana kawo mana cikin gida;
wan nan badun daga gidan arziki tafito ba sai na ce wani muguntar take son kitsawa,
takawo aljanu su kwashe mana dukiya su kai mata gidan iyayenta."

"Hajiya wai ashe aljana Hajiya Fatima ta kawo wlh kar kiga yadda na razana aljana kuma a cikin gidan nan, to ita meye gamin ta da aljanu kuma."
cewar Kulu tana zama kan kujera d'an nesa da Hajiya.
Hajiya takai loman katon nama baki tana fad'in
"Niman jaraba mana da niman ganin bayan mutum, to ni nafi karfinta da jikokina,
sai dai taje can ta karata da aljanun, ba dai a gidan nan ba kam, je ki kawo min lemon gorar nan mai d'an sanyi."
Kulu ta tafi tana rike hab'a da mamakin lamarin.

Kwanan Feeryal uku a gidan batare da kowa yasan tana nan ba, dan kowa ya yi zaton da hajiya ta tada bori an mai da ta in da aka d'auko ta.
itama Hajiyar sam batasan tana nan ba.

Umma Karima ce cikin Bedroom in Daddy, shigowarta kenan bayan komawar ta part inta da asuba, data kwana a sashin nasa,
anje anyi wanka an cab'a kwalliya, an shafo wasu turaruka masu tsayawa a kuwa.
ganin baya side d'in gaba d'aya, ta koma side d'in ta,
ta tura babbar 'yarta Saddiqa taje ta duba mata Daddyn su yana part d'in Aunty'n su.

A bakin get in shiga side in Aunty suka had'u da Ajeemal zai wuce side d'in Hajiya.
yana ganin ta ya sai da ta.
"Ina zakije?."
ta ce "Umma ce ta ce naje na duba Daddy a side in Aunty."
ya ce "Wuce ki koma kice baya nan."
baki ta zumb'uro, tana ganin wucewar sa da gudu tayi cikin side d'in.
tana shiga parlour'n Aunty kai tsaye ta wuce cikin bedroom inta babu ko knocking bare sallama.
Aunty na zaune bakin gado tana shirya Feeryal data yi mata wanka,
jin an turo kofa yasata d'agowa tana duban mai shigowar.
ganin Saddiqa ce, ta girgiza kai tana fad'in
"Saddiqa bana ce in zaku shigo kurika yin knocking da sallama ba, ba kyau shigowa d'aki kai tsaye batare da yin sallama ko niman izini ba,
to ya akayi?."
Aunty tayi tambayar tana mai da hankalinta kan shirin da take yiwa Feeryal.
Saddiqa ta juya ta fita bare da ta ce komai ba, kai takuma girgiza wa ta cigaba da abin da ta ke.

Da sauri ta koma side d'in su, tun kan takaraso in da Umma Karima ta ke tashiga fad'in
"Umma Umma Umma wlh Aunty tadawo da aljanar nan, naganta tana sa mata kaya."
huf Umma Karima ta mike ta ce "Ke wai da gaske kinga yarinyar nan a sashinta, eh lallai Fatima anyi bakar munafuka wato boye 'yar tayi,
ko komawa tayi takuma d'auko ta, to wlh sai ta bar gidan nan."
tayi waje fuuu sai sashin Hajiya.

Kirji Hajiya ta buga da jin abun da Umma Karima tazo dashi.
Hajiya ta mikawa Umma Karima waya tana fad'in
"Lalub'o min lambar Abubakar yanzu-yanzun nan, wai ni Abubakar zai maida mutumiyar banza, yazab'i tsintacciyar aljana a kai na."

Daddy na d'aga wayar Hajiya tafashe da kuka tana fad'in
"Ni zakayiwa haka Abubakar wlh yau babu abin da zai zaunar da ni a gidan ka, yanzu-yanzun nan zan bar maka gidan ka,
kacigaba da zama da matarka da bakason b'acin ranta da aljanar da ta tsinto."
Hajiya ta kashe wayar tana sharb'ar hanci, tamike ta nufi bedroom d'in ta tana fad'in
"Ina zan iya zama da annoba a gida d'aya, gara natattara inawa-inawa na koma Yalwa yafi min kwanciyar hankali."

Umma Karima ta saki murmushi akasan ranta tana fad'in
"Fatima ke karamar makira ce."
tamike tafice takoma part d'inta.

Cikin hanzari Daddy yashigo side d'in Hajiya, yana shiga parlour'n ta,
Hajiya nafitowa janye da akwati.
da sauri ya isa inda take yana fad'in
"Dan Allah Hajiya kiyi hakuri kada ki tafi."
"Bani guri da alla! in zauna inmaka me?, ni da bani da mutunci agurin ka,
gara nabaka guri kacigaba da zama da wad'an da kake ganin su da kima,
ina dalili ina mafari zama da aljana guri guda, ina bil adam, kai da kazabi haka sai kayi ta zama da ita,
amma kasani idan jikokina suka sami wata matsala bazan yafe maka ba!."

Da sauri Daddy yarike akwatin ganin tana kokarin tafiyar da gaske ya ce
"Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki gafatarce ni, kada ki tafi, za'a maida ita inda aka d'auko ta dan Allah kiyi zamanki."
"Ni Abubakar ai ka gwada min iyakata aljanar ruwa tafiye maka ni,
ni uwar da na haife ka naci kashinka, ni Abubakar ni."
Hajiya tasaki kuka tana sharb'e hanci da bakim mayafinta.
akwatin ya karb'a a hannunta yana
"Yi hakuri dai Hajiya yanzu za'a fita da ita."
yaja akwatin ya maida shi ciki bedroom, yafito ya isketa zaune a parlour.
hakuri yacigaba da bata sai da yaga ta d'an sauko kafin yafita.

A b'angare Aunty lokacin da Hajiya ta kira Daddy shigowar sa side d'in ta kenan, ko zama baiyi ba yafita zuwa kiran Hajiya.

Kuma jin motsi yasa Aunty fitowa, ganin Daddy ne ta karaso in da yake jiki ba kwari.
murmushi ya yi mata domin karfafa ta, fuska ta dan marairaice ta ce
"Hajiya bata hakura ba ko?."
zama ya yi a bakin gado yana fad'in
"Zanji da ita zaki rayu da Feeryal insha'allah, nayi miki alkawari."
zama tayi gefen sa kana ta ruko hannunsa tana jaddada godiyar ta a gare sa.
tana mai alfaharin kasantuwar sa a matsayin abokin rayuwarta,
dan bai tab'a rageta da wani abu ba, duk abin da ta nima a gurin sa tana samu; hakan kuma baya rasa nasaba da so da kauna da kuma yardar da yake yimata.

Wanda itako take saka masa ta hanyar nuna masa tsantsar kulawa mai had'e da zallar soyayya da nuna damuwa kan abin da ka damu da shi.

Hakan yasa abokan zaman ta suke ganin tagama mallakesa ta hanyar asiri, wan da sam abun ba haka yake ba, Hajiya Fatima babu abin da ta tsana take kyamatar sa sama da bin bokaye da malamam tsubbu.

Hajiya Fatima mata ce mai hakuri da juriya gami da kawaici, tana da matukar hakuri ga ladabi da biyayya; tsafta iya girki iya kwalliya, iya tafiyar da miji yadda ya kamata, uwa uba ruko da addini.
shiyasa tazamo lamba d'aya a gurin maigidan nata wato Alhaji Abubakar Fiya.

Da yamma Daddy yashigo sashin Hajiya, Hajiya na ganin sa ta b'ata fuska, ya isa ya zauna yana yi mata barka da warhaka.
ta katse shi da fad'in
"Har kun dawo daga mai da aljanar in da kuka d'auko ta, ko yaya?
wlh Abubakar ka kiyaye ni in ban da rashin hankali ina kai ina taimakon aljanu,
kai da bakada da wata sari a jikin ka, ko wannan maganin tsari idan nabaka kayi amfani da shi saboda makiya bakayi, bare kayi wa kanka kyakkyawan shiri;
kana nan bakasan da wasu irin mutane kayi huld'a ba, makiya ta ko ta ina sukan iya rab'ar ka, kai har matan da kake aure ba abun yarda bane a wannan zamanin,
amma ka tattara yarda kaf ka d'aurawa Fatima, gashi har ta fara kaika ga halaka,
ai ko matan da suka haifa maka ya'ya Halima da Karima ba zaka tattara yarda duk ka daura a kansu ba,
bare Fatima da bata aje ko d'an hanji agidan nan ba,
shine zaka biye mata ku d'auko aljana har ka lamunce ta shayar da ita,
kaga daga nan sai duk tashige jikin mutanen gidan nan, ayi ta jinya har kud'i ya kare dama abin da takeso kenan,
shi mutum a rayuwarsa baya son ganin wani yaci gaba."

Kai Daddy ya girgiza ya ce
"Kiyi hakuri Hajiya ai shi kariya yana daga Allah, idan kayi ruko da addu'o'in da manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam,
ya koyar babu mutum ko aljanin da zaiyi galaba a kanka,
ko kin mance daga gidan manya Fad'imatu ta fito, wani dukiya ne zai tsole mata ido."
"Eh ai kai a kan Fatima da uban kowa ma zaka ja, tun da ka iya ja da ni,
su sauran da suka fito a tsatson talauci sun fita sau dubu, tun da suka iya haifo min jikoki, tana nan shekara goma da d'ori, ko b'atan wata bata tab'a yi ba."
Chapter 4 · 0% Book details