← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 52

Sashe 11

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka rayuwa yaci gaba da tafiya Feeryal nata dad'a kara wayo, ya yin da suffarta dake saka kokonto cikin zukatan duk wanda ya ganta ke dad'a karuwa.
zuwa yanzu Aunty ta saki zuciyar ta da Feeryal.
har ta yarda abaya wancan lokacin da take gane-ganen Feeryal tana wasu abubuwan da gaske gizo ne, da kuma sharrin shed'anun aljanu da suke son shafarta kamar yadda Daddy ya fad'a mata.
sosai ta dawo kula da d'iyarta.
tuni Feeryal ta kai na yaye aka yaye ta..

Kamar wasa rayuwa mai tafiya da sauri shekarun Feeryal hud'u ke nan, amma a zahiri idan ka ganta zaka iya kira mata shekaru biyar har da d'ori.
Aunty bata barinta fita ko nan da can,
iyakacin ta cikin side d'in da farfajiyar sa zuwa garden d'in cikin side d'in.
bata zuwa side d'in kowa a gidan, kamar yadda kowa ma baya zuwa nasu side d'in.
in banda Hajiya Safiyyah da kuma 'yarta Meimei sa'ar Feeryal ce,
sai dai ta d'an girme mata ita shekarunta shida ke nan,
amma kusan tsawon su d'aya,
sosai Feeryal ta saba da Meimei, Hajiya Safiyyah tana kawota suyi wasa da ita.

Ganin bakinta ya bud'e sosai da magana,
Daddy yace za'a sata a makarantar su Ameerah.

Ranar wata juma'a Daddy na zaune a parlour'n sa yana waya.
Mommy ta shigo parlour'n ta taras da shi na waya, ta zauna gefe tana saurarar abin da yake fad'a
"Ashirya mata duk abin da ya dace zuwa ranar Monday nake so ta fara zuwa makarantar, a kawo mata uniform da sauran abubuwan bukata gida ranar Lahadi,
Monday kuma ta fara zuwa."
yana sauke wayar Mommy ta bishi da kallon tambaya
"Alhaji wa kuma za'a canzawa makaranta, kar dai ace Ameerah sarkin rigima ce ta kuma tada buren sai an sauya mata wani makarantar?."
ta karashe maganar tana washe baki da jin dad'in fitinar d'iyar tata.
Daddy ya ce
"Ai naga alama Ameerah yanzu tana son makarantar nan, tun da najita shiru bata kuma tada borin a canza mata wani ba,
Feeryal ce za a kaita makarantar tasu."

Da mamaki ta ce "Feeryal kuma wacce Feeryal d'in?."
dan ita tagama mancewa da wata Feeryal a gidan ma, dan tun lokutan baya da suka tab'a tafiya saceta sukaga abin da yafi karfin su.
tun da suka gudu basu sake gigin kuma zuwa ba, a sannu kuma suka mance da batuntu, tun da ba ganin ta suke ba, bugu da kari kuma gargad'in da Daddy ya yi musu, kan duk wanda ya fad'awa hajiya abakin auren ta.
Daddy ya ce "Feeryal y'ar wajen Fad'imatu mana."
wani uban ashar Mommy ta mulmulo tare da buga kirji ta gwalalo ido waje
"Kutumar ubancan Alhaji dama aljanar nan tana gidan nan!? muna shakar iskar numfashi d'aya da ita?
wato Fatima b'oye aljanar nan taye,
ta b'oye bakar gamasheka tayi ta raino harta hab'aka tazamo muguwar dafi,
to wlh bata isa ba
dolen ta tabar gidan nan, dan wlh bazamu rayu da aljana ba,
wai kuma har kake batun sakata a makarantar su Ameera, wlh bazai sab'u ba, bazai yuwu a had'a mana ya'ya da aljana ba, taje can ta karaci tsiyarta."
"Ke Halima ina ruwan ki, idan an sakata a makarantar su Ameerar ke zaki biya kud'in ko me? ki cire bakin ki a lamarin yarinyar nan tun ranki bai b'aci ba, idan aljanar ce sai me ni na shirya taimakon ta."
zumbur ta mike tsaye har tana kumfar baki
"Wlh ba a isa a sakata makaranta d'aya da ya'yan mu ba,
Alhaji kafa fitar da mayyar aljanar nan a gidan na, idan kuma ba haka ba to mu zamu kwashe ya'yan mu mubar mata gidan,
dan bazamu zauna da mayyar aljana ba,
Fatima ta gama asirce ka takawo mayya gida ka runguma wane d'iyar cikin ka,
sabo da haka ka hana Hajiya dawowa kasar ma baki d'aya, to wlh asirinsu sai ya tonu,
babu abun da zai hana ni sanarwa hajiya komai,
dan wlh ina ji ina gani kam bazan zauna da mayyar aljanar ruwa ba!."

Daddy ya gyara zaman sa tare da d'aukar gilashin sa ya saka, ya mai da dubansa kan TV sannan ya ce
"Sai dai kubar gidan nan badai Feeryal ba kam, je ki sanar wa Hajiya daga nan kinsan sauran."
Fuuu tayi waje tana cigaba da zazzage buhun masifa
ba'a isa a had'a musu ya'yan su da aljana a makaranta d'aya ba.

Har ta isa side d'in ta bata fasa masifar ba,
ta kirawo Umma Karima ta sanar mata da abin da ke faruwa.
a bujajan Umma Karima ta taho side d'in Mommy
tun daga bakin kofar parlour ta ke fad'in
"Kar ki gayamin wannan zance Hajiya Halima, ya akayi mukayi bacci ne bamu farka da wuri ba,
Eh lallai Fatima tasan me tayi, wato sai da tabi kowa ta toshe masa baki, tasaka kowa baccin ido biyu ta yadda babu wan da zai kuma batu kan aljanar nan,
hahahaa wlh karya kike Fatima bokanki ya yi kad'an."
tawani saki makirin dariya takaraso cikin parlour'n ta hakimce kan kujera.

Da sauri Mommy ta ce
"Meye mafita Hajiya Karima, idan fa bamuyi da gaske ba, Hajiya Fatima zataga bayanmu."
"Akwai mafita amma bazamu sami ganin Mali ba sai nan da karshen wata sabo da sun shiga mitin natsawon wata guda,
sai dai muyi hakuri zuwa lokacin."
kai Mommy ta girgiza tana ciza yatsa.

Farida da Sumayya dake zaune can gefe suna karatu a littafan makarantar su,
Farida ta rike had'a tana wani yamutsa muska cike da iyayi da manyance kamar uwar mata ta ce
"Yanzu dama har yanzu yarinyar nan tana gurin Aunty? sai da Hajiya ta ce wa Daddy su mai da ita
cikin ruwan da suka d'auko ta shine suka ki, ai Hajiyar zata dawo."
ta karasa maganar cike da zallar manyance da rashin kwab'a irin na iyaya.
idan manya suna magana
sai yaro ya tsoma baki, ba a hanashi ahaka duk
suka gina ya'yan su.
babu kwab'a ko kad'an.
"Ai rannan da naje side d'in Aunty na ganta tagirma kamar Ameerah, har ta ce zata bini Aunty
ta ce ta zauna, kun ga in da tayi kamar Miesho
nacikin Film d'in Tigezam, har idon su iri d'aya
da gashinsu."
cewar Sumayya tana waro ido.

Harara Mommy ta banka mata ta ce
"Ai ke kam albasa batayi halin ruwa ba, uban me ya kaiki side d'in nasu,
ai dole tayi kama da Miesho kin tab'a ganin mai
kama da ita ko a kasashen su ne bare a kasar nan mai tsuffar aljanu, idan na sake ganin ki a side d'in
sai na ci ubanki,
me za'ayi da Fatima gayyar tsiya."

Ajeemal da yanzu shigowar sa ya b'ata fuska
"Mommy to ku ina ruwan ku da yarinyar nan, Daddy
shi yaji zai iya riketa imma aljanar ce meye matsalar ku, tun da Aunty ce ke rukon ta ba ku
ba."
"Dalla tafi can ka ba muta ne guri, me ka sani a rayuwar yau."
cewar Umma Karima.
Mommy ko ashar ta auna masa, ya girgiza kai yaja
kafarsa ya yi gaba.

Lanar Lahadi aka kawo wa Feeryal kayan makarantar
ta, ranar ba zama tun da aka gwada mata taki a cire har sai da Aunty ta lallab'a ta tayi bacci kafin a ka cire mata tana bacci bata sani ba.

Washegari ranar Monday da wuri Aunty tagama mata
shiri, tayi matukar kyau sosai cikin shigar uniform.
tagoya school bag d'in ta, sai tsalle take da murnar zata makaranta.

A can side d'in Mommy su Farida sun gama nasu shirin
suna zaune a dinning suna breakfast.
Mommy ta dube autarta Ameerah tashafa kanta tana fad'in
"Daddyn ku ya kafe sai da yasaka munafukar aljanar
nan a makarantar ku, nasan kuma karshe ajin ku
za'a kaita, kar ki kuskura kirika bari tana zama
kusa da ke, bare ta manna miki damuwa;
idan tamiki wargi kici uwarta da duka,
dan aljanu
tsoron duka ne da su, shegiyar yarinya mayyar aljana 'ya'yana sun fi karfin ki,
kuma kar wata ta raga mata acinku ba jinin ku bace
ita, babu abin da ya had'a ku da ita."
Farida da Sumayya suka girgiza kai alamun sunji gargad'in nata.

A b'angaren Umma karima kuwa
Harsu Bilkisu Saddika Rahama Nabila sun gama komai da komai suna shirin fita,
tun tashin su Umma Karima ke musu bitar tsiya har kawo yanzu da zasu fita,
ta dubi Nabila karamar su ta harare ta tana fad'in
"Ba an iya tab'aki ki bud'e baki haa ba, duk san da naji labarin aljanar can tayi miki kallon banza baki cire kwayar idanunta a hanun ki ba,
sai na ci kutumar uban ki da duka,
babu ragawa sakanin ku,
kurika yiwa shegiya dukar tsiya,
yar tsintuwa ce uban ku ba d'aya ba, ko ya mutu bata da gadon sa,
ita uwar kanzagin nata ma haka zata tashi a tutar babu, bata tab'a nishin haihuwa ba sai dai na kashi a shadda,
maza ku kama hanya bance ku ragarwa shegiya ba."

Aunty ta fito rike da Feeryal.
suna daf da fita bakin get d'in side d'in ta, ta ce
"Tsaya-tsaya y'anmatan Ammie, sa kafar ki ta dama kifara fita da shi, sannan kice tawakkaltu'alallah walahaula'wala kuwwata illa billah, sai ki fita da kafar da ma."
baki ta wace har da d'an tsallenta.
sannan ta ce
"To Ammie,tawalkaltu alallah walahaula wala kuwwata illa billaaaah."
murumushi Aunty tayi, batayi mamakin yadda ta iya addu'ar ba, dan ire-iren addu'o'in nan tana koya mata su sosai.
ta shafa kanta tana fad'in
"Yauwa y'anmata Ammie, to ban da kwad'ayi, ban da fad'a, ayi karatu sosai."
kai ta gyad'a tana murmushi itama, suka fito.
Chapter 11 · 0% Book details