Sashe 6
Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dakatar da ita yakuma yi ta hanyar kuma d'aga mata hanu ya ce
"Ya isa, ai na fad'a muku duk sanda kuka shirya yin girki da hannunku zan ci."
"Haba Alhaji me zai sa mu yin girki bayan ga masu aiki har rai nawa, babu kalar girkin da basu iya ba,
Allah ya bamu hutu sai kuma mu kasa hutawar,
a ce duk wannan daular da muke ciki mukasa hutar da rayuwar mu sai mun bautatu,
haba Alhaji ai kai yakamata ma ka ce mu huta, ma'aikata sucigaba da hidimta mana."
Kai Daddy ya girgiza kana ya ce
"Fad'imatu duk da kaancewar ta d'iyar masu kud'i; bata d'auki girman kai ta sawa ranta ba, da kanta take girki dan naci abinci cikin kwanciyar hankali, da sauran aikace-aikacen da ya kamata, dan haka bakuda bakin da zaku dakatar dani daga cin abincin ta,
fad'i abin da yake tafe da ke, in kuma wannan ce ta kawo ki to ki koma sashin ki bana son damuwa."
"Eh ai basai kayi mana gori ba, mu y'ay'an talakawan ita 'yar masu kud'i, a haka kuma muka fita ba,
idan kud'i na iya yi maka komai taje ta sayi haihuwa tasakawa cikinta tayi nakuda da kanta ta haifa mana,
bata soma bin 'ya'yan aljanu tana d'ibowa tana kawo mana su gida ba,
kai kuma ka amince mata mu rayu da aljana cikin gida d'aya, daga nan duk ta shige jikin ya'yan mu."
"Karima ya ishe ki haka fita kitafi sashin ki nace!."
Umma Karima ta juya tana cigaba da mita tafice.
tsaki Daddy yaja tare da cigaba da abun da yake cikin computer sa.
Washegari da misalin karfe 6, su Hajiya ne zaune a parlour anata fita da kayan su zuwa mota.
Mommy Umma Karima Hajiya Safiyya matar Alhaji Sulaiman wato Abbieh da kuma Hajiya Nafisat matar Alhaji Tukur Dad ke nan.
da ya'yan su duk suna parlour'n.
Hajiya Bishira tun a daren jiya ta iso kamar yadda Daddy ya fad'a.
Mommy ta nisa ganin saura kad'an a gama fita da kayan su ta ce "To Hajiya in an tafi kuma sai yaushe?
yauwa Hajiya dan Allah ki kumakiyiwa Alhaji magana kafin ki tafi,
har yanzu fa baya cin abincin mu sai na wancan matar Fatima, ma'aikata masu tsafta muke da su amma ya ce wai bazaici abincin mu ba,
sai dai yarika shiga hakkinmu ran girkin mu ma ita ke masa girki."
Hajiya ta d'au gilashin ta ta saka tana fad'in
"Kai sai dai fa kuyi hakuri dan abinshin gado ne dan asali ya samo,
da ubansa ma baya cin abincin mai aiki, idan ina so yaci kuwa dole sai na girka masa da kaina, shima kuma Abubakar d'in a haka ya taso in har me aikice ta dafa to bazaici ba sai in ni na girka da kaina kafin yaci,
bai iya cin abincin masu aiki bane tuntuni,
in kun zab'i hutu kawai ku huta ku barta ta cigaba da bauta."
Kai Hajiya Safiyya ta girgiza tana mai mamakin hali irin na Mommy da Umma Karima,
Hajiya Nafisat kuwa cewa tayi
"To me akayi ke nan kana da halin hutu baka hutan ba."
Shigowar su Daddy ne yasa Umma Karima da ta budi baki zatai magana yin gum da bakinta.
Daddy ya ce "Hajiya taso maza saura awa guda jirgin ku ya tashi."
duk suka mike sukayi waje gurin mota.
Hajiya na kokari shiga mota Aunty ta karaso gurin,
tad'an rusuna tare da fad'in
"Ina kwana Hajiya, Allah ya tsare hanya ga wannan ki samu na d'an tab'awa a jirgi."
Hajiya ta karb'i laidar da take mika mata ta bud'e, wani roba ne mai d'an girma cikin laidar, ta bud'e robar lafiyayyen dambun naman kaza ce dayaji kayan had'i yana fidda wani irin sihirtaccen kamshi.
