← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 52

Sashe 42

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Babu nisa sakanin gidan nasa da asibiti, titi ne ta rabasu, gidan na kallon asibitin.
suka sallaka suka isa bakin get d'in gidan.
Nasir ya kwankwasa, mai gadi da ke gyangyad'i kan kujera ya zabura da sauri ya mike, ya leko ta mahangarsa dake jikin get d'in.
ya hango police da ma'aikacin asibitin mai gidan sa.
ya bud'e karamar kofa yana rarraba ido da son jin ba'asin abin da ya kawo su tsohon daren nan.
Inspector Nasir ya ce
"Sannun ka da aiki, mun zo gurin mai gidan ne."
ido mai gadi ya gwalalo ya ce
"Yallab'oi Allah dai yasa lafiya, wlh shi kam ma yau ya shigo kasarnan yana can kasan turawa,
yana rayuwar shi babu ruwan shi da kowa."
"Bamu hanya dai yanzu mu wuce."
da sauri mai gadi ya matsa gefe.
suka shigo ciki Nasir ya dubi mai gadin yana fad'in
"Kayi mana sallama da shi yanzu dan Allah."
mai gadi ya isa da sauri jikin garun d'akin sa, in da wayar tafi da gidan ka take sakale a gurin.
ya daddanna ya kara a kunnen sa.

Aci kuwa nan take wayar ta soma kara ta karad'e cikin parlour.
yana kwance idanunsa a lumshe da sauri ya kai hannu ya toshe kunnuwan sa,
"Ya salam."
ya furta yana mikewa zaune.
kai ya dafe da hannunsa biyu, jin yadda kiran yake kuma shigowa babu kakkautawa.
ya mike a fusace ya fito parlour.
ya fincike wayar ya kai sa kunne cikin tsawa ya ce
"Kai wani irin hauka ne wannan zaka cika min kunne da kira!."
mai gadi ya durkusa kaman yana gaban sa ya ce
"Allah baka hakuri oga hankali na ne a tashe ganin police a tsohon daren nan wai yazo niman ka."
tsaki yaja ya saki wayar Allah ya kare bata isa kasa ba da sai dai wata ba dai ita ba,tana ririto ajikin igiyar ta.

Kugu ya rike tare da furzar da huci mai zafi daga bakin sa.
ya yi da na sanin zuwa kasar shi da ya gudo domin ya huta ashe wata musifar aikin zai kuma gamuwa da shi a nan.
a hankali ya ke takawa yana mammatse idanunsa da bacci yake cike tam a cikin su,
Allah ya sani ba karamin bacci yake ji ba.
ya isa in da takalman takawan cikin parlour'n suke ya zura d'aya a kafarsa ya fito da gajeren wandon jikin sa da singileti.
yana aikin jan tsaki fuskarsa a had'e kamar tun da yake bai tab'a dariya ba.
tun kan ya karaso in da suke Nasir yashiga takowa gare sa shima suka had'e a tsakiya.

I'd d'in sa ya ciro a aljuhu ya nuna masa yana fad'in
"Inspector Nasir B Suleja, barka da dare Dr Abdurrahim A.A FIYA."
Nasir ya mika masa hannu, da kyar ya miko masa nasa hannun suka gaisa.
Nasir ya gyara tsayuwar sa ya ce
"Nasan baka sanni ba, nima dai bana ce nasan ka a ido ba, amma ina jin sunan ka,
akwai kuma kyakkyawar alaka sakanin Alhajin ka da hukumar mu."
fuska ya dad'a had'ewa dan ya kosa da jin bayanan sa, katse Nasir ya yi da fad'in
"I'm okay me ya kawo nan?."
Nasir ya yi murmushi ya ce
"Dole zan sanar maka abin da ya kawo mu ai bayan gabatarwa,
kayi hakuri mun katse maka baccin ka,
dole ne yasa hakan, muma bamu samu mun rumtse ba cikin daren nan,
aikin mu da naka yana kamancece niya so dole bacci zai zamo mana short saboda taimakon al'ummar mu,
muna tafe da patient tana asibitin ka, amatsayin mu na jami'an tsaro mun sami nasarar kwato ta daga hannun 'yan tadaddan da suka saceta suke kokarin guduwa da ita,
mu munyi aikin mu saura naka,
kai kuma a matsayin ka na likita yanzu sauran aikin naka ne, tana bukatar taimako dan Allah kaje ka duba ta."

