Sashe 2
Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tuni idanun Hajiya Fatima suka kawo kwalla, tamasa kusa da mai gidan nata.
ta saka hannu cikin kwandon da jaririyar take ciki ta d'agota tana kare mata kallo kana ta rungumeta tana fad'in
"Daddy ina kaunar yarinyar nan ina sonta mutafi da ita."
a hankali Alhaji Abubakar yakai hanu cikin kwandon dake rike a hannunsa kasan inda aka d'aga jaririyar wata takarda ce ta bayyana mai d'auke da hoto da rubutu karkashin hoton jaririyar,
(FEERYAL) sunan dake rubuce a karkashin hoton jaririyar kenan.
a karkashin hoton kuwa wasu abun hanun gold ne masu kyau guda uku manya uku kanana da sarka da y'ankunne acikin gidan su.
ajikin kyakkyawan kwantenar gold d'in nan d'auke da tambarin kasar Russia.
Alhaji Abubakar ya d'ago hoton nan da kyakkyawan mazubin gwala-gwalai d'in nan yana fad'in
"Da alama dai wannan badaga kasar nan take ba, watakila hanya ce ta biyo dasu tagefen yankin nan suka samu had'arin ita Allah ya ketar da ita,
zai iya yiwuwa kuma y'ar kasar nan ce,
tambarin wata kasa baya nufin y'ar kasar ce,
tun da kayakin kasashe da dama suna shigowa kasarmu."
Hajiya Fatima ta karb'a a hannunsa tana fad'in
"Ikon Allah ta ina za'a fara cigiyar dangin ta bama y'ar kasa bace ashe, Allah sarki Daddy mutafi da ita kawai."
Masincin nan yadube su tare da fad'in
"Alhj ku tafi da ita Ubangiji ne ya turo ku ta fad'a a hannunku, idan kuka barta anan karshe asamu masu maidata cikin ruwan nan dan bakowa ne zai yarda ita d'in mutum bace, duk da tabbacin da ya nuna ba y'ar kasar nan ba ce,
ba lallai ayarda da hakan ba,
dan aljanu babu abin da bazasu iya yi ba,
kowa da wannan fuskar zai rika kallon ta,
idan har kunyi niyyar taimakon ta to kutafi da ita kawai."
kai Alhaji Abubakar ya jinjina kana ya zaro kud'i masu yawa ya mika masa yana fad'in
"Mun goge da taimako."
mutumin ya karb'a yana yi masa godiya.
nan suka nufi inda matarsu ya ke,
Hajiya Fatima na rungume da jaririyar.
ko da suka hau hanya Alhj Abubakar ya juyo yana duban Hajiya Fatima dake rungume da jaririyar tana ta aikin jijjigata.
murmushi ya yi tare da fad'in
"Raino ya yi miki kyau."
itama murmushin tayi ta ce
"Kamar nawa ko ina fatan hakan ta kasance amma da kamar wuya."
da sauri ya ce
"Gashi kuwa ta kasance kin sami kyauta daga Allah,
ki gode masa ta hanyar rukonta tamkar mu muka haife ta."
kai ta jinjina ta ce
"Wlh ina jin sonta acikin zuciyata lokaci guda naji hakan ya kasance da ni, sai nake ji kamar y'ar danayi nakudan ta, Allah nagode maka."
takarasa maganar da d'ago yarinyar ta sumbaci goshinta.
Alhaji Abubakar ya maida idanunsa titi yana cigaba da fad'in
"Kyakkyawar yarinya ban tab'a ganin kyau irin nata ba, ni dai har yanzu ina kokonto a kanta, idan ba jinsin mu bace Allah kagani mu taimako mukayi niyya,
kutaho ku d'auki d'iyar ku cikin salama batare da cutar da mu ba,
dan muma ba da niyyar cutarwa muka d'auke ta ba."
Hajiya Fatima ta girgiza kai tana fad'in
"Wlh har cikin raina ina jin cewa ita mutum ce irin mu,
nafi gamsuwa da cewa watakila ba daga yankin kasarnan take ba,
dan zubin halittar ta ya banbanta da namu,
sai dai Allah babu abin da bazai iyaba,
zai iya halitto ta cikin kasar mu takuma bambanta a cikin mu,
dan ikonsa ya wuce yadda ake zato."
kai ya jinjina cike da gamsuwa da kalaman ta,
dan ita d'in ta musamman ce a garesa..
Lagos
(A'A FIYA STREET)
A katafaren tamfatsetsen wani get Alhj Abubakar ya yi hon aka wangale masa get, ya kusa hancin motarsa ciki.
da sauri wasu sojoji biyu masu sanye da kaki suka rufawa motar baya da gudu, daga bakin get zuwa sashin Hajiya Fatima dake side 5 zuwa parking lot d'in dake side d'in, tafiya ne daya kai na mintuna 10 a mota.
a parking lot ya gyara parking, sojojin nan suka karaso da gudu d'aya ya tsaya a gefen Alhaji Abubakar d'aya a gefen Hajiya Fatima.
suka bud'e musu kofa cikin hanzari suka kuma sara musu tare da kamewa.
Alhaji Abubakar da Hajiya Fatima suka fito, kana sojojin nan suka maida murfin motan suka rufe tare da kuma sara wa suna fad'in
"Welcome sir welcome Madam."
hannu ya d'aga musu kana ya ce
"Sannun ku da aiki."
Hajiya Fatima ma barka da aikin tayi musu kana suka nufi cikin side d'in kai tsaye.
mai kamada aljannar duniya.
Suna shiga direct d'akinta Hajiya Fatima ta wuce, in da Alhaji Abubakar yawuce nashi d'akin dake nan cikin sashin nata, dan ya watsa ruwa ya rage gajiya.
wan da a kaf girman gidan iya sashin ta ne kad'ai yake da d'aki bayan nashi side d'in.
Bakin rantsattsen gadonta ta isa ta shinfid'a jaririyar da tun a hanya tayi bacci.
ta janyo katon blanket d'inta mai kyau da laushi ta rufe ta da shi kasancewar sassanyar AC daya karad'e ilahirin bedroom d'in.
ta wuce katafaren bathroom d'inta mai kyau da kawa tamkar d'akin kwana.
tsaf-tsaf da shi ko ina a goge kwalkwal sai sheki da tashin kamshi yake.
kyakkyawan pampo na alfarma ta matsa ta tari ruwa mai d'umi dai-dai in da jikin jariri zai d'auka, ta tari ruwa cikin bawun mai kyau da tsafta,
ta zuba tureren wanka mai sanyin kamshi cin ruwan sannan.
ta d'auko tafito da shi cikin d'akin.
ta kashe AC.
dai-dai lokacin da jaririyar take farkawa, ta isa da sauri ta d'auketa ta tub'e mata kayan kijinta.
kana ta sakata cikin ruwan tayi mata wanka da sabulu mai tsada.
ta dunkuleta cikin towel mai taushi ta kwantar da ita kan gado,
kana ta tattare gurin ta tsaftace shi.
sannan ta isa gaban ramb'asheshen wardrobe d'inta taciro wani kayataccen akwati mai kyau da kaganshi kasan na musamman ne sannan kuma badaga kasarnan yafito ba.
bud'e akwatin tayi tana bin kayan ciki da kallo, kai ta girgiza tare da sakin murmushi.
kayan yara ne masu kyau da tsada, wan da ta jima tana adanarsu.
duk sanda suka fita wata kasar sai ta shiga kasuwarsu tayi siyayyan kayan jarirai.
dukda kuwa bata da tabbacin samin cikin dan har tafara cire rai da samin haihuwa.
