← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 52

Sashe 25

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna Delu matar malam Buba Mani, dake aiki a sakar gida ta amsa musu sallamar tana fad'in
"Lale barkanku da zuwa."
tayi saurin mikewa ta isa ta d'auko tabarmar kaba ta shinfid'a musu tana cigaba da fad'in
"Ku iso ga gurin zama maraban ku dai."

Wani irin mikewa malam Buba Mani dake zaune cikin wata 'yar rumfar kara ya yi.
"Ta bayyana ke nan!."
ya yi maganar a zabure.

kafin su Aunty su karasa gurin zaman da aka musu shi ya rigasu fito wa, daga cikin rumfar karar da yake ciki.
da sauri tamkar mai tafiya kan iska tsohon dattijon ya iso gaban su kamar kiftawar ido.

Beyi wata-wata ba ya kai askar dake rike a hannunsa kan goshin Feeryal, ji kake kyasss ya tsaga shi dai-dai tsawon gab'ar yatsa d'aya.
nan da nan wani bakin jini yashiga tsartuwa.

Jikin Aunty ya d'auki b'ari ba ita kad'ai ba har da Baba Rabi da ita kanta mai d'akinsa Inna Delu.
abin mamaki Feeryal na tsaye babu wani alamar da ya danuna jin zafin yankan da aka mata bare d'igon hawaye a idon ta.

Malam Buba Mani.
ya kamo hannun Feeryal ya janyo ta cikin 'yar rumfar karar nan, da sauri ya zaunar da ita kan wata kututturen itaciya.
ya mike da sauri ya shiga wani d'aki dake cikin rumfar,
da sallama mai karfi d'auke a bakin sa.
da gani dad'ad'd'en d'aki ne,
yana duk ya baiyaye ko ina.
ya saka hannu ya yaye yanar da ke gabansa kana ya mika hannu ya d'au wani d'an karamin tukunyar kasa,
ya yaye yanar da ya rufe jikin tukunyar kana ya juya yafito da sauri.

A gaban ta ya aje tukunya yasaka hannu da sauri cikin sa, ya d'auko wani magani ya mannashi a goshin ta dai-dai gurin da ya tsaga.
da sauri ya danne gurin da yatsarsa ta tsakiya.
yashiga goga maganin a gurin yana zagaye da shi kamar zagayen mantega.
sai da ya d'anyi fad'i da shi kana ya d'aga hannunsa ya d'au wani, maganin yakuma shafe gurin da shi.
nan take gurin ya shafe tamkar ba gurin bane a ka yankata kafin yanzu, ya dawo normal kamar inda ainihin fatarta yake.

Aunty suna tsaye suna kallon ikon Allah.

Numfashi Malam Buba Mani ya sauke, ya mike tsaye yana dafe jikin karar rumfar sa, yana kuma sauke numfashi, kamar wanda ya yi aikin gayya.
kan kace me suka fara jin kukan tsuntsaye da wasu nau'ikan dabbobi.
kamar kiftawar ido tsuntsaye suka cika gidan ta sama suna ta shawagi da kuka iri daban-daban.

Dajin Malie.

A can cikin kasurgumin dajin boka Malie a karkashin kogon tsafin sa.
A firgice boka Malie ya mike yana zazzare jajayen manyan idanuwansa, masu matukar tsoratarwa had'i da firgidar ga duk wanda ya yi arba da shi.
ya damke tsandar tsafin sa, cikin hargitsatsen murya mai fidda amon sauti maraddad'i mai cike da razanarwa ya furta
"Ma somar faruwar wata husuma!."

Ya buga sandar tsafin sa a kasa, yana gwalalo manyan munanan idanunsa, yana son ganin me ke faruwa.
sai dai daya buga kasa madadin ya sami amsar tambayar sa,
sai dai yaga bakin hayaki mai duhu ya kasa ganin komai.

Nan da nan ya tura aike izuwa fadar sarkin bokaye.