Hajiya tahad'iye miyau mukutt, ba yabo ba fallasa ta wage baki tana fad'in
"Lafiya lau amin amin to angode."
"Cusa kai ba kwari niman gindin zama."
Aunty tajiyo muryar Mommy dake tsaye a bayanta, bata kula ta ba, yi tayi kamar ma bata jita ba.
tamasa in da Hajiya Safiyya take suka shiga gaisawa, Hajiya Nafisat kam 'yar fatin su Mommy ce ko kallo bata isheta ba.
Motar su Hajiya na tashi ta juya ta wuce sashin ta...
Yau ya kama kwanan Daddy hud'u a side in sa, yau ne zai koma gurin Aunty.
lafiyayyun girki kala-kala ta shirya masa, bakajin komai sai tashin daddad'an kamshin turare na musamman ke tashi a side in.
Aunty tagama shirya tarb'ar mijinta.
Al'adar ta ne a duk san da zai dawo gurin ta, da daddre kafin yatafi side d'in ta sai tazo ta gyara masa sashinsa, dan basa gyarashi haka kowa zata gama zamanta ta tafi, tun da ya ce baya son me'aiki ta gyara masa sashinsa, suka gwammace su barshi haka, dan suma nasu sashin masu aiki ne suke gyara musu.
duk da sashinta yake zuwa ya tare idan kwanan ta ya zago,
amma sai ta taho ta gyara masa side d'in sa idan yana d'akinta.
Tana saka da gyaran part d'in nasa da ya yi datti tamkar ba mata bane sukayi rayuwa a ciki, tsawon kwanaki hud'u.
Feeryal na kwance a kan kujerar parlour'n Daddy Aunty na goge-gogen parlour'n.
Mommy da Umma Karima suka shigo, kallon banza sukabi ta da shi.
ko in da suke ma bata kalla ba in da sabo ta saba.
idon Mommy ne ya sauka kan Feeryal da ke kwance kan kujera.
ido ta gwalalo ta buga kirji tare da fad'in
"Me zan gani haka anan aljana a parlou'n Alhaji!."
Umma Karima ta shiga tafa hannu tana fad'in
"Dama ashe baki mayar da ita ba sai da kikaga Hajiya ta tafi kika fito da ita,
ai kuwa babu abinda zai hana Hajiya bataji labarin nan."
"Duk matar da tayi gigin kiran Hajiya a kan maganar nan to a bakin aurenta!."
Suka jiyo muryar Daddy dake fitowa daga bedroom d'in sa.
"Kasan me kake fad'a kuwa Alhaji? akan wata banza aljana tsintacciyar cikin ruwa kake mana barazana da auren mu."
Mommy tayi maganar tana nuna Feeryal.
Umma Karima ta karb'i zancen da fad'in
"Eh ba laifin ka bane shi dama aljani da makiri babu ta inda baya b'ullowa da salonsa, muje Hajiya Halima amma dole za'a yi zama dan bazamu yarda ba wlh."
taja hannu Mommy suka fice sunata surfa bala'i
Da sauri Aunty ta dubi Daddy ta ce "Daddy ya zaka ce haka."
"Dukkanin su na san halin su idan ba haka nayi musu ba to ko shakka babu sai sun kira Hajiya da zancen, tanan ne kad'ai zai sa su hakura da kiran nata."
kai Aunty ta jinjina.
Daddy ya isa ya d'auki Feeryal dake ta baccin ta ya sakata a kafad'a, kana ya dubi Aunty ya ce "Muje ko."
nan suka fita suka nufi part in Aunty'n.
Waiwaye adon tafiya shin wane ne Alhaji Abubakar Fiya? kubiyo ni dan jin wane ne shi.
Alhaji Shitu Fiya, mahaifi ga Alhaji Abubakar Fiya haifaffen d'an jahar plateau state ne awani gari da ake kira da Yelwan Shandam,
Alhaji Shitu Fiya shahararren manomi ne wanda yake noma gonaki sama da hamsin a ciki da wajen Yelwan Shandam.
yana da mata d'aya da ya'ya biyu Abubakar da kuma Sulaiman.
yana da manya-manyan gonaki da girman su yakai girma, a kalla sama da guda hamsin, yana noma nau'ikan abubuwan da akafi amfani da su sosai a kasarmu.
Auduga, Shinkafa, Masara, Gero, Dