← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 52

Sashe 22

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty na tsaye tana kallon ikon Allah.
"To taso muje."
ta fad'a ganin ta sauke hannun nata, ta ruko ta sukayi waje.

Washegari da safe Aunty na kichin tabar Feeryal tana bacci.
tana gama abinda take ta dawo d'aki taga bata nan.
bathroom ta shige tana kiran sunan ta,
tsayuwa tayi ganin bata ciki, sai ta juya tanufi kofa tana cigaba da kiran ta.
bata parlour bata kuma cikin bedroom d'inta in da take wasa ciki.

Daddy dake zaune cikin parlourn ya dube ta yana fad'in
"Ko tana toilet ne kin duba can."
"Babu in da ban duba ba Daddy."
batare daya d'ago daga kallon labaren safe da ake a TV ba ya ce
"Zata fito ai tashige wani gurin ne."

Bata kuma magana ba dan ita kam lungu da sako duk ta duba bata nan.
da d'an mamaki ta tsaya cikin parlour da tunanin to ina taje.
"To ina taje? kar dai ace taje gurin Miemie ce."
tayi maganar tana nufar kofar fita daga parlour'n, da sauri.

Tana fita farfajiyar waje, cikin hanzari ta nufi bakin get d'in side d'in ta.
har tarike karamar kofa zata bud'e, taji yo dariyar ta ta can baya ta cikin garden.
da sauri ta waigo tare da soma nufar gurin da take jin sautin dariyar nata.
da mamaki take kallon ta kan lilo ita kad'ai, lilon na lilata sai b'arkewa da dariya ta ke tana kuma fad'in
"Ku kara yi min sau biyar ni ma zan muku."

Hannu Aunty ta d'aura a kirjinta tana son dai-dai nutsuwarta, cikin karfin hali daga in da take takira sunan ta.
"Feeryal."
da sauri ta kalli gurin da Aunty take sai kuma ta ce
"Kutsai da ni ga Ammie na zanje gurin ta, zan dawo na rama muku."
ta diro a kan lilon da gudu ta taho in da Aunty take, ta ruko hannunta tana d'an bubbuga kafa cike da shagwab'a take fad'in.
"Ammie yunwa nake ji."

Aunty ta had'iye tsoro mai had'e da fargaban da yake taso mata ta dube ta a hankali ta ce
"Shine kika tsaya anan kina kuma jin yunwa iye Feeryal? to muje kiyi wanka sai kici."
sun kusa isa bakin kofar parlour Feeryal ta juyo tana fad'in
"Kuma zakuje Ammie na tayi muku wankan kuci abinci ne?."
da sauri Aunty ta waigo, bataga kowa ba sai ji da ta kuma tana fad'in
"Ammie suma zakiyi musu wankan ko?."

Bata iya yin magana ba har suka shige cikin parlour.

Daddy na ganin su ya ce
"A'ina kika samo ta, Feeryal ina kkje da safiyar nan?."
Zamewa tayi a hannun Aunty ta koma jikin sa tana fad'in
"Daddy wasa muke yi da kawaye na."
"Wasa kuma Feeryal da safen nan, baki ji ana sanyi ba,
ko kayan sanyi fa babu a jikin ki, sanyi zai kamaki je maza Ammie'n ki ta sa miki rigar sanyi."
ta ce to. ta mike ta dawo gurin Aunty da ke tsaye.
Aunty ta kad'a keyarta ta ce
"Je maza ki jira ni a bathroom ina zuwa, kice da kawayen naki kar su biyo ki."
kai ta gyad'a da gudu tayi cikin bedroom.

Fuska Aunty ta kwab'e tana kallon gefen da Daddy ya ke.
murmushi mai sauti ya yi, kana ya miko mata hannu ya na fad'in
"Taho muji ya akayi ne, kefa wani lokacin rikicin ki yafi na d'iyarki Feeryal."

Hannu tamika masa ya janyo ta tazauna gefen sa.
sosai ya maida hankalin sa gare ta,
"Mene ne ko angaji da zaman gida ne, nayi mana bukin zuwa London."
kai ta girgisa sannan ta ce
"Yanzu ina fad'a sai kace gizo ne, kai bakaji Feeryal ta ce maka taje wasa ne da kawayenta ba, sai tayi ta magana ita kad'ai fa tun jiya,
kamar da wasu take magana, kuma har nuni tayi min ta ce ga wad'an da take maganar da su,
nikuma banga kowa ba."
murmushi ya yi, ya ce
"Gimbiyata ban isa in fad'i ba yanzu kam, dan naji da kunnena ta fad'a,
magana kuma a gun yaro shi kad'ai, ba yana nufin da wani agun bane,
yaro shi komai nashi na wasa ne."
baki ta tsuke bata kuma cewa komai ba, dan tasan duk yadda tayi da shi bazai tab'a fahimta ba.
ta zame jiki tayi d'aki.

Tana shiga bathroom ta isketa tana ta wasa da tsalle cikin ruwa tana fad'in
"Ku zubo mana ruwan gidan ku muyi wankan yafi dad'i."
"Anya Feeryal bata sami matsalar kwakwalwa ba kuwa?."
tayi maganar a kasan ranta.
"Idan har ba matsala ta samu a kwakwalwa ba to kuwa akwai wani abin akasa."

Haka ta daure tayi mata wanka, tana mata tana fad'in
"Ammie kiyi wa kawaye na suma."