Sarkin bokaye Lazzi shima a gurinsa yaji alamun faruwar wata husuma, sai dai duk iya binciken sa ya kasa gane mene ne, ya wanzu yanzu-yanzu.

Dole shima sai da ya dangana ga sarkin bakaken aljanu.

Sako ne ya dawo wa sarkin bokaye Lazzi daga gurin sarkin bak'aken Aljanu,
wacce suke nima ce ta bayyana sai dai babu haske a gareta basa iya ganin komai sai duhu.

Nan da nan sarkin bokaye Lazzi ya sanarwa boka Malie abin da ke faruwa.
tsabar firgita sai da ya fad'i ya suma.

Duguri

Malam Buba Mani yafito daga rumfar karar sa, in da Feeryal ke zaune ko a jikin ta tasa yatsar ta cikin baki tana wasa da shi.
har lokacin su Aunty suna tsastsaye da kafafun su, sai dai yanzu duk kawunan su a sama yake suna kallon tsuntsayen da suke ta shawagi saman gidan. kasa-kasa kamar zasu sauko kansu.
ya yin da tsoron su ya karu ganin wasu irin halittun tsuntsaye daban-daban, wasu masu yanayin ban tsoro.
lokaci kankani suka cike saman gidan sai kuka iri daban-daban suke.
sunayi kamar zasu sauko kasa.

Malam Buba Mani ya d'aga hannu sama yana fad'in
"Maza kuyi tafiyar ku babu abin da ke faruwa anan, tana cikin koshin lafiya."
ai ko nan take tsuntsayen nan suka soma watsewa, har suka watse duka.
sai guda biyu suka rage akan rufin d'aki.

Baki Feeryal ta washe daga in da take zaune tana hango tsuntsaye guda biyun nan, wan da a zahiri ita ba tsuntsu take gani ba mutane ne.
da saure ta mike tafito daga cikin rumfar tana nuna su da yatsa
"Laa Chuchu Chulu yaushe kuka zo kuma a jirgi kuka zo, ya ban ganku ba,
shine kuka hau sama kuma?
ai naga mutane da yawa a sama, nima ku hau da ni."
ta d'aga hannu sama tana tsalle, wai itama zata haura sama.

Aunty ta zubawa tsuntsaye biyun nan ido da Feeryal ta kira su da sunan da take kiran kawayen ta da su, abin ya matukar d'aure mata kai.

Maganar Malam Buba Mani yasa Aunty dawowa daga tunanin da ta tafi jin yana cewa

"Ku gusa a gareta kar ku shagaltar da ita."
yana rufa baki suka fire.

Fuska ta bata tana cuno baki
"Ba kun tafi ba, ko kunzo gidan mu bazan baku baby na kuyi wasa da ita ba, ai Ammie na ta siya min babban baby kuma."

Malam Buba Mani ya dubi Aunty da ke tsaye tsoro ya bayyana gare ta.
ya ce
"Bismillah Hajiya ku isa ku zauna."
da kyar ta iya jan kafarta, Baba Rabi ma da tsoro ya gama da ita ta biyo bayan ta suka karasa kan tabarmar da aka shinfid'a musu suka zauna.

D'aya daga cikin mutanen da suke tare da su Daddy a waje, ya kwad'a sallama cikin zauren gidan.
Malam Buba Mani ya amsa tare da nufar zaure ya fita.

Aunty na zama Feeryal ta dawo jikinta ta zauna, tana ta zuba mata shagwab'ar ta data saba.
Aunty dai bata iya ko kyakkyawar motsi ba dan tsoro yagama cinye kanta,
sai satar kallon goshin ta take inda d'azu ke fidda jini yanzu kuma yadawo tamkar inda da yake.

Jim kad'an Mamal Buba Mani ya dawo gidan, ya karasa 'yar rumfarsa ya zauna.
da hannu ya kira Aunty ya ce
"Kuzo ku da d'iyar ta ki."
jiki a sanyaye Aunty ta mike rike da Feeryal suka karasa cikin rumfar ya nuna musu gurin zama suka zauna.

