← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 52

Sashe 24

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Hajja Umma tayi tana sauraran bayanan da Aunty take kora mata,
na duk abinda ya faru a baya da kuma abin da ya faru da Mommy yanzu ba da jimawa ba.
Aunty tad'aura da fad'in
"Nakanji tsoro wani lokacin na tsinci kaina cikin fargaba, wlh Hajja Umma ina son Feeryal bana son rabuwa da ita,
ni ko aljana ce ma ita ina son ta zan rayu da ita a haka,
abin da nake tsoro d'aya kada ta cutar da ni ko wad'an da nake tare da su, bana so na rabu da Feeryal, wlh ina son ta a haka."
Aunty ta karasa maganar cikin sanyin murya.
Hajja Umma ta jinjina kai sannan ta ce
"Yanzu ina Feeryal d'in?."
"Tana parlour tana ta kan wasa wai da kawayen ta, da ni bana ganin su, ni tsoro na ma d'aya kar ta faje da wasu tarika cutar da mutane."
d'an shiru Hajja Umma ta yi kana ta soma magana.
"Akwai wani malami a can jahar Bauchi awani gari da ake kira Duguri,
Allah ya basa baiwar fahimtar irin wad'an nan matsalolin,
ki kaita can koma mene ne zakiji, in har ba mutum bace bama kafin ku isa zaki nime ta ki rasa, dan bazan mance ba, lokacin jinyar Yayan ku da muka gama karad'e kasashe da dama bamu dace ba, a can gurun sa muka dace,
lokacin da mukaje wata mata tazo da kwatankwacin irin wannan matsalar sai dai ita haifar d'iyar tayi aka canza mata,
ya ce taje ta zo da yarinyar, 'yar tana goye a bayan ta a hanya ta b'ace, bata sani bama har sai da tazo zata kunceta ta shafa taji wayam babu komai a bayan ta,
ganin yadda hankalin ta ya tashi malamin yace ai dama ba 'yarta bace nasu ne ta koma gurin iyayenta,
shi da kansa yaje ya karb'o mata asalin d'iyarta a gurin su,
idan zaku tafi ki sanar mata da in da zakuje, in har Feeryal ba mutum bace baza ta soma dumfarar gabansa ba zata gudu, tun kafin ku isa,
zan bincika ko yana nan har yanzu dan shekarun da dama tun Yayan ku na d'an shekara uku."

Aunty ta ce "Amma Hajja Umma ba dai irin mushrikai d'in nan ba ko? yanzu sai susa ka kauce hanya."
"Haba Fatima ni da kaina bazan kaiki in da zaki halaka ki rasa imanin ki ba,
kin san ba irin wannan tarbiyyar na baku ba, haka nima ba irin wacce iyayena suka bani shi ba ke nan,
idan da yana shirka da tun zuwata ta farko bazan kara zuwa ba,
bare kuma har na tuna da shi a yanzu har nayi miki sha'awar zuwa gurin sa,
malami ne mai aiki da ilimin addini, ba irin masu fad'e-fad'e da karyace-karyacen nan ba,
zan bincika ayau d'in nan idan yana nan sai kubi jirgi kuje."

Aunty ta ce to. nan sukayi sallam.

A b'angaren Mommy kuwa, tana fita ta had'u da Ajeemal dasu Sahla suka kira sa.
da sauri ya tare ta yana fad'in
"Mommy lafiya? su Nabila sun ce min wai kin fad'i kina ihu."
"Biyo ni kawai Ajeemal kar ka tsaya anan da alama kaf yankin side d'in ta ta zagaye shi da kafin asiri."
kai ya girgiza shi sam baya son irin wad'an nan abubuwan da Mommy da Umma Karima suke yi,
baisan me ya kaita sashin Aunty'n ba da take maganar wani asiri.
su komai sai sun dangantashi da asiri.
sam baya jin dad'in yadda iyayen nasa suke zama da abokiyar zamar tasu.
yabi bayanta.

Suna shiga parlour'n ta Mommy ta zube a kan carpet tana dudduba kafafunta, da d'azu take jin sa tamkar za'a finceke su sufice daga ganganr jikinta.

"Kai Fatimah bakar munafuka ce, wannan zata iya kashe mutum da bakin asiri take aiki."

Fuska Ajeemal ya b'ata ya ce
"Mommy to me ya kaiki side d'in Aunty Mommy ku dai na yin haka fa."
wani uban harara ta buga masa.
"Rufa min baki dan ubanka me kasani a rayuwar duniyar, abin da yafi asiri ma in akwai Fatima zata iya, an tab'o uwar ka ai dole ka nuna b'acin rai, ai nasan ba banza ta barku ba,
dole ma na tashi tsaye,
kafin a fini karfi a kan 'ya'yana."

Bai kuma yin magana ba yaja bakin sa ya yi shiru yana girgiza kai kawai.
a sawace ta ce
"Wuce kabani guri ai najima da sanin 'ya'yana mata ne kad'ai masu tausayi na, dama ciwon 'ya mace na d'iya mace ce, da kazo ka same ni cikin halin da nake ciki ma d'azu da asirinta ya rike ni, da babu abin da zaka iya yi min ma acan sashin nata, sai dai in zanmutu ad'au gawata."
"Allah ya baki hakuri Mommy."
yafad'a yana nufar kofa ya fice abinsa.