Tana cikin shirya ta aka turo kofa da sallama.
ta tad'ago da murmushi tana amsa sallamar.
shima murmushin yake aika mata ya karo bakin gadon ya zauna yana fad'in
"Ammie'n FEERYAL tun yau anfara nuna min anyi baby anshare ni, an barni nayi komai da kaina,
da ma ance idan mace ta haihu tofa daga ranar soyayyar ka tadawo rabi rabin kuwa za'a maida kan d'anka,
to nagode tun da iya rabi ne ba duka Feeryal zata kwace min ba,
zan samu a bani abinci kuwa?."
yakarashe maganar yana d'aukar FEERYAL data sha mata kwalliya cikin wani dogon rigar jarirai mai matukar kyau da d'aukar ido.
ido ya zuba wa yarinyar tare da fad'in
"Sarki ya tabbata ga Ubangijin halittu daya halicci wannan kyakkyawar halittar, tabarakallah masha'allah."
murmushi Hajiya Fatima data amshi sunan Ammie tayi ta ce
"Ayi min afuwa yanzu ma kuwa zan baka abinci,
bari nashiga kichin yanzu na samar maka abincin da zakaci."
Hannunta ya rike ganin tana kokarin mikewa ya ce
"Dakata mufara samar mata da nata abincin kafin,
muje asibiti musami shawarwari gurin likitocin yara, ta in da zamu inganta mata lafiyarta da kuma abincin da zata rika ci."
kai Hajiya Fatima ta girgiza kana ta ce
"Kuma yunwa takeji da gani, tun d'azu take ta kananun kuka."
mayafinta ta d'auka yana gaba rike da FEERYAL tana biye da shi suka fita,
direba yakaisu asibiti.
Kasancewar likitan sananne ne agurinsu,
Alhj Abubakar ya yi masa bayanin komai kan tsintarta sukayi.
bayan likitan ya bincika lafiyar ta da nazari kan abincin da zai karb'i jikinta.
ya shaida musu madara bazai d'auki jikinta ba, idan har akace za'a masa kan sai tasha madara,
karshe ta iya rasa ranta dole nono ne kad'ai zai iya d'aukar ta.
Alhaji Abubakar ya ce
Za'a nimi mai shatar da ita, Hajiya Fatima ta ce ina ita zara shayar da ita.
Da amincewar maigidan nata atake agun aka sakamata sinadaran da zasu kawo mata ruwan nono bayan wasu y'an awanni suka juyo gida.
Kan kace me ruwan nono ya kawo tamkar mai sabon haihuwa kuma na fari, haka ruwan nono yaciko.
nan da nan kuwa yarinya ta karb'i nono takama sha.
Washegari da safe.
Hajiya Fatima ta shirya jaririyarta cikin wasu kaya masu kyan gaske, suna zaune a parlour,
Alhaji Abubakar nazaune a gefen ta yana kallon yanda take yashar da jaririyar, gwanin ban sha'awa.
murmushi ya yi tare da shafo gefen fuskarta.
"Yamiki kyau sosai shayarwa, Allah ya baki iko da lafiyar cigaba da shayar da ita."
da ido ta amsashi tana aika masa murmushi.
Knocking akayi tare da turo kofar parlour'n.
burki taja daga bakin kofar tarike hab'a tana kallon Hajiya Fatima da jaririyar da take shayarwa, cike da matukar mamaki.
murmushi Hajiya Fatima ta yi ta ce "Ki karaso mana Farida, ya kika tsaya daga bakin kofa."
Fuska ta yamutsa gulma na cinta har kafarta na rawa tana alla-alla ta yuya ta ce
"Daddy wai kazo inji Hajiya."
tana gama fad'i ta juya da sauri.
gudu ta saka bata tsaya ko ina ba sai side d'in Hajiya Halima mahaifiyarta kuma uwargida ga Alhaji Abubakar Fiya.
a parlour ta tadda uwar tata, da kuma Hajiya Karima mata ta biyu ga Alhaji Abubakar, da y'ay'an su duka.
kamar zata zube kasa cikin haki take fad'in
"Mommy Aunty ta haihu."
cikin rashin fahimta Hajiya Halima wato Mommy ta ce "Ke wata Aunty? kin shigo a razane duk kin razana mutane."
murya na rawa cike da tsugudidi ta ce
"Aunty Fatima wlh yanzu nan naganta tana baiwa jariri nono, Daddy na zaune a gurin."