Sashe 48
Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jikin FEERYAL ya yi sanyi matuka.
Miemie ta bi bayan su da harara tana fad'in
"Ai ke kam Ameerah kin shiga uku sai ki hanata zama ai tun da ke kika gina gidan,
ku kuma kun bita kamar wata uwar ku, dalla rabu da su zo mu tafi FEERYAL suyi abinda zasuyi."
ta jata suka nufi sashin Ammah tana ce mata
"Karki wani damu da su."
cikin sanyin murya FEERYAL ta ce
"Hum Ameerah ke nan har yanzu dai bata sauya ba."
"Ai bazata sauya ba haka zata mutu da halinta,
kinga Sumayya tana da sanyin hali ita dai kawai zugi ke mata tasiri,
mance da su dalla."
ta d'auko mata wata hirar har suka wuce sashin Ammah.
Ammah na ganin ta ta rungume ta tana fad'in
"Oyoyo FEERYAL ke ce haka,
Allah sarki ya jiki ya abinda ya faru?."
FEERYAL tayi mirmushi tana gaisheta.
Miemie ta jata sukayi cikin d'akin ta bayan su. gaisa da Ammah.
hira sosai Miemie ke janta da shi ita dai murmushi sai dariya take binta da shi dan bata iya dogon hira irin haka ba.
sun jima sosai har wajen azahar sai da FEERYAL tace zata koma tayi wanka.
Miemie ta ce
"Kiyi wankan a toilet d'in na sai kije ki sa kaya."
ido FEERYAL ta waro ta ce
"To kaya fa bazan iya maida na jikina ba."
"Sai kisa nawa ba ga nawa ba, ko an ce miki kin fini kiba ne."
"Miemie muje dai ki rakani zan canza pad wajen awa uku yana jikina."
"To ai ina da shi shiga kiyi wanka bari na d'auko miki."
dole Miemie tasa ta shiga bathroom d'in ta tayi wanka ta bata pad da sabon pant ta saka,
ta fito ta samu ta ciro mata doguwar rigar abaya,
zata tafi da nata kayan Miemie ta ce ta barshi anan.
sannan suka fito ta rako ta.
Suna fita can suka hango su Ajeemal Faisal Zaraddin Shamsuddin, zasu shige side d'in su.
Miemie ta d'aga murya tana fad'in
"Kai-kai ku tsaya ku tsaya."
ta janyo hannun FEERYAL da sauri suka karo gurin su.
Faisal ya harare ta yana cewa
"Ke mu sa'annin ki ne da kike mana irin wannan kiran?."
Shamsuddin ya kai mata bugu a baki ta yi saurin kaucewa.
tana cewa "Wayyo Allah baki na, to ku tsaya kuji mana."
ya ce "Waye sa'anki."
Ajeemal ya ce "Ku kyale ta, mene ne Miemie?."
baki ta turo ta ce
"To ai bana so na kira sunan ku ne taji game d'in ya rushe,
yauwa kutsaya-kutsaya kuji in kun canka waye wannan?."
ta nuna FEERYAL sannan ta ce
"Ke ma in kinci su waye wad'annan fad'o min sunan su."
tayi maganar tana dariya da tafa hannu.
duk suka bi FEERYAL da kallo Zaraddin da shi dama ya kasa magana tun d'azu idanunsa yana kan ta gaba d'aya yawun bakin sa ya gama tsinkewa.
Ajeemal da ke ta juya kamannin nata cikin kwakwalwarsa, ya yi saurin janye idanunsa daga kallonta, jin yadda gaba d'aya kasala ke kokarin shigarsa.
Faisal kuwa cewa ya yi
"Nasanta mana balarabiya ce ai mun sani duka."
dariya ta kwashe da shi ta nuna Zaraddin da Shamsuddin da Ajeemal ta ce
"Kuma baku gane ko wace ce ba, to ke suwaye ne su."
tayi maganar tana kallon FEERYAL.
murmushi ta sake wanda ya sami nasar bayyan hushiryar da ke tsakiyar kyakwawan jerarrun hakorar ta,
yayin da kumatun ta ya lotsa dimples d'in ta ya bayyan.
ta kai yatsarta baki tana bin ko wannen su da kallo.
wani irin had'iye yawu Zaraddin ya yi yawani lumshe ido tare da jan numfashi a fili.