Fuska ya dad'a had'e wa, ina gashi nan kalar aikin da yakin aka matsa masa sai ya yi, shi kullum bashida lokacin kansa sai na mutane.
d'an baccin ma baza'a barshi ya yi ba.
juyawa ya yi yana kokarin barin gurin tare da fad'in
"Ku barta a gurin gobe Doctor's zasu shigo su duba ta."
da sauri Nasir ya sha gaban sa ya ce
"Haba kai kuwa yarinyar da take cikin halin mutuwa ko rayuwa, idan ka taimake ta kaima Allah zai dad'a taimakon ka, bata cikin hayyacin ta gaba d'aya please ka taimaketa dan Allah, daure dai muje ka duba ta,
ai duk irin aikin namu ke nan muna son baccin nan muke hakura da shi."

Gajeren tsaki yaja, kana ya zura hannayen sa cikin aljuhun gajeren wandon jikin sa, ya juya suka nufi kofa.
Nasir yana ta bashi baki har suka fice a gidan suka ketare titi suka shiga asibitin.

Ma'aikatan da suke kwana asibitin suna ganin sa kowa ya mike tsaye da kafafunsa, suna mika masa gaisuwa, ba wanda ya amsa gaisuwar sa ya wuce ICU Nasir na biye dashi.

Har lokacin Major Sadam yana tsaye da kafafunsa yana ta kai kawo cikin room d'in.
yana shiga room d'in ya zare hannayen sa daga aljihu ya nad'e su a kirji yaja ya tsaya.
inspector Nasir ya dube sa, ya yi murmushin gefen baki, a ransa yake fad'in
"Wannan fa d'an zafin kai ne, dube shi kamar wani boss yawani b'ata rai, ya juye tamkar shine sojan."
a fili kuwa cewa ya yi
"Yauwa Dr bari mu baka guri ka gudanar da aikin ka, Major muje ta waje ko."

Sadam ya watsa masa mugun kallo cikin kakkausar murya ya ce
"A kiraka kana wani ji da kai who are you! idan kayi wasa sai Kayi sallen kwad'o a nan,
yarinya tana cikin wani hali kazo ka duba ta,
kana gayawa mutane magana,
mu da muke hana idanun mu bacci domin baku tsaro bamu ce mun gaji ba sai kai ne zaka wani ce wai lokacin baccin ka ne,
kai dole ma na baka wani punishment idan ka gama dubata ka biyo ni office!."
wani kallo ya bisa da shi sannan ya ce
"Go ehead for the punishment in zaka iya,
ku d'auke ta ku fita da ita a nan bazan duba ta ba!."
a fusace Sadam ya bud'i baki zaiyi magana
Nasir ya yi saurin ruko hannunsa.
"Please Major barshi ya yi aikin sa dan Allah babu tima.
ya janyo Sadam dayake nuna Dr A.A Fiya da hannu yana fad'in
"Who are you be careful."
ya jashi suka fito dan yaga Dr nan ba sauki damasan sa sai wani bud'ewa suke babu tsoro ko d'igo a gare shi.
za'a iya yin ba dai-dai ba,
karshe ya nimo masu taya shi rabon fad'a dan bazai iya shi kad'ai da wannan murd'ad'd'en Dr ba.
duk da kuwa kasancewar sa hukuma shi da yake likita yafisu zubin kakkarfan zaratan jaruman maza.

Dogon tsaki yaja a fili ya furta
"See this guy mttss."
yakuma jan tsaki akan wata patient sun d'aga masa hankili sun hanashi bacci, daya sani ma da baizo kasar ba, shi da ya gudo yazo dan ya huta amma daga zuwan sa an wani takurawa rayuwarsa, shifa wannan aikin in da yasan yadda zaiyi ya yakace shi a gareshi daya kakkab'e shi,
domin babu komai cikin aikin sai takura a hana mutum sakewa da hutawa kullum mutum bashi da lokacin kansa sai na mutane,
da Daddy zai duba masa da ya barshi ya jingina aikin nan gefe baya son damuwa.
kwafa ya yi a fili.
tare da sauke idanunsa kan bed in da take kwance flat kamar babu rai a jikin ta, tana sanye da riga da wandon bacci.
a hankali yashiga d'aga kafarsa yana takowa inda take.........!

Mommyn Twins ce

🌺 *FEERYAL* 🌺

*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*

( _Book 1_)

~Free page~

( _Bismillahirrahmanurrahim_)

*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

🅿�19

Dipp! karar sautin bugun zuciyarsa dai-dai san da idanunsa ya sauka a kanta.
babu zato yaji bugun zuciyar da baisan musabbabin abin da ya haifar da shi ba.
da karfi ya rumtse idanunsa yana sauraran sautin bugun zuciyarsa.
Chapter 42 · 0% Book details