Sashe 32
Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Uwar amarya Mommy ta fito da ka kawayen ta zasu gurin walima, ta cab'a kwalliya cikin wani arnen lashi mai tsadar gaske tasha d'inkin manyan mata,
matan masu nera.
Umma Karima ita ma da nata kawayen kusan shiga iri d'aya sukayi da Mommy sai dai kalar leshin ta daban ne amma mai tsadar ce ita ma.
Motar Hajiya Luba ne ya kunno kansa cikin gidan.
bayan ta nunawa security pas d'in gayyatar ta,
suka bud'e mata get ta shigo.
Mommy suka tsaya suna zaman jiranta su karaso dan ta gane motar ta.
a babban parking lot d'in gidan in da motoci ke cike tam nagidan dana jama'ar da suka sami halarta bikin ke tare.
direban ta ya dai-dai parking.
Hajiya Luba suka fito ita da wata budurwar yarinya.
suka karasa in da su Mommy ke tsaye.
suka rungumi juna da Mommy,
Hajiya Luba ta saki Mommy tana fad'in
"Kaga uwar gida a gidan Alhaji Abubakar Fiya, Allah dai yasa bamu makara a walimar ba."
"Kun dai kusan makara dan har an fara, na ce gajiyar jiya ce ta hanaki isowa da wuri, to ya gajiyar jiyan."
"Wlh ke kam dai ingaya miki bawai gajiya bace ta zaunar da ni, d'iyarki ce gata nan Kuraiba ta b'ata min lokaci, kin san shirin 'yammata sai a hankali, a fenta nan a fenta can,
ke Kuraiba ga Mommyn ku nan ki gaida surukan ki."
Budurwar da aka kira da Kuraiba ta ce
Ina yini."
ta fad'a a takaice.
Mommy tayi murmushi tana amsawa da
"Lafiya lau Kuraiba ya school."
ta ce "Alhmdulillah."
"Kuraiba fa an girma nakai 1y rabon da na ganta,
har tafi Farida a tsaye."
cewar Mommy, tana dubanta da murmushi.
Hajiya Luba ta ce
"Ni da nayi zaton ma lokaci guda za'a had'a bikinsu a wuce gurin."
"A'a dai adai bi d'aya bayan d'aya, ayi shi daban-daban ai zaifi dad'i, surukar tawa ko ba laifi."
cewar Mommy tana duban Kuraiba.
"Da dai mun karasa kar a gama muna tsaye muna wata maganar muyi wacce take gaban mu, abar wannan da ba'a san yuwuwarsa ba tukun."
cewar Umma Karima da tun farin maganar ta had'e rai da alama dai akwai wata a kasa,d'ayan biyu ko bata son faruwan lamarin da suke magana a kai ko kuma akasin haka.
Hajiya Luba ta ce
"Ai Insha'allahu Kuraiba ita ce surukar Alhaji Abubakar Fiya na farko, mudai karasa wanda ake cikin yanzu dai kawai, kafin zuwan nasu lokacin."
FEERYAL data fito daga side d'in Hajiya da sauri, sukayi kicib'us da su zasu wuce.
Mommy ta bita da harara tana fad'in
"Ke kutumar uban ki bakya gani ne zaki bige mutane yarinyar banza kawai."
Umma Karima ta kai mata zunguri a goshi tana cewa
"Tsintacciyar mage bata mage wuce ki je in da aka gayyace ki."
"Wace ce wannan d'in?."
cewar Hajiya Kuba tana nuna ta.
tsaki Mommy taja ta ce
"Yarinyar da Hajiya Fatimah ta tsinto mana."
"Wai ita ce haka anya ba sato musu yarinyar mutane tayi ba a asibitin wata kasa ba kuwa?
bata shiga US after 2 mon before kawo yarinyar gidan nan ba."
Mommy ta ce
"Hm zata iya ai dan rashin haihuwa babu abun da bazai iya sata ba, an gama yawon gurin malamai niman maganin haihuwa an rasa ai dole ta b'ullo ta wata hanyar."
"Amma dai tayi asara, taraba yarinya da danginta dubi kyakkyawar yarinya fa dan Allah."
cewar sauran kawayen nasu.
Feeryal bakin get na side d'in Aunty ta tsaya har saida su Mommy suka wuce kafin ta dawo ta d'au hularta da ya fad'i lokacin da Umma Karima ta zungure ta.
Ta sunkuya ta d'au hularta tana mikewa, ta saki murmushi ganin wad'an da suke kusa da ita ta ce
"Laa Chuchu Chulu baku tafi ba da man?."
"Babu tafi ba muma mun tsaya jin wa'azin ne mu je gurin walimar dan anyi nisa da farawa kar a gama babu je ba."
"Ni dai bazan je ba, akwai su Mommy a gurin zasu kore ni ko su duke ne."
"Baza suyi miki ko mai ba zo muje, bazamu zauna ma a kusa da su ba."
yatsa ta saka a hab'arta ta ce
"Kun tabbata."
"Mun tabbata."
suka had'a baki wajen fad'a.
Suka sakata a tsakiya suna tafe a hankali suka nufi gurin da ake gudanar da walimar.
har suka dumfaro filin gadan-gadan babu wanda ya lura da su.
malamar da take gudanar da walimar ita ta fara lura da su.
zumbur ta mike tsaye tana fad'in
"Yaaaku jama'a ko shin kuna ganin abin da nake gani kuwa!?."
Gabakid'aya jama'ar gurin sukabi inda take nunawa da hannu.
nan da nan gurin ya kace da hayaniya had'e da kururuwan mata suna fad'in
"Wayyo ga zakuna zakuna sun shigo gida."
tuni mata suka fara hargitsewa suna niman mafaka domin ceton rayuwar su.
zo kaga mata in da suke zubewa kan kujeru suna karya kujeru.
