← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 52

Sashe 18

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunkan takaraso inda Aunty take tasoma d'aga murya wadda hakan ya soma janyo hankalin 'yan gidan garesu aka soma taruwa.
cikin d'aga murya sosai Maom take fad'in
"Meya shuka miki da zai girbe Hajiya Fatima? bazan yarda da sharri ko k'azafi ba, shi ke nan ko wani cin maita a gidan nan akan Zaraddin zai kare,
ko da shike kai ka janyo shiyasa ko wani dattin bola a kan ka yake karewa."
ta harari d'an nata dai-dai lokacin da suka karaso in da Aunty suke.
"Hajiya Fatima nace me ya shuka miki da zai gurba?."
Aunty bata ko kalli ta ba ta dubi Zaraddin da kyau kana ta mai da duban ta ga Feeryal sannan ta ce
"Wannan shi ya cire miki pant?."
kai Feeryal ta gyad'a tana yi masa kallon tsoro.

Wani uban kururuwa mai had'a da manya-manyan ashariya Mom ta kurma.
"Kutumar uban can, kaga kulu uwar sharri, yau tanan kika b'ullo, Hajiya Fatima,
a ina ya ganta da har zai cire mata pant,
sharrin fyad'e zaki masa, ina abin kwakula ajikin wannan figigiya tatsitsiyar!?
na rantse da Allah bazan yarda ba sai kin wanke zargin da kike masa a gaban kotu,
yihuhu jama'a kufito kuji wlh Hajiya Fatima ba ki isa ba, baki isa ki bakanta min d'ana ba,
sharrinki a kanki zai kare,
aljanar 'yar da kike b'oye ta ina zai ganta har ya yi yunkurin yi mata sharrin da kike kokarin kulla masa!
bazan yarda ba yau Fatima zaki san da ni Nafisatu kike zance, idan kin saba yi wa wasu ki share to ni wlh karyan ki ba ayi ruwan isarki ba wlh!
kije can kije ki nimi wanda yakuma yiwa mata fyad'e,
badai Zaraddin ba wlh."

Ta bigi kirji baki na kumfa cike da bala'i da masifa had'e da rashin mutunci.
kan kace me mutan gidan kaf sun taru a gurin,
har hankalin security yafara karkata wurinsu.

Mommy da Umma Karima suka shiga tambayar Mom abin da ke faruwa, ta ce
"Sharri zatayi wa Zaraddin wai ya cirewa wannan mayyar aljanar pant, idan ba sharri ba a ina Zaraddin ya ganta ita da ake b'oyewa a kunshe a d'aki kamar daddawa a kwano, a ina zai ganta."
hab'a Mommy ta rike ta ce
"Tabd'i jam lallai akwai aiki, yau d'in ma fyade za'a ce akayi mata ke nan,
lallai wannan lamari akwai lauje cikin nad'i."
ta wasawa Aunty kallon banza.

Umma Karima kam cewa ta yi
"To ai ba farau bane, yau aka fara sharri wa mutane akan ta irin haka, har makaranta akaje aka tozarta malami, da ganin yarinyar nan ba karamar hatsabibiya za ayi ba, tun tana kankanuwa tasan yadda ake makalewa maza, ita kad'ai ce a makarantar ba sauran yara ne, me yasa hakan bai tab'a faruwa da wataba sai ita, shine abun yanzu ya dawo har cikin gida ko, to wlh bazamu yarda ba."

"Haba Hajiya Karima wani irin magana ne wannan yanzu fisabilllahi wannan yarinyar har ta san yadda ake bin maza haba ku kuwa, kuyi adalci a maganar ku."
cewar Ammah tana binsu da kallon takaici.

Fuska Umma Karima ta yamutsa
"Wani irin adalci kuma daya wuce wannan, ko aki ko aso wannan ita ce dai gaskiyar,
sharri ya tashi daga waje ya dawo cikin gida,
kada a aje mana gamasheka a cikin gida, ta tashi ta koyawa yaranmu iskanci da bin maza, dan da gani karuwa za ayi anan."