Dattijon ya dube Aunty da kyau kana ya soma magana cikin nutsuwa,
"Duk wani wanda Allah ya hukunta zamanta a gurin sa dole yaji fargaba da tsoron abubuwan da zai rika gani da ji a gare ta,
shin ke ce mahaifiyarta?."

Aunty ta girgiza ta ce "A'a."
"To wace ce ke a gareta?."
Aunty ta gyara zama tare da duban Feeryal sannan ta ce
"Tsintar ta mukayi, ni da megida na acikin ruwa, ruwa yana shirin gudu da ita,
shine muka riketa har izuwa wannan lokacin."
kai ya jinjina kana ya ce
"Angaishe ku da kokari, sannunku da ceton farar aniya."
ya shafa kan Feeryal da ke ta wasa da igiyar tabarma,
ya ce
"Karni bayan karni shekaru masu tsawo fidda rai ga samin 'yanci bayyanar ki ya dawo da komai sabo,
an jinjina miki 'yar baiwa,
shekaru arba'in rabon da na shiga wancan d'akin amma yau ganin ki ya bani tabbacin zan iya shigarsa batare da wata tsaiko ba,
zan kuma cigaba da taimakawa mutane da baiwar da Allah ya yi min,
wan da nakasa kuma taimakawa wani tun bayan shekaru arba'in."

ya gyara zaman sa kana yaci gaba da fad'in.
"Nasan abinda ya kawo ku nan bai wuce kokon to a kan ta ba,
ita mutum ce kamar ki kamar ni kamar kowani mutum, sai dai ita ta bambanta, tana da wasu irin tarin baiwa da ba kowa yake da irin sa ba,
ita kanta a wannan shekarun nata sam bazata fahimci komai cikin rayuwar ta ba,
har izuwa wasu shekaru masu dama,
kada ku damu da yana yin ta ko wani d'abi'arta,
idanunta da kanta a bud'e suke tana iya ganin abin da ku bazaku iya ganinsa ba,
baiwa ce daga Allah, kada hakan yabaki tsoro,
zata iya yin mu'amala da su kamar yadda zatayi da ku, kada ganin hakan yatada muku hankali babu komai da yardar Allah,
naji dad'i da Allah ya nufeku da tunanin zuwa nan, bakuyi tunanin zuwa gurin wani ba,
bamu sani ba wanin ko shi wane ne, wala'alla ko shi na d'aya daga ciki 'yan kwangilan da aka baza domin niman ta,
a wannan lokacin da sukasan da bayyanar ta, suke fafutukar niman inda take,
shi yasa nayi gaggawar goge shaidar da zai sa suyi saurin gane ta, a duk inda zasu had'u bazasu tab'a gane abin farautarsu ba,
haka zasuyi ta nima su rasa, na goge tabon da ke goshinta da zai bayyana ta a gurin su cikin ruwan sanyi."

Kai Aunty ta jinjina cikin ranta cike yake fal da tambayoyi.
kamar yadda nasan kuma kan ku masu karatu kuke d'auke da shi cikin zuciyar ku.
"Wace ce ita meye had'inta da aljanu bayan ita mutum ce ba aljanar ba,
me yasa wasu ke niman ta, to ko shi yasa aka jefata cikin ruwa ya tabbata ba had'arin jirgin ruwa sukayi da iyayen ta ba?."
ya akayi ya santa bayan bai tab'a ganin ta ba."
ire-iren waÉ—annan tambayoyin ke yawo cikin zuciyar Aunty.

Malam Buba Mani ya yi murmushi ya na fad'in
"Nasan akwai tarin tambayayo cikin ranki amma lokacin sanin hakan yana zuwa, naji dad'in jin a hannunku ta ke, nasan zata sami tsaro da kulawar daya da ce,
kutashi ku koma gida d'iyarku mutum ce mai daraja ma kuwa."
Chapter 25 · 0% Book details