Sashe 41
Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da karfi mator gaban su ya taka burki, kad'an yarage suyi karo da juna.
da sauri ogan b'arayin ya d'ago dan ganin me ke faruwa.
wanda ke jan motar nasu ya ce
"Ogo kalli can ka gani, kamar ba hanyar da muka shigo muka biyo ba."
cikin tsawa ya ce
"Hanyar ce mana dalla ku hanzarta mu tafi ba lokaci."
da sauri direbar d'aya motar gaban nasu ya sauko yazo ya bud'e gefen da ogan nasu ya ke ya leko yana fad'in
"Oga ba hanya fa ta nan, ina ga mun b'ata hanyar ce sai dai mu juya."
"Maza koma mota mu juya da sauri."
"To oga."
ya rufe motar ya juya da sauri yakoma d'aya motar suka juya a d'ari.
sunyi tafiyar 5min a razane suka kuma jan burki sakamakon ganin wani irin haske mai tsananin k'aifin haske daya haske musu ido.
nan take kuma wasu nau'ukan tsuntsaye masu girman gaske suka bayyan ta cikin hasken,
suna shawagi ta cikin haskennan suna karkad'a fukafukan su.
ya yin da kukan su ya karad'e cikin kunnuwan su, tamkar zasu fasa musu dodon kunnuwa.
A kid'ime ya ture FEERYAL daga jikinsa,
ya kai hannu ya toshe kunnuwan sa, da dodon kunnuwan nasa suke barazanar zazzagowa waje.
yakuma rumtse idanunsa da yake jin tamkar hasken nan zai fasa masa kwayar idanunwa.
ba shiri ya b'alle murfin motar ya fito yana layi da tangad'i cikin tsananin jin azabar da kunnuwansa da idanuwansa suke masa tamkar zasu zazzago su fad'o kasa
A b'angaren 'ya'yan gidan nasa ma, duk kanin su sun fito daga cikin motocin, kowa da ido a rufe kunne a toshe da ala ma dai irin abin da ogan nasu yake ji shi sukeji suma.
FEERYAL na cikin mota a rakub'e sai b'ari da kuka take, bata ma san abinda ke faruwa ba, zaton ta ma sun iso in da zasu kawo ta ne.
Tawagar Major Sadam dana Inspector Nasir a kusan tare suka iso.
jiniyar polisawa da na sojoji ya karad'e cikin unguwar.
san da motocin jami'an ya karyo kwanar layin,
kamar kiftawar ido haske da karar tsuntsayen nan suka b'ace cikin dakika d'aya, b'arayin nan suka nimi abin da suke ji cikin kinnuwansu da idanunsu suka rasa.
hanya ta bud'e samb'al suke hango hanyar ficewa daga unguwar.
da sauri cikin azama ko wannensu ya shige cikin mota, suna kokarin gudu.
jiyo jiniyar hukuma na dumfaro su.
sai dai kafin suyi aune hukuma ta cin musu.
Daga can jami'an tsoro suka soma magana da amsa kuwa.
"Ku dakata a gurin ku aje makaman ku, mun cinmuku muna zagaye da ku."
Da karfi ogan b'arayin ya naushi jikin sit d'in mota yana fad'in
"Oh sheet! maza wuta!."
duk kanin su suka d'auki bindigogin su, suna fita daga motocin suka soma harbi.
tuni jami'an tsaro suka soma musanyar wuta da su.
tuni unguwar ta karad'e da karar harbi kamar za'a tashi unguwar da b'arin wuta tamkar ana diyafara.
mutanen unguwa kuwa kowa ya yi flat a cikin gidan sa yana jiran ta Allah ta kasance.
B'arayin nan basu sakaita wutaba har sai da bulet d'in su ya kare.
inda jami'an tsaro suka sami nasarar harbin mutum biyar a cikin su, ciki kuwa har da ogon nasu da aka harba a kafa,
sauran suna kokarin gudu aka kamasu da hannu.
mutum uku a ka harba acikin jami'an tsaron, biyu police d'aya soja.
Da gudu Major Sadam ya nufi gurin motocin b'arayin yana b'alle makarin bulet d'in dake jikinsa, ya yi wurgi dashi kasa, dai-dai san da yake karasowa jikin motocin, yana haska cikin su da touch d'in wayarsa.
da sauri ya kai hannu ya bud'e marfin motar da ya hango FEERYAL a ciki.
ta tafi gaba d'a zata fad'o kasa,
dan ajikin murfin motar tage rakub'e.
tun lokacin da aka fara harbi na farko ta suma.
cikin hanzari ya tarota ta fad'o jikinsa, ya d'agota cak ya rataya ta a kafad'ar sa.
dai-dai lokacin da inspector Nasir yake karasowa gurin hankali a mugun tashe ya ke fad'in
"Ya dai Sadam badai harbin ta akayi ba?."
"No! harbi bai same ta ba, sai dai she painted, firgici yasa ta suma, muyi sauri mu kaita asibiti dan Allah Nasir, wani asibiti za'a samu yanzu."
cikin hanzari ya nufi d'aya daga cikin motocin su,
inspector Nasir yabi bayansa yana cewa
"Za'a samu general hospital ma, sai dai matsalar ba lallai ne a sami likitocin su ba,
a kwai wani asibiti a d'an gangaren J.Y.P d'in nan.
asibitin wani babban likita ne da yake aiki a kasar waje, yawancin lititocin da suke aiki a asibitin gidajen su yana kusa da asibitin, har da shi kansa me asibitin ma gidan sa na kusa a gurin,
sai dai ba lallai ne mu same shi ba dan bana da tabbacin yana kasar, amma ko sauran muka samu ina da yakinin zasu fito dan suna da kokari sosai kan majinyata."
