← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 52

Sashe 45

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr Imran ya koma office d'insa ya na zama yakira number Dr A.A Fiya.
sai da ya kira sau uku a na hud'u ya d'aga.
Dr Imran ya ce
"A.A ban kira ka naji ko ka isa lafiya ba, tun dawowa na daga kaika airport dana shiga asibiti har yanzu ban fito ba, ko wanka banyi ba,
ashe guduwa kayi ka barmin aiki,
kaifa kasan aikin ka sai kai, kafara ka barwa mutum yarasa ta inda zai kare,
to dai gashi munsha da kyar 'yar da kake sawa mutuwa gata ta farka da bakin ta rau, Allah ya amsa ka mata jinya ta warke."
tsaki yaja ya ce
"To meye na kirana kana fad'a min wannan, sai ka sanarwa 'yan'uwanta ba ni ba."
"To ai kai ne kayi jinyarta shiyasa nake sanar maka nasarar da ka samu, ga Daddy a nan a tare da su nayi mamakin ganinsa a nan."
d'ip yaji ya kashe wayar tun kan ya karasa abinda zai fad'a
Dr Imran ya ciro wayar yana binsa da kallo,
bai damuba dan shi ba bakon sanin halin sa bane...........!

Mommyn Twins ce

🌺 *FEERYAL* 🌺

*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*

( _Book 1_)

*~Free page~*

*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

🅿�20

Aunty ganin shiru-shiru Daddy bai dawo ba,
ta d'aga waya ta shiga kiran sa.
sai dai har kiran ta yanke bai d'aga ba,
hankali tashe takuma maida kiran a karo na uku, nan ma har ya yanke bai d'aga ba,
abinda Daddy bai tab'a yi ba ta kira sa a waya duk abin da yake zai bari ya d'aga kiran ta,
sai gashi yau ta kirasa har sau hud'u baya d'aga kiran ta.
ba karamin masifar tashin hankali ta shiga ba, lokacin da ta kira wayoyin su Hajja Umma Abba Maryam basu d'aga ba.
sai ga Aunty na hawaye tama rasa me ma zatayi sai kai kawo take sakanin parkour zuwa bedroom.

A b'angaren Daddy kuwa wayarsa ya mance cikin motar kamfanin sa na abuja da akaje d'auko sa a airport, sabar damuwar son sanin halin da FEERYAL take ciki.
su Abba kuwa wayoyin nasu duk a gida suka barosu.

Jin kirar yayi yawa ne direban ya d'auko wayar ya biyo sa da shi cikin asibitin.

Aunty na rike da waya tana zaga guri da ambaton sunan Allah yayin da wasu hawaye ke fita a idon ta batare da tasan suna zubowa ba.
Baba Rabi na ta tausasata tana cewa
"Insha'allah komai zaizo da sauki muyi ta addu'a."
da sauri ta d'ago wayar jin shigowar kira, bata tsaya duba mai kiran nata ba tayi saurin picking call d'in,
ta kai wayar kunnen ta.
jin muryar Daddy yana fad'in
"Hello Fad'imatu."
bata san san da ta fashe da kuka ba tana fad'in
"Daddy kana ina ka bani tsoro ina ta kiranka baka d'agawa, su Abba basa d'aukar waya, dan Allah Daddy kazo, ni zanje Abuja hankali na bazai kwanta ba in banje naga halin da suke ciki ba."

"Ki nutsu Fad'imatu ki saurare ni, ya isa haka kibar kukan nan, bani hankalin ki a nan Fad'imatu, uhm kina jina?."
hawayen ta ta share ta ce
"Eh."
"Yauwa ki kwantar da hankalinki yanzu haka ina abuja gani nan tare dasu Alhajin Abuja,
duk suna cikin koshin lafiya,
d'iyarki ma tasami lafiya tana bacci yanzu haka."
wani numfashi ta sauke ta ce
"Daddy shine ka tafi baka fad'a min ba, baka kuma tafi da ni ba,
to kasa ayi min bukin yanzun nan nima zanzo bari naje na shirya."
"A'a Fad'imatu ki saurare ni, basai kinzo ba kiyi zaman ki,
ba gani a gurin ba."
"Daddy ni dai ina so naga FEERYAL basu mata komai ba ko, me yasa to take asibiti?."
"Babu abin da suka mata razana tayi tashiga dogon suma, kuma ansami nasarar cirota daga dogon suman yanzun nan muna tare muna hira da ita,
bata jima da komawa bacci ba, kar ki damu zan taho miki da d'iyarki."
numfashi mai karfi Aunty ta sauke tanayiwa Allah godiya,
kana ta ce
"Ina su Hajja Umma?."
Daddy ya masa ya mika musu wayar.
jin muryoyin su yasa hankalin Aunty dad'a kwanci.

Bayan Abba sun gama waya da Aunty.
ya dubi Daddy ya na fad'in
"Dama ina fargabar cigaba da zaman FEERYAL a gurin mu a irin wannan lokacin,
munyi magana da kwamishinan 'yansanda yake ce min da da hali da an d'aga yarinyar a nan, sabo da
mai tawagar d'aukar amarya yana da mugun hatsari sosai,
dan yana da mutane da yawa kuma an shaidesa bai tab'a kaho hare ya tashi a banza ba,
zai iya yin komai duk da yana tsare amma akwai idanunsa a waje,
bare kuma ya kai hari an samu nasarar cafkesa zai iya ninka haushin sa,ya yi abinda ba'ayi sammani ba,
ta hanyar waiwayo wa kuma d'aukarta, tun da akwai sauran tawagar sa a waje,
yanzu haka suna ta kan bincike don su sami nasarar cafke sauran tawagar nasa."
Daddy ya jinjina kai sannan ya ce

"Ni ma nayi wannan tunanin, sannan kuma nasan hankalin Fad'imatu bazai tab'a kwanciya ba har in ba ta ganta ba, zan tafi da ita, har zuwa san da komai zai lafa."

Kwanan FEERYAL d'aya a asibiti in aka had'a da daren da aka kawota biyu ke nan.
da yamma Daddy ya bukaci a sallame su ganin jikin nata ya ware sosai, suka tattara sukayi gidan Abba.
'yan'uwa da abokan arziki da makota suka rika tururruwa zuwa gaida FEERYAL da musu jaje.
ancika tam a parlour sai jajanta lamarin ake 'yan cikin unguwar kuwa sai bada labarin yadda suka tsinci kansu lokacin da ake musayar wuta sakanin 'yan ta'addan da jami'an tsaro.
FEERYAL dai na zaune tana bin kowa da ido bata iya ce da kowa komai dama can ita ba mai yawan magana bace,
ga kuma faruwar lamarin da har yanzu yana jikinta tsoro da firgici mai had'e da fargaba, sai ta dad'a zamowa very silent.

Kiran Inspector Nasir ne ya shigo wayar Maryam ta mike tanufi bedroom d'in su.
ta zauna bakin gado tare da d'aga wayar tana jingina bayanta a jikin gado.
"Hello, Nasir ya aikin?."
"Lafiya lau, ya fargaba?."
"Hm har yanzu ban gama dawowa normal ba, fargaba yaki sake ni, har yanzu ina ganin abin a idona."
dariya ya yi yana cewa
"To FEERYAL kuma tace yaya ke nan, ita da ta shiga hanunsu taga yaki a kan idon ta."
"Ai FEERYAL tafini tsoro a mugun razane take har yanzu, kar kaga yadda take ciccire ido a parlour, da zataji karar wani abu yanzu dogon suma zata koma."
dariya duk sukayi.
Nasir ya ce
"Maryam ba kin ga girman irin son da Major Sadam yake yi wa FEERYAL ba,
ki duba kiga irin babban taimakon da ya yi mata,
yabada jikin sa da ransa wajen ceton rayuwarta daga annun 'yanta'addan can,
bai bari sun tafi da ita ba sai da ya tabbar da ya kwato ta a hannunsu,
Sadam yana son FEERYAL wlh bakiga halin da ya shigaba ranar, sai da ta farfad'o kafin hankalin sa ya kwanta,
haka ya wuni ya kwana bai d'and'ana komai a bakin sa ba, har sai da ta farfad'o kafin
ya samu ya sawa cikin sa wani abu."

Zama Maryam ta gyara sannan ta ce
"Nasir FEERYAL ita ta ta baku babban gudumawa wajen cafke 'yanta'addan da kuka jima kuke son kamasu kuka kasa,
bawai ita kuka taimaka ba ita ta taimake ku, ta baku damar cafke su,
Nasir bakasan waye FEERYAL ba,
FEERYAL tana da wani b'oyayyen baiwa da ba kowa ne ya sani ba, sai idan ka zauna da ita zaka san hakan,
ina da tabbacin FEERYAL ita ce silar taimakon ku wajen kama b'arayen nan, bance kun gaza ba ina mika jinjina ga jami'antsaron mu,
kuna kokari kam yadda ya kamata,
amma a wannan fannin kam tambas FEERYAL ita ce Star d'in wasan."

"Hm Maryan ke nan ke dai duk in da aka biyo sai kin toshe, to naji FEERYAL ta bada gudumawa wajen cafke tawagar d'aukar amarya, tun da ita akazo d'auka, har muka samu nasarar kamasu,
amma fa ki sani, Sadam sadaukar da rayuwar sa ya yi yafito gaba da gaba suka gwafza shi da kansa ya harbe Bala Kwari shugaban tawagar d'aukar amarya,
bayan ya harbe mutum uku cikin 'yan tawagar nasa."

"Duk wannan bajintar bayan da ta gama nata aikin ne, mance kawai duk yadda zan gaya maka bazaka fahimta ba,
amma lokacin da zaka fahimtar na zuwa,
san da mukayi aure FEERYAL tazo gidan mu."
"To shike nan Allah ya kaimu lokacin,
bayan ma kina ta jan lokacin please Maryam ki bari
na turo gida a sa mana rana, ban san me kike jira ba,
ko so kike sai kin had'a digiri na biyu ban sani ba."
dariya ta yi ta ce
"Ban ce ba dai ni kam, kai kam to meye matsalar ka bayan sadakinka yana hanu."
"Kin fi kowa sanin matsala ta, dan na bada sadaki iya haka bai wadatar ba, ke d'in nake bukata a kusa da ni,
bari komai ya lafa hakuri na ya kare yanzu kam."
shiru tayi tana saurarar sa.
"Kinyi shiru kina jina ba, kin manna min hauka ina."
"Na'isa yaushe Nasir d'ina ya sami tab'in hankali."
tayi maganar da muryar dariya.
"Saura kad'an ai bakisan rashin aure yana tab'a kwakwalwa ba."
ido ta waro ta ce
"Bana fata ya tab'a maka hankali,
last year insha'Allah zamu kasan ce ma'aurata, shike nan?."
"Yauwa yanzu naji batu, duk da dai har karshen shekara ya min nisa, za'a janyo lokacin."
nan suka cigaba da hira irin dai na masoya.
Chapter 45 · 0% Book details