Mommy da aka tureta a kan kujera ta zube kasa shirim, ta kasa ko da iya motsawa tsabar tsoro tana baje a kasa jikinta na rawa.
idanunta a kan Feeryal da manya-manyan zakunan da suka sakata a tsakiya.
suna cigaba da dumfaro gurin gadan-gadan.
Hajiya kuwa da rarrafe take tafiya ta tafi bayan wasu kujeru can ta b'oye, ta rufe idanunta gam-gam.
tana karanto addu'ar ta da ta saba
"Wasayyahu wasayyahu wasayyahuuuuu yasin me manjaga li'eelafi kafa bakwai yasin kafa dubu lakadija'akum kafa d'ari ba d'aya."
Mata sai karo da juna ake ana zubewa kasa, sai ihu da niman agaji.
Ganin haka yasa Feeryal taja ta tsaya.
tana bin jama'ar da kallo.
tsoro taji ganin idon Mommy a kanta sai ta juya da sauri ta gudu, tana gudun kada Mommy'n ta taso ta bige ta, dan a zaton ta, zuwan gurin su da tayi ne yasa ran Mommy b'aci, kuma ta rigada ta san cewa ta hanata zuwa in da suke.
Side d'in su ta koma ta haye upstair tana hango yadda mata ke gudu suna fad'uwa suna karya kujeru.
Dariya ta tuntsure da shi hango wata katuwar mata ta zube kasa timm , mata sai zubewa a kanta suke sai ihu take kurmawa takasa tashi.
tana ta juya katon d'uwawu a kasa.
"Ke Feeryal."
da sauri ta juyo jin maganar Aunty a bayanta.
Aunty ta ruko kunnen ta ta ce
"Ke ce ko, ke ce kika sa duk wancan ko?."
kai ta girgiza tana kunshe dariya ta ce
"Auchii Ammie zafi."
"Me yasa kika yi haka Feeryal su d'in sa'annin ki ne, ko abokan wasanki."
d'an karamin bakinta ta cuno
"Ba ni bace fa Ammie babu ruwana Chuchu da Chulu ne, suke razanin su."
fuska Aunty ta had'e ta ce
"To ki ce dasu su daina su saida abinda sukeyi haka, ya isa!."
Duk da tazaran da ke sakanin su wan da ko ihu mai tsananin karfi tayi daga in da take zuwa gurin walimar nan baza'a jitaba,
amma sai gashi ta kira sunan su sun waigo, ta ce
"Ammie na ta ce ku dai na razanin su."
aiko nan take suka juya su na girgiza gashin jikin su, da suka rikid'a suka koma manyan zakuna masu matukar ban tsoro.
suka fice a filin taron.
Sai a lokacin hankalin security yakai kan jama'ar da ke ta ihu,
suka shigo ciki da sauri.
mutane kuwa ganin juyawar zakunan nan yasa wad'anda suka fad'i mikewa tsaye suna kuma niman mafaka.
Ganin security yasa wasu dawowa cikin hayyacin su.
Hajiya ta fito daga mab'oyar ta tana ciccire ido da fad'in
"Kun harbe su kun kashe su ko ya?."
security suka ce
"Su wa suka shigo Hajiya?
babu wanda suka shigo kai tsaye batare da shaidar izinin shiga gidan nan ba."
Hajiya ta ce
"Injiwa ai wad'annan basa bukatar niman izini,
ko ku suka samu loma d'aya zasuyi da ku a bakin get babu wanda ya sani,
ku bisu ku harbe su in baku kashe su ba karsu kuma dawo mana nan, zakuna ne suka b'allo suka shigo mana gida."
Sai a lokacin Mommy da ta sha tumurmusan mutane ta mike da kyar tana kad'e jikinta.
sai matse ido take kafa tayi tsami.
Umma Karima kuwa bakin nan mud'uss ya mutu itama ansha birgima gaye ya b'aci.
Farida amarya ma ta tumurmusu ba kad'an ba ita da kawayen ta.
Su dai jami'an tsaron basuga wani bakon halittar daya shigo gidan ba bayan duk jinsin mutane ne babu na dabbobi.
kofar baya ma a kulle take ko mutum bazai iya bud'e shi ba bare kuma dabba, in ta sama ne ma bazasu iya hayewa su shigo ba, babu wata hanyar da zasu iya shigowa sai dai in ta ainihin kofar gidan.
suka juya da sauri suka soma bincikar gidan rike da bindigogin su, lungu da sako.
amma babu wani halittar da suka gani face mutane wad'an da suka ziyarci bikin.
Haka nan taron walima ya watse, da yawan mutane kuwa kowa ya kama gabansa.
Da karfe 6 na yamma 'yan d'aukar amarya suka zo, aka d'auki amarya a kaita tsarenren gidan ta na gani na fad'a.
Sai da aka nutsu aka fara maida zance.
uwar amarya Mommy kam ana zaune ana jinyar kafa dan ko kafa tayi tsami.
Hajiya'n Dubai da ita bata je gurin walimar ba tana sashin Hajiya lokacin da abin ya faru, ta ce
"Wai kuma kun ganta da idon ku tazo da zaki, a ina ta sami zaki? kai gaskiya da sake wannan 'yar ban yarda da ita ba."
Hajiya ta ce
"Wlh idona idon ta da jibga-jibgan zakuna,
'yar nan ta girma a maitanci duk jinin mu taso sha kurwar mu ya mata d'aci, shiyasa ta kyale mu,
ku kira min Abubakar yau za'ayi ta ta kare,
ke Bishira kirawo min matar tasa itama 'yar gol d'in tasa ba, da mayayyar yarinyar duk suzo nan."