Idan ran Aunty ya yi dubu to ya b'aci, bata san san da ta d'auke Umma Karima da marima ba.
cikin tafasar zuciya tashiga nuna ta da yatsa sannan ta ce
"Kada ki kara danganta min 'ya da karuwa, gargad'i na karshe, idan kuma bakijiba zakiyi nadamar kuma fad'in haka!."

Umma Karima ta dafe gefen fuskantar ta tana fad'in
"Bura'uban can ni kika mara Fatima, ni zaki ki mara?."
"An mare ki, ko yanzu kika kuma jefinta da kalmar karuwa sai na kuma d'auke ki da mari!."

Umma Karima tayi wani kukan kura zarayi kan Aunty da sauri Ajeemal ya shiga sakaninsu.
Umma Karima sai wani tsalle take ita a dole a barta ta shake Aunty.
baki na kumfa take fad'in
"Wlh yau sai na nuna miki ni cikakkiyar 'yar tasha ce, ni zaki mara Fatima, ko sa'a ta bata tab'a kai hannu jikina ta share ba, ba re ke!
kud'in ubanki bazai bani tsoron naci uban ki anan ba,
wlh yau sai na nuna miki ainihin ko wace ce ni."

Ammah data ruko hannun Aunty tana janta gefe ta ce
"Dan Allah Hajiya Fatima kada ki kulata ba girman ki bane, irin wad'an nan, abun kunya gaba suka bashi ba baya ba."
"Rabu da ni Hajiya Safiyyah matar nan ta ishe ni,
ai ba yau nasan cewa ke 'yar tasha ba ce, mai sai da shinkafa akan titi ba, ke in banda ma kaddara ai ko in da nasa kafa ba ki isa ki sakaba bare nayi zaman kishi da ke,
kurabu da ita tazo zan nuna mata kalar tawa barikin."

Hon d'in motar Daddy da yanzu ya shigo ne ya mai da hankalin su wajen sa.
da sauri Ajeemal ya nufi gurin motar ya bud'e marfin gefen da yake, yana ya yi masa sannu da dawowa.

Jim kad'an Daddy ya fito daga cikin motar ransa a b'ace, ga dukkan alamu dai Ajeemal ya shaida masa abun da ke faruwa.
ya nufo inda suke rai b'ace.
a kusan tare motar Alhaji Tukur wato Dad mahaifin su Zaraddin da na Alhaji Sulaiman Abbieh mahaifin su Miemie suka shigo.

Ganin yadda yayan nasu yake nufar inda mutan gidan ke tara da alama ransa a b'ace yake.
yasa su fitowa cikin motocin su da sauri suka rufa masa baya.

Daddy na isa baiyi wata-wata ba ya janyo kwalar rigar Zaraddin.
ya tura shi wa
security kattin maza guda biyu dake biye da shi cikin murya mai nuna zallar b'acin rai ya ce

"Ku tub'e shi ku zane shi!."

Nan da nan suka shiga aiwatar da umurnin da aka basu.
suka tub'e masa riga da wando suka barshi da iya gajeren wando.
Zaraddin daya gama tsurewa yashiga bada hakuri yana fad'in
"Dan Allah Daddy kayi hakuri wlh ba abun da na mata, bammata komai ba, ni ko ganin ta ma banyi ba yau."
tuni security
suka zare bel d'in jikinsu suka shiga shinfid'a masa ta ko ina, yana ihu.

Ido Dad ya rumtse, yana jin zuciyarsa na tafasa.
da kyar ya iya dai-dai ta kansa ya yi kokarin b'oye fushin sa.
yana fad'in
"Ku kara masa sha-sha-shan banza, mu zaka b'atawa sunan family."
Mom gaba d'aya ta birkice ji take kamar ta je ta tsare ta ce kada wani ya sake dukar mata d'a, amma ina babu hali Daddy ne da kansa ya bada umurnin hakan.
ba Zaraddin ba ko Dad akasa a zane babu wanda ya isa ya dakatar da faruwar haka.
jikin Zaraddin yayi taya-taya ya daku sai birgima yake a kasa.
Daddy ya d'aga wa security hannu tare da fad'in
"Ku barshi haka."
aiko cak suka d'auki umurni kowa janye belt d'inshi a kansa.
Daddy ya sunkuya ya kwashi kayansa ya wasa masa a jikinsa.
ya nuna sa da hannu
sannan ya ce "Tashi kabar gidan nan yanzun nan kayi nesa da nan! kar ka sake nakara ganin ka a eriyar unguwar nan!."

Abbie ya yi saurin masowa in da Daddy ya ke ya ce
"Allah yahuci zuciyar ka Yaya, dan Allah ayi hakuri a barshi, ya yi laifi kam, zai gyara kuskuren sa gaba."
"Sulaiman yaron nan bansan me ke damun sa ba, yana ta kokarin dole sai ya b'ata mana sunan family,
ni da shi na kirasa na zaunar dashi,
kan ya natsu ya dai na biyewa abokan banza,
suna sha-shan ci,
suna gama makarantar da suke waje zan turasu shi da 'yan uwansa, akasar nan ma ke nan a gaban mu, yake irin wannan hali bare kuma da yaga baya kasar ma baki d'aya,
babu idon kowa a kansa, bazai dai na ba ya tafi kawai idan ya gyara ya dawo!."

Dad ya taune lab'b'ansa ya yi saurin yiwa Mom ido dayaga tana shirin magana.
ya dubi d'an nasa cikin b'acin rai ya ce
"Ta shi aka ce ka tafi! wannan shine hukuncin da ya dace da kai."
ya shure shi da kafa yana cigaba da fad'in
"Kai d'ayan ka baka isa kasa mana ciwon kai ba,
ba kai kad'ai muka haifa ba,
kuna da yawa, tashi ka b'ace mana da gani, ku d'auke shi ku fita da shi!."
security suka janye shi sukayi waje da shi.

Dad ya dubi Daddy cikin kwantar da murya ya ce
"Allah ya baka hakuri Yaya,
wlh ina iya bakin kokari na akan ganin ya natsu kamar sauran 'yan'uwansa."
kai Daddy ya girgiza ya ce
"Banga gazawarka akan tarbiyarsa ba, d'an yau shiriyar Allah ce kad'ai mafita a gare sa, Allah ya shirya mana zuriya baki d'aya."
duk suka amsa da amin.

Daddy ya juya ya nufi side d'in sa bayan ya ce, kowa ya koma nashi matsugunin.

Jikin Aunty yayi bala'in sanyi, bata tab'a sammanin abin zaiyi tsamari har haka ba.
Mommy da Umma Karima suka bita da kallon banza, kowa yaja tsaki.
Umma Karima ta ce
"Babbar munafuka, d'a da gidan yayan uban sa ki tsige shi aciki da zallar iya munafurci, zan waiwayo ta kanki bawai na kyale ki bane."
Mom kuwa tsabar bakin ciki da tafasar zuci bata iya bita kanta Aunty ba juya fuuu ta yi side nata.

Ammah ce ta bubbuga kafad'ar Aunty ta ce
"Karki d'aura alhajin komai a kanki, baki da laifi ko kad'an."
kai Aunty girgiza jiki a sanyaye ta ce
"Wlh bansan har haka abun zai kai ba."
Ammah tayi saurin katse ta
"Yi tafiyar ki duk wanda yaji haushin ki ma shi ya sani, hukuncin da akayi masa shine dai-dai da abun da ya aikata, ko a fad'i ko kar a fad'i ma hakan ne,
yunkurin fyad'en da ya yi mata ba abun haushi bane sai hukuncin da aka yanke masa;
wlh ko Faisal ne ya aikata hakan ina goyon baya d'ari bisa d'ari fiye da hukuncin da aka yankewa Zaraddin."
Aunty bata kuma iya cewa komai ba taja Feeryal suka bar gurin.
Chapter 18 · 0% Book details