← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 52

Sashe 34

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kiyi hakuri Fad'imatu ki bani kwarin gwuiwar yiwa mahaifiya ta biyayya, bazan iya jure ganin ki cikin damuwa ba, dalilin hakan zai iya kaini ga baud'ewa daga doron biyayya wa iyayen da nake kai,
kin san kuwa zan fad'a halaka, muyi hakuri mu sanya hakan cikin kaddarar mu."

A hankali ta kai hannu ta rike hannunsa dayake kan fuskarta ta d'aurashi kan cinyarta, tana d'an murzashi.
cikin sanyin murya da son gusar da damuwarta dan bata son ace a kanta ya sami matsala da mahaifiyarsa.
tasan batayi adalci wa kauna da soyayyar dayake nuna mata ba.
"Daddy kewa ce kawai ke damu na tun kan tayi nesa da ni, ka tayani da addu'a na rage jin ta cikin raina."
ta kwantar da kanta jikin kafad'ar sa.
ya shafo gefen fuskarta
"Ai baku rabu ba ko kin mance cikin ahalinki ta tafi yanzu,
tamkar kuna tare ne har yanzu."
kai ta jinjina tana dad'a kwanciya jikin sa.

Sai da ya tabbatar da ya yi nasara wajen rage mata damuwar da take ciki baifi saura taki ba, kafin ya bar sashin nata.

Abuja

Karfe 5 da mintuna 10 jirgin da su FEERYAL suka bi ya sauka a cikin airport d'in babban birnin tarayya Abuja.
wan da suka share mintuna hamsin da uku a sararin samaniya daga Lagos zuwa Abuja.
a nan airport suka tadda motar gidan Alhaji Tahir Abbas, yana jiran saukowar su.

Tun a cikin jirgi FEERYAL take ta baza ido, har a yanzu da suke tafe cikin mota a hanyar su ta zuwa gidan Alhaji Tahir Abbas da ke maitama,
dan bata tab'a tafiya mai nisa ba, daga gida sai school.
Aunty bata barin ta ko da Miemie ta bukaci suje wani gurin ko gidajen dangin su,
a kan FEERYAL Aunty ta jingine zuwa ko'ina sabo da gudun bakin mutane,
dan duk wanda ya ga FEERYAL d'in ya rinka wuu-wuu ke nan, wani ya fad'i alkhairi wani akasin sa.

A bakin wani katafaren gida mai girman gaske, direba ya yi hon aka wangale masa get.
babban gida ne mai matukar girma da tsaru,
duk da girma da tsaruwa irin na gidan Alhaji Abubakar Fiya,
sai da FEERYAL ta tsaya kallon tsaruwan gidan Alhaji Tahir Abbas.
sabo had'uwan shi shima.

Direba na gaba janye da akwatunan ta tana biye da shi.
suka shige cikin wani katafaren parlour na alfarma.

Tun kafin su karasa cikin parlour'n
Wasu dattijai biyu mace da na miji suka fito daga wata kofa.
ko ba'a fad'a ba kasan Alhaji Tahir Abbas ne Abba'n Aunty da hamaifiyarta Hajja Umma.
suna tozali da FEERYAL a tare suka furta
"Tabarakallah masha'allah."
ganin ainihin suffarta a zahiri yad'are wacce suke gani a hoto.
da gudu Maryar autarsu da ke biye da su,
ta wuce gaban su tana fad'in
"Wow beautiful oyoyo FEERYAL."
ta rungume ta.
Hajja Umma tana kokarin tareta, Abba ya yi saurin shangabanta ya ce
"Barni ni zan tari amarya ta da kai na."
Hajja Umma ta yi murmushi tana cewa
"Saboda ni kishiya ko, ai dai gara ni na fara tsare ta na kakkab'e abinda tazo dashi,
koma da baya na d'ebo sakin kuka na zuba a hanyar shigowar ki,
ya karya abinda kikayiwa Alhaji tsawon shekaru nice amarya nice uwar gida,
daga zuwan ki zaki firgita shi."

"Taho nan amaryata gimbiya FEERYAL rabu da ita."
ya ruko hannunta.
suka karasa suka zauna kan kujera.
Maryam ta kasa zama tana ta kallon ta, kyawun ta ya mugun tafiya da imanin ta.
sai fad'i take
"Wayyo Allah kyakkyawa ce wlh kamar ita tayi kanta, kullum tare zamu rika zama ko kamshin kyan ki zai shafani."
dariya maganar ya bata ta yi karamar dariya, kyakkyawan kumatun ta ya lob'a.
Hajja Umma ta ce
"Tabarakallah masha'allah."

Direba ya aje akwatunan ta ya fita bayan ya gaishe su.
Abba ya ce
"Maryam d'auki akwatin ki kaisu d'akin kusa da naki d'akin ta ke nan, amarya ta ko kina son d'akin sama kusa da na Hajja Umma ne?."
da sauri Maryam ta ce
"Abba a d'aki na zata zauna murika kwana tare."
"A'a ki bari dai a bata d'aki na, ni na sauko kasa,
ai in bakuyi wasa ba sai dai ka ajeta a kitchen ko store."
cewar Hajja Umma tana dariya.
Abba ya ce
"Ai wannan gold d'in tafi karfin zama a gurin da kika ambata, Maryam kaita taci abinci tayi wanka ta huta, sai tazo muyi hira."

Maryam ta janyo akwatunan ta ce
"Taho muje."
babban d'aki ne mai girman gaske komai na bukata yana ciki kamar d'akin matar aure, bana 'yar matashiya mai tasowa ba.

Maryam ta dubi ta tana fad'in
"Shiga bayi kiyi wanka ko nazo nayi miki?."
kafad'a FEERYAL ta make ta ce
"Na iya fa Ammie na ma tana barina nayi ranar da ba school."
"To je kiyi kizo ki sauya kaya muje kici abinci."
ta shige bayi. ita kuma Maryam ta shiga ciro kayan ta tana sakasu cikin wardrobe.

Ko da ta gama ta fito Maryam ta taimaka mata ta shirya tana ta yaba kyawun halittarta, FEERYAL ta zame mata abin kallo.
Maryam ta janyo ta tana fad'in
"Zo muje kici abinci ki rakani gidan wata kawata."
cikin zakuwa ta janyo ta suka fito.

A parlour suka sata gaba sai taci abinci tad'an ci dai ba laifi dan ita ba ma'abociyar cin abinci da yawa bane,
yogurt da cake sune abin cin ta.

Sosai suka rika janta ajiki a wunin ranar harta saki jiki da su.
taga soyayya da kauna da kulawa kamar zasu goya ta.
Alhaji Tahir Abbas yana gida bai fita ba saboda zuwan FEERYAL, ya kira Aunty video call suka sha hira tamkar suna tare.
bayan sun gama waya da Aunty Maryam ta mike tace tazo suje ta rakata.
Hajja Umma ta ce
ta bari sai gobe yanzu yamma ta yi.

Da daddare ma a parlour'n sama suka yada zangon su, sai da suka kai karfe 12 suna hira kafin Abba ya ce suje su kwanta.

Washegari Maryam ta ja FEERYAL sukayi gidan kawarta a nan unguwar su.
suna shiga gidan da
Haulat kawar Maryam d'in suka fara cin karo.
Haulat ta kasa amsa sallamr da Maryam takeyi.
ta kurawa FEERYAL ido.
"Ke dalla ina sallama kinyi shiru bazaki amsaba."
"Wow wannan fa a'ina kika samota, ko ba'in turawa kukayi?."
Haulat ta fad'a tana nuna FEERYAL tana ware idanunta sosai a kanta.
"Ni dad'i na dake hauka ke kam baza'a yi miki surprised ba ana miki zaki iya mutuwa, d'iyar Aunty Faty'n Lagos ce."
"Ke da'alla serious Maryam kar ki shigar da ni, wannan dai ba bahaushiya bace, da gani ruwa biyu ce baturiya balarabiya."
"Da gaske d'iyar Aunty Faty ce jiya ta zo, kin wani barmu a tsaye komu koma ne kin wani tsare ni da tambayoyi."

"Yi hakuri taho mushiga ciki wlh ganin ta ne yasa ni shiga yana yin nan, zo na rike hannunki ya sunan ta?."
Haulat tayi maganar tana ruko hannun FEERYAL.
"Ya salam ashe ana ganin irin su a zahiri ba a TV ba."
dariya Maryam tayi ta ce
"Wlh ke da a kauye kike bansan ya zaki kare ba."
"Ke dai Maryam barni nafad'i gaskiya ta, wlh yarinyar nan so beautiful, ta tafi da ni gaba d'aya."

Haulat na rike da hannunta suka shige parlour'n su.
Maryam ta zauna tana dariyar Haulat da gaba d'aya ta rud'e da ganin kyan FEERYAL.
a gefen ta ta zaunar da ita tana rike da hannunta bata sake ba, ta dubi Maryam tana faÉ—in
"Wai dan Allah kuma da gaske d'iyar Aunty Faty'n Lagos ce, ko dai abokin kasuwan cin Abba ne yazo da 'yarsa daga wani kasan,
yanzu wannan 'yar Alhaji Abubakar Fiya ne?."
fuska Maryam ta had'a ta ce
"Abin da na saba miki, kin ga tabon sa a goshi na ai, karya ba."
"Allah baki hakuri kawata, lallai kuwa babu ko shakka kwanciyar hankali ma yana karawa mutum kyau, d'iyar Alhaji Abubakar Fiya jika ga Tahir Abbas ai abin bana wasa bane, sai dai ita wannan kyan nata na daban ne tamkar ta had'a jini da larabawa ko turawa,
watakila Alhaji Abubakar Fiya ya had'a jini da su, duk da cewa Aunty Faty ma badaga nan ba a kyau."
Maryam ta sakar mata hararar wasa ta ce
"Yauwa yanzu kika gyara kalamanki ai muma dai kinsan muna da kyau, har da namu kyan ta d'auko makoyi ne dai yafi gwani."
"Lallai kuwa yarinya kin fito a dai-dai d'iyar Alhaji Abubakar Fiya jikan Tahir Abbas."
"Sai kin kiramin sunan uba, kiji dad'i ina Haulat banson cin fuska."
"Suna da inkiya ba cin fuska bane."
dariya duk sukayi.
Maryam ta ce
"Wai ya naji gidan shiru ne, Momma fa?."
"Unguwa suka tafi dukan su,
sun je gidan tsohuwar ta, yanzu haka sai yamma su dawo,
ni ma dama zan gama ne na bisu can d'in,
tun da kunzo muyi hira kawai."
nan suka cigaba da hira wanda rabi da kwatan hirar duk akan FEERYAL ce.
Haulat taki barin su su tafi tana ta jansu da hira.
ita dai FEERYAL da ido kawai take binsu, hakan nadaga cikin dabi'ar ta rashin magana da yawa, bata daga cikin yara irin masu yawan surutun nan.

Har kusan azahar suna gidan sai da Hajja Umma ta kira Maryam a waya ta ce ta dawo mata da jikarta yanzun nan, kafin suka tafi.

Washegari kuwa gyaran gashi Maryam ta d'auke ta suka tafi.
suna shiga shagon kallo ya dawo kansu.
daga nan suka wuce gidan Aunty Zainab yayar Aunty da take binta.
FEERYAL taga kauna a gidan ita da 'ya'yanta kamar zasu goyata, har Aunty Zainab tace a bar mata ita tayi mata kwana biyu.
Hajja Umma ta ce
maza-maza a dawo mata da ita.
Chapter 34 · 0% Book details