"Muje can d'in please Nasir yi sauri dan Allah bata numfashi."
ya bud'e mota ya shinfid'a ta a gidan baya.
dukan su suka bada umurni wa tawagar su, su kwashe b'arayin su tafi da su.
Major Sadam yaja motar da kansa batare da ya bukaci wani jami'in sa ba, inspector Nasir na gefen sa suka nufi hospital d'in.
Suna isa kofar katon asibitin ya yi hon, mai gadi ya leko, ganin soja da police a gaban mota,
da sauri ya wangale musu get.
suka shige harabar asibitin, ya gyara parking suka fito.
da sauri Sadam ya bud'e inda take ya ciccib'ota, sukayi cikin asibitin.
Cikin hanzari ma'aikatan asibitin suka nufo inda suke da welcher.
Sadam ya ce "Not ina za'a shiga da ita?."
da sauri wani nurse ya yi gaba ya tura kofar ICU yana fad'in
"A shigo da ita nan."
Sadam ya shinfid'a ta kan bed yana cewa
"Ina likitocin ku suke?."
nurse d'in ya ce
"Tun 6 suka tashi, yanzu nan kuwa bada jimawa ba Dr A.A FIYA ya bar nan ya yi wa wata me ciki C'S ko 30min baiyi da barin nan ba,
amma gaskiya da kyar ya dawo sabo da yau ya shigo kasar, ya shigo asibitin ne kawai ya taras da ita cikin wani hali shiyasa ma ya tsaya har ya mata C'S d'in."
Da sauri Major Sadam ya ce
"Kirashi dan Allah ita ma wannan baka ganta cikin wali hali ba, yazo ya ceci rayuwar ta pls!."
Shiru nurse d'in ya yi yana tunanin ta in da zai fara tuntub'ar Likitan nasu,
ta ina zai fara gashi a gaban soja yakuma umurceshi, wanda aka umurta da ya kira shi d'in ma
a gefe guda shima sojan kansa ne.
bayan keyar sa ya d'an sosa ya ce
"Zaizo kuwa? adai kira wani Dr dai."
tsawa Sadam ya buga masa ya ce
"Kana kallonta a sume ka tsaya kana wani kame-kame,
shi wanda bai jima da barin nan ba shi yakamata ya dawo ya duba ta, sauran da duk yanzu sun jima da yin bacci ta ina zasu iya kulawa da ita yadda ya kamata, ka kirashi yanzun nan!."
Hannu na rawa yashiga lalub'o lambar Dr A.A FIYA. har kiran ya yanke bai d'aga ba.
Sadam yana tsaye yana ji dan wayar a handsfree ya saka, ya ce yakuma kiransa.
sau uku yana kira ba'a d'agawa sai ana hud'u tukun ya d'aga bai yi magana ba.
ganin ya d'aga ya yi shiru da sauri shi nurse d'in ya fara magana.
dan yasan halinsa idan zasu kwana a haka shi ba zai fara yin magana ba,
sai dai ya aje wayar idan ya gaji, kai da ka kirashi kai kasan sauran da kud'in ka,
ko ya kashe watar.
"I'm sorry Sir an kawo patient emergency."
tsaki ya ja tare da kashe wayar ya jefata gefe ya gyara kwanciyar sa, ya mai da kansa pillow.
Major Sadam ya ce "Ka sake kiran sa maza yasan wa yake wa tsaki anan kuwa!."
jiki na b'ari ya mai da kiran shikam yau tashi ta same shi wuta biyu ta gefe da gefe suke kokarin amsawa da shi.
nan ma wayar ta yanke bai d'aga ba, yakuma mai da kiran a karo na biyu har ya kusa yankewa ya d'aga.
da sauri Sadam ya karb'i wayar ganin ya d'aga ya ce
"Kana magana da Major Sadam Wakili, patient tana bukatar taimako kazo ka duba ta."
"I'm Doctor Abdurrahim A.A FIYA, yanzu lokacin bacci na ne."
d'inp ya kashe wayar gaba d'aya ya jefata gafe yakuma gyara kwanciyar sa.
A fusace Sadam yashiga kokarin kuma mai da kiran sai jin sa ya yi a kashe.
"Amma d'an ji da kan nan bai san da wa ma yake magana ba, zan nuna mashi ko wane ne ni!."
Inspector Nasir ya yi murmushi tare da bubbuga kafad'ar sa ya ce
"Yanzu ba wannan ne a gaban mu ba, damuwar mu ta farfad'o ta sami lafiya ne."
ya dubi nurse d'in ya ce
"Gidan sa nan kusa ne ba? taho muje ka raka ni."
Sadam ya ce
"Wai gurin sa zakaje shi zai zo da kafarsa har barrack ya same ni, zan punishment nashi,
mu d'au keta mu tafi wani asibitin."
kai Nasir ya girgiza yana murmushi ya ce
"D'an'sandan ke nan abokin kowa, zanje na d'auko shi, kasan kowa sarki ne a fannin aikin sa,
yanzu idan aka barmu da ita bamusan ya zamuyi da ita ba, saboda ba aikin mu bane,
a wannan fannin dole mu zamu bisa aikin sa ne,
yanzu idan mukace zamu d'agata a nan kafin mu isa wani asibitin ai zamu b'a lokaci, kuma tana bukatan taimakon gaggawa."
da sauri Inspector Nasir ya fita nurse d'in yabi bayan sa.