Bayan ta gama mata wankan tafice da gudu, tana fad'in
"Ayi rige-rige."
Aunty ta tsaya ta gyara in da suka b'ata, koda ta fito d'akin.
can saman wardrobe ta hango ta d'ororo a tsaye da kafafunta, tana ta kyakyata dariya.
tsoro ne ya ziyarci Aunty, ko ita tsawonta baya kai saman wardrobe d'in nan.
ko abu zata d'auko a saman sa sai ta samo abin hawa takara tsawo kafin hannunta ya iya kai wa saman sa,
sai ga Feeryal d'ororo a saman wardrobe.

Hannu ta mika tana fad'in
"Ammie ki saukar da ni sun gudu sun barni."
da sauri Aunty ta yi waje, jikinta na b'ari.
ganin yadda ta fito yasa Daddy fad'in
"Lafiya Fad'imatu?."

Kofa tashiga nunawa tana fad'in
"Feeryal a saman wardrobe."
Daddy ya mike yana cewa
"Me kuma ya kaita saman sa, kin d'aura ta ne kika kasa sauke ta?."
kai ta girgiza da sauri ta ce
"Bani na d'aurata ba a kai na ganta."
da d'an sauri Daddy ya nufi bedroom yana fa d'in
"Shine zaki fito ki barta idan kuma ta fad'o taji ciwo fa?."

Yana shiga ya ganta tsaye a cikin d'aki.
Aunty da ke biye da shi ta
tsaya cike da mashahuriyar mamakin ganin ta a tsaye cikin d'akin.
Daddy ya dubi Aunty yana cewa
"Bansan me yasa kike kin amfani da magani da hayakin can ba,
bari nayi waya a karb'o miki wani."
"Daddy ka maida ni mai tab'in hankali ce ko?."
tun kafin yakuma cewa wani abu, ta b'ata fuska ta koma parlour tayi zamanta.

Yakama hannun Feeryal da kansa ya saka mata kaya ya shiryata tsaf yaruko hannunta suka fito.
Aunty na ganin sa takuma had'e fuska.
murmushi ya yi ganin yadda ta cika tam.
ya kad'a keyar Feeryal ya ce
"Je kichin maza Baba Rabi ta had'a miki breakfast."
tace tom.
da gudu tayi hanyar kichin.

Ya karaso ya zauna gefen Aunty yaruko hannunta tare da kiran sunan ta
"Fad'imatu."
da sauri ta tari numfashin sa.
"Daddy gizo ne yanzun d'in ma kada ka ce komai, amma ni bana da wata matsala a kwakwalwa ta, wlh ina son Feeryal ban tab'a jinta a wata daban ba, ina jinta ne tamkar jinin jikina, wacce ta fito daga tsatsona;
abubuwan danake gani tare da ita ne kawai yake sani shiga fargaba a kanta,
ina tsoron kada wataran na rasata, bayan nayi sabo da ita."

Hannuta ya dad'a rike wa cikin nasa ya ce
"Insha'allah bazaki rasata ba, sai kin kaita har d'akin aurenta, kin ga jikokin ki."
ido ta d'an lumshe ta bud'e tana jinjina kai.

Kullum abin Feeryal karuwa yake salon yau daban na gobe da ban ita da Kawayen nata da babu mai ganin su sai ita.
zuwa yanzu Aunty tafara tunanin kodai mayu ne ke bibiyar ta, tana tsoron kada su bata maita ko su cinye ta.
kullum a cikin addu'a take ba dare ba rana, Allah ya kare mata ita daga sharrin miyagon da ido baya iya ganinsu.

Kimanin wata biyu ke nan ana cikin wannan halin kuma kullum abin gaba ya ke ba baya ba..

Aunty ce zaune cikin bedroom tajiyo hayaniya cikin parlour.
jin muryar Mommy tana fad'in
"Wlh sai kin bar gidan nan tun da bana ubanki bane, baki isa kice zaki takurawa 'yan gida ke kina agola ba, wacce ta tsaya mikin ma bata isa ba bare kuma ke."

Da sauri Aunty ta fito parlour'n.
Mommy Ameerah Feeryal Miemie Sahla Nabila. tagani cikin parlour'n.
Mommy na damke da hannun Feeryal, kamar wacce ta kamata tayi mata sata.
Ameerah tsaye baki na fidda jini gefen goshin ta ma haka.
Mommy na ganinta takuma d'aga murya tana cigaba da fad'in
"Wannan annobar 'yar da kika kawo mana gida take kokarin kashe mana 'ya'ya wlh in akan buzu kike kwana karshen tsafi, sai nayi duk yadda zanyi naga tabar gidan nan,
kina sane da cewa dai nafiki fawa a gidan nan, da uban Alhaji Abubakar da ubana uwarsu d'aya ubansu d'aya, kinsan dai na d'are miki nesa ba kusa ba,
d'an'uwa na jini kuma mijina nice nan kuma uwar manyan 'ya'yansa,
kinsan ina da hanyoyin da zanbi cikin sauki na fidda wannan aljanar mayyar a cikin gidan nan, ba ita ba hatta ke wlh ina da yadda zan bi kibar gidan nan tacikin ruwan sanyi, kibi a sannu na gaya miki ke nan;
ina dalili ina mafari da zata sako mana 'ya'ya gaba,
jiya ta fasawa Nabila baki an kyaleta shine yau bari ta komo ta kan autata, to wlh bata isa ta ci bulus ba, baki isa ki takurwa 'yan gida kina tsintacciyar agola zubin mayun aljanu ba,
a gaban uwar tsintuwar taki zan ci uban ki."

Ta tsulawa Feeryal bulalar da ke rike a hannunta, har sau uku.
Feeryal tasaki kara tana tsalle da yarfe hannu.
Chapter 22 · 0% Book details