Dariya Miemie tayi ta ce
"Wai dukan ku baku gane ta ba, kema baki gane su ba? yee naci wina."
tayi maganar tana tsalle a tsakiyar su.
Ajeemal ya ce
"Ke Miemie wani irin shiririta ne wannan."
"Ya Ajeemal ku bani gari kawai FEERYAL ce fa,
FEERYAL baki gane Ya Ajeemal Ya Shamsuddin Ya Zaraddin Ya Faisal ba."
ido ta waro tana murmushi da bin ko wannen su da kallo, sai da ta fad'a sannan kamannin nasu na tun da yake zuwar mata ido.
suma d'in mamaki duk suka cika da shi,
wai FEERYAL ce ta zamo haka.
Zaraddin da yakuma hadiye miyau ya furta
"Wow! she is cute completely."
Shamsuddi da Faisal suka had'a baki wajen fad'in
"Haka kika girma FEERYAL."
nan ma murmushi ta bisu da shi batayi magana ba.
Ajeemal ne ya ce
"FEERYAL ya abin da ya faru ina tayaki jaje, ya karatu kuma,
au na mance wani rana Aunty take sanar min graduation naki, kinyi kokari fa kinfi su Miemie."
"Haba Ya Ajeemal sai kasa tayi tunanin bamuyi ba muma, tun yaushe mukayiwa secondary bye-bye, mun barwa yara."
hararar ta Faisal ya yi ya ce
"Wuce ki bar nan ke d'in mece ce."
hannun FEERYAL ta ja suka bar gurin da sauri tana dariya dan tasan zuwa anjima zata sami tsarabar mari.
Zaraddin yabi bayanta da kallo yana wani matse ido da latsar lips d'in sa.
Ajeemal ya d'an harare shi dan ya lura da yanayin da ya shiga tun d'azu, ya yi tsaki yana girgiza kai ya yi gaba abin sa suka biyo bayan sa.
Kan ka ce me gidan ya d'auki labarin FEERYAL ta dawo,
a bujajan Umma Karima ta d'auko kafa tayi sashin Mommy.
tun kafin ta zauna take cewa
"Hajiya Halima wai da gaske ne batunnan ko maganar yarannan ne kawai?."
"Ni ma yanzun nan su Ameerah suke sanar min kin san bazasuyi karya ba."
Umma Karima ta zauna tana fad'in
"Tabd'i jam wata sabuwa inji d'an caca!
aljana mayya annobar ta kuma dawo mana gidan."
ta saki dariya
"Hahaha lallai Hajiya Fatiya ba karamar 'yar wasa bace, sai da ta bari muka sakankance sannan ta shammace mu,
ta dawo da ita bayan ta hab'aka dafinta yagama kwari ta inda duk wanda ta kaimai sara zaiyi masa mummunar illa,
Fatima Fatima Fatima muzuba mugani waye zai cinye wasan!."
Mommy ta ce
"Ham tun da suka kawo min batun nan narasa a bin yi, yanzu ya kike ganin za'ayi Hajiya Karima."
"Yanzu ne za'a yi mai gaba d'aya ai ta farkar da mu daga nannauyar baccin da muke."
cewar Umma Karima tana girgiza kai.
Ameerah dake zaune sai cika take tana batsewa,
tun dataga FEERYAL, bakinciki kamar ya kasheta,
bata kaunar ganin wacce ta fita bare kuma a yabeta a gabanta.
ta ce
"Mommy amma dai zata bar gidan nan ko, dan wlh bazamu zauna da ita ba,
ta ya za'ayi ne ma kawayen mu suzo su ganta,
ina bazai yuwuba,
nifa duk yadda za'ayi Mommy tabar gidan nan."
