Sashe 49
Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Miemie ta dad'a b'ata rai ta ce
"Haba Hajiya ya zaki ce mata mayya kuma aljana, yanzu idan wani ya tsangwame mu haka kema fa bazakiji dad'i ba."
"To uwar ta ki karb'a mata, kefa Miemie tun da na datsa ayar tambaya a kanki, dan naga alama yarinyar nan bata barki banza ba,
kar na sake ganin ki da ita, kuma zanje na amso magani a soma miki dan da gani turen aljanu ta miki."
Miemie ta tura baki tana kunkune ta nufi kofar fita tana cewa
"Ni ba wanda ya isa ya rabani da FEERYAL, ba kuma maganin da zanyi in kin karb'o maganin sai kiyi amfani da kayanki."
tayi waje abin ta ta bar Hajiya tana ta masifa.
Bilkisu Saddiqa Rahama da Siyama kanwar Umma Karima da yanzu ta dawo gurin Umma Karima da zama,
suka fito daga sashin Umma karima.
Nabila da tayi fitowar karshe idanunta ya sauka kan FEERYAL da ke tsaye a bakin get d'in Hajiya.
da hannu ta nuna musu ita tana fad'in
"Yauwa kun ganta can ga FEERYAL d'in can."
duk suka maida dubansu gareta.
Saddiqa ta bud'e murya tare da yafaro ta da hannu ta ce
"Ke FEERYAL zo nan."
A hankali ta ke d'aga kafarta cikin yanayin ta na sanyi har ta iso inda suke.
dukkanin su suka bita da kallon tsaf,
Siyama ta yamutsa fuska tana fad'in
"FEERYAL d'in ke nan?."
Bilkisu ta ce
"Wai ita ce, bamu sani ba dai ko Aunty ta kuma d'auko wata ce tace ita ce ta da d'in data tsinto cikin ruwa,
dan lokacin da aka koreta a gidan nan tana ficiciya."
Rahama ta ce
"Ke kifa daina mana yawo a gida idan kuma kika ki dukan tsiya zaki ci, dan sau uku ke nan nake hango ki kina kai kawo cikin gidan nan."
Nabila tace
"Ah to gaya mata dai dan nan gidan ubanmu ne agola bata isa tayi abin da ta so ba,
ke daga yau ma duk abin da zakiyi sai kin nimi izin mu, har idan kina so ayi miki alfarmar zama na d'an wani lokaci."
Siyama ta bita da kallon banza tana wani yamutsa baki ta ce
"To dai kinji abin da masu gida suka fad'a, sai kibi a hankali domin ki cigaba da zaman alfarma, in ba haka ba kuma a koma in da aka fito."
Rahama ta ce
"Ai kuwa dama zaman alfarma take dan Hajiya ta fad'awa Umma Daddy ne ya nima mata alfarman zama dai-dai, kunsan 'yan kidnapping d'in nan wannan mai tawagar d'aukar amaryar nan sun d'auke ta da kyar aka kwato ta,
bayan ya gama bidirin sa da ita."
dariya suka kwashe da shi Siyama ta ce
"Kice ashe dai fanko ce tsaye a nan, kyalkyali daga waje ciki fanko."
FEERYAL na tsaye bata ce da su kala ba,
gaba d'aya tsoro ya rufe ta bata saba ganin haka ba,
tun bayan da ta sami 'yancin barinta gidan rabon da ayi mata irin haka.
Miemie da ta fito daga sashin Hajiya ta hango ta can tsaye dasu Bilkisu,
kugu ta rike tana kallon su sai magana suke suna nuna FEERYAL da yatsa.
itako tayi kasa da kai kamar mai d'aukar wa'azi,
a kufule ta nufo gurin su fuska d'aure ta ce
"Ke kuma FEERYAL me kike a nan? na fito ina ta duba ki a she kina tsaye anan, to muje."
Bilkisu ta ce
"Mu muka kirata muna mata kashedi ne, kar ta sake ta rika mana yawo a gida."
Miemie ta dube ta shekeke ta ce
"Kuma dai Aunty Bilkisu meye wani abin kashedi dan anyi ya wo a cikin gida,
waje ke nan kuke so muje murika yawo."
Rahama ta ce
"Bawai ke ba da ita muke."
"Har da ni mana Aunty Rahama tun da tare kuke ganin mu, idan bamuyi yawo a cikin gida ba waje kuke so mufita."
Siyama ta ce
"Ke Miemie ana gaya miki ba ke ba da ita ake."
"Dakata Siyama ba da ke nake ba da su nake, ban kira sunan ki ba,
Aunty Bilkisu Aunty Rahama Saddiqa Nabila,
ina ga acikin mu da ni da ku duk babu mai hurumin ikon hana wani yawo cikin gida, tun da babu wacce ta gina gidan a cikin mu,
Daddy ke da ikon yanke hukunci ba mu ba."
"Ke karkice zaki min rashin kunya dan tuntuni nake ganin take-taken ki."
Siyama ta fad'a tana nuna Miemie da yatsa.
Miemie ta wani dalla mata harara taja tsaki tare da jan hannun FEERYAL tana cewa
"Dalla zo mu tafi, sai naga wanda ya isa ya hanaki yawo,
ai agololin suna da yawa a gidan idan sauran suka daina ke ma zaki daina."
Sai da sukayi nisa da su Miemie ta harare FEERYAL tana fad'in
"Kin wani tsaya suna gaggaya miki magana baki maida musu amsa ba, in fad'a miki a gidan nan idan bakada baki anrika cin tuwo a kanka ke nan,
garama ki koya kiyi baki,
duk ba mutunci suke da shi ba, shi yasa nima bana ganin su da mutunci, Bilkisu da Rahamar ma albarkacin Ammah suka ci nake had'a su nan su da Aunty, amma ba dun haka ba duk da sunan su zan kira su, tun da basu rike girman su ba,
duk sun turewa shekara 27 ko uwar me suke d'auka a gidan suka kasa aure oho,
ita kuma wannan shegiyar Siyamar ba karamin haushi take bani ba,
an kasa auruwa a Kano an dawo Lagos ko za'a sami mashinshini,
wai a haka budurwace da kike ganin ta nan kamar bazawara,
da gani wannan ta kai shekaru arba'in
kanwar Umma Karima ce da bushasshen jiki ko ina a bushe ba soka."
FEERYAL dai murmushi tayi bata ce ko mai ba,
Miemie ko bata fasa mitar ba har suka shige sashin Aunty.........!
Mommyn Twins ce
🌺 *FEERYAL* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ?*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇ðŸ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿�22
Suna shiga parkour suka tadda Aunty zaune,
Feeryal ta karaso ta kwanta kan kujerar da Aunty ke zaune tayi pillow da cinyar.
Aunty ta zame d'ankwalin kanta tana fad'in
"Me kitso anjima tana zuwa."
fuska ta kwab'e ta ce
"Ammie gyaran gashi fa zamuje da Miemie jibi."
"Wai haka Miemie? ko duk gudun kitson ne haka."
cewar Aunty tana duban ta.
Miemie ta gyad'a kai tana dariya.
Feeryal ta dubi Aunty ta marairaice fuska da fad'in
"Ammie ba kince za'a aske gashin ba."
Aunty ta dunguri kanta tana fad'in
"Baki da kaine, ama bar gyaran gashin a gyare yake,
maza akitsa kyan yau,
in anyi tsifa sai aje a gyara gashin."
birmima ta shiga yi a jikinta tana bubbuga kafa kan kujera Miemie sai dariya take mata.
Mai kitso ta zo da yamma, tana ganin gashin nata ta ce wlh bazata iya kitsa shi ba dan ya yi yawa.
Aunty ta ce ta gwada dai da kyar aka tuttuka akayi biyu,
karshe tsefe biyun akayi ta tafi,
Feeryal ko sai murna take dama bata son kitson har da hawaye da aka kama kan ana kitsawa...
Umma Karima ce ta fito tana gyara mayafin kan ta,
da alama dai shirin fita tayi dan ga jaka rike a hannunta.
a parlour ta tadda 'ya'yan nata duka kowa na sha'anin gabansa.
Siyama ta mike tana fad'in
"Aunty Karima fita zakiyi ne?."
"Eh fitan gaggawa ce ta taso min bazan jima ba zan dawo, wai ina Nabila ce?."
bata rufa baki ba Nabila ta shigo tana kananun magana.
"Ke kuma da wa kike?."
uwar tata ta fad'a tana duban ta.
ta ce
"Ni da wancan direban naki Sule mana Umma, d'an rainin wayo wai kullum ya ganni sai jira yake ni na fara gaishe shi har na wuce bazai haishe ni ba,
shine yanzu nazo zan wuce har da ce min wai ban gaishe shi ba,
kajimin fa d'an rainin wayo,
ni da gidan ubana yazo cin arziki yace ni zan rika gaishe shi ba shi zai gaishe ni ba,
kaf ma'aikatan gidan nan su ke gaishe mu ba mu muke gaishe su ba,
hatta Baba Ilu mai baiwa fulawa ruwa shi yake gaishe mu ba mu muke gaishe shi ba,
na gaya masa na rantse watarana sai na d'auke shi da mari,
kuma zan gayawa Daddy sai ya bar gidan nan,
ni ban san me yasa kiko son tukin wannan kazamin buzun ba ma Umma, to wlh
ya yi a bakin aikin sa dan wlh sai na sa Daddy ya kore shi."