Kamar yadda Hajja Umma ta fad'a, a ranar tasa a binciko mata labarin malamin da yake garin Duguri dake jahar Bauchi.
ta turowa Aunty cikakken adireshin sa har da lambar waya.
kana ta biyo bayan sakon da kira.
Aunty tana rike da waya tana saurarar karin bayanin da Hajja Umma take mata.
Hajja Umma ta d'aura da fad'in
"Idan kun d'au hanya ki ambata mata inda zakuje da sunan wanda zakuje gurin sa,
sunan sa malam Buba Mani,
na sami labarin tun a wancan lokacin bayan jinyar da mukayi a gurin sa bada jimawa ba,
ya daina jinya da shigan irin wad'annan kasadar daya shafi junnu,
ko an je masa baya saurara, amma kuje ku gwada Allah zai wuce gaba"
"Har jikina ya yi sanyi kuma Hajja Umma, anya zai saurare mu?."
"Insha'allah mu dai gwada mu gani, ni ma nafi kyautata zaton 'yar nan mutum ce, sai dai su jinnu basu da kama,
sukan iya sajewa a cikin mu tamkar mu d'in, surika yin komai irin namu, ku dai je muji,
in kuma ta koma gurin danginta a hanya to ai shike nan sauki ma ke nan."
jiki a sanyaye Aunty ta ce to.

Ko da Aunty ta sanarwa Daddy, da fari kamar bazai amince ba, amma dayaji ta ce Hajja Umma tabada yakinin mutumin baya shirka sai ya aminta.
ya ce zaiyi musu bukin zuwa jibi sai subi jirgi su tafi, har da shi za'a tafi.
da kuma Baba Rabi ko bukatar wani hidima zai taso a can suna da mai yi musu.

Bayan kwana biyu da faruwar hakan kuwa suka biyo jirgi daga Lagos zuwa Bauchi.
bayan Daddy ya sanar wa aminin sa gwamnan jihar Bauchi, zai shigo garin sa.
suna sauka a airport, suka taras da motar zuwa d'aukarsu a cikin airport d'in.
motar da gwamnan jihar Bauchi aminin Daddy ya turo a d'auke su a kaisu masauki.
direct government house aka wuce da su.
a kyakkyawar masauki na alfarma aka sauke su,
bayan sun gaisa da mai girma gwannan jihar Bauchi, sukaci suka sha.
gwamna yaso su kwana kafin su wuce Duguri, Daddy ya ce kawai zasu wuce yau baya so su b'ata lokaci.
nan da nan aka shirya musu jagora zuwa garin Duguri, da motoci uku, biyu nasu d'aya na jami'an tsaro.
tun a mota a kan hanyarsu na zuwa Duguri Aunty tarika sanarwa Feeryal inda zasuje.
suna zaune a bayan mota su biyu Baba Rabi tana gaba a gefen mai zaman banza.
sai direba a mazaunin sa.
Daddy na d'ayan motar shi da deputy governor.
sai direbar dake jan su.

Aunty da tun d'azu hankalin ta ke kan Feeryal d'in tana ta son gano wani sauyi tattare da ita,
ta ce
"Feeryal kinsan ina zamuje?."
Feeryal dake tsaye kan sit tana leka titi ta jikin window mota tana kallon wuraren da suke giftawa ta girgiza kai alamar a'a.

D'an numfashi Aunty ta sauke cikin yin kasa da murya ta in da direba ko Baba Rabi baza sujiba ta ce
"Zamuje gurin Malam Buba Mani ne, malami kuma mai magani."

Feeryal ta b'ata fuska ta dawo jikin Aunty ta kwanta tana fad'in
"Ammie kice kar ya min allura, yabani magani kawai, zan sha bazanyi kuka ba, kar ya min allura."
tawani cuno baki tana dad'a shigewa jikin Aunty tana niman yin kuka.
Aunty dai shiru tayi tana binta da kallo ya yin da kaunarta ke dad'a shigarta bata fata ace ta tafi ta barta,
ita dai fatan ta arabata da gane-ganen da take, taji ta gani zata iya zama da ita ko ba mutum d'in bace.

Jin mota ta tsaya yasa Aunty d'agowa sai gani tayi ashe dai har sun iso, gasu a kofar wani d'an madai-daicin gida ginin laka.
Duk suka firfito daga cikin motocin,
inda Daddy da dipiti gwamna suka fito daga tasu motar.
cikin azama jami'an tsaron dake tare da su suka zagaye su sukayi wa gurin kawanya.
dattijan dake zaune a gindin bishiyar kofar gidan.
duk suka mike cike da girmamawa suka shiga mika musu gaisuwa,
duk da basu san ko su d'in su waye bane, amma sun fahimci su d'in ba kananun mutane bane.
Daddy ya mimmika musu hannu duk suka gaisa,
suna mai mamakin ganin sanyin hali irin nasa.
da gani ba sai an fad'a musu ba sun san cewa shi d'in bana wasa bane.
Dipiti gwamna da tun saukar su waya yake sai sannan ya sauke wayar, yad'aga musu hannu alamun gaisuwa yana fad'in
"Sannunku dai barkanku da war haka."
da sauri
duk suka amsa da "Barka dai ranka shidad'e, sannunku da zuwa."
shi kam sun gane shi mataimakin gwamnan jahar su, suna ganin sa a jikin posta.
"Yauwa godiya muke, am nan ne gidan malam Bubu Mani ko?."
cewar dipiti Gwamna yana nuna kofar gidan da suke.
suka ce "Kwarai kuwa nan ne gidan ai yanzun nan ma yashiga ciki duk muna tare da shi a nan."

D'aya daga cikin mutanen cike da girmamawa ya ce da su Aunty
"Hajiya bismilla ku karasa ciki mutan gidan suna ciki."
kana yayi saurin d'auko d'aya daga cikin taburman da suke zaune a kai mai hasken ciki ya shinfid'a wa su Daddy yana fad'in
"Bismilla ranku shidad'e ga gurin zama bari a kirawo sa."

Aunty na rike da hannun Feeryal Baba Rabi kuwa na rike mata da handbag d'in ta suka shiga gidan da sallama.
Chapter 24 · 0% Book details