"Ai barin gida ma yazama dole kwantar da hankalin ki d'iyar masu gida,
har wacce ta kawo tan ma wannan karon tare zasu bar gidan."
cewar Umma Karima tana gyara zaman ta.
Sumayya ta ce
"Wlh bakuga yadda ta girma ta zamo wata tsaleliyar budurwa ba,
ko gane ta bamuyi ba, ni na d'auka ma bakuwar balarabiya mukayi,
sai da Miemie ta ce mana wai ita ce,
wlh tafi da kyau gaskiya tana da kyau sosai kamar ita tayi kanta."
Mommy da ke ta aika mata harara tun da ta fara maganar ta ce
"Dalla rufa mana baki, kusheta kike ko yabon ta, ni fa watarana tantama nake akan ki dan naga kamar halinki na kamancece niya dana Ajeemal duk zan ci ubanku ai marasa ziciya,
wad'annan badun lokacin da na haifeku a take aka d'ago aka nuna min kuba da sai nace canza min ku a kayi."
Ameerah tabi Sumayya da harara tana jan tsaki ta mike tayi bedroom d'insu.
gaban mirror ta tsaya tana karewa kanta kallo.
sai kuma ta juya ta koma bakin gado ta zauna tana fad'in
"Aikin banza banga abin da ta fini da shi bama."
Yau kwanan FEERYAL uku a gidan.
kullum suna tare da Miemie ko a sashin Aunty ko a sashin su Miemie'n.
ko yanzu ma sun fito ne daga side d'in su Miemie zata rakata side d'insu.
Ammah ce ta kwallawa Miemie kira ta koma ciki,
kula mai d'auke da dambu ta mika mata ta ce
"Mikawa Hajiya wannan sai ku wuce."
ta amsa tana fad'in
"Hajiya mayyar dambu sai ya shake makogwaron masifar nan mu huta,
wata rana da kaina zan mata mara kayan had'e na kai mata taci ta shake."
"A bakin ki akaji ba a baki na ba, ke da Abbieh'n ku idan ya jiki."
Ammah ta fad'a tana juyawa ciki.
Miemie tayi waje tana cewa
"Allah sai na yi mata sai dai Abbieh yayi min masifa ko ya bige ni, mata kullum masifarta karuwa yake takusa mutuwa madadin ta rusuna amma sai gaba abin ta yake."
ta karaso in da FEERYAL ta ke ta ce
"Taho muje ki rakani na mikawa Hajiya dambun nan sai mu wuce."
FEERYAL tad'an waro ido ta ce
"Muje dai na jira ki a bakin get d'in ta."
"Dalla matsoraciya zo muje me zata yi miki, ai yanzu ta saduda, tun da ta amsawa Daddy ki zauna."
FEERYAL dai shiru tayi har suka karasa sashin Hajiya.
dan Hajiya tana daga cikin abubuwan da suka ki gogewa cikin kwakwalwarta na tun yaranta.
A parkour suka tadda Hajiya FEERYAL ta karaso a hankali kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.
Miemie nayiwa Hajiyar magana ita hankalin ta na kan FEERYAL da ta d'an rusina tana fad'in
"Ina yini Hajiya."
Hajiya ta ce
"Ke Miemie wannan ba aljanar yarin yar nan bace?."
Miemie ta b'ata rai sannan ta ce
"FEERYAL sunan ta."
"Da gani ai ba sai an fad'a ba, dan ina ido biyu da ita naji tsikar jikina ya tashi,
haba kyan har ya kazanta hankali bazai d'auka ba,
ke tashi min a kai fita waje! kar na sake ganin ki cikin sashin nan,
ki zauna can sashin Fatima kafin a gama binciken ki koma can in da akayi gayyarki ba gidan d'ana ba, mayya aljana mai zubin aljanun ruwa."
Da sauri FEERYAL ta juya har tana had'awa da sassarfa tayi waje.
sai da tafi wajen get d'in sashin kafin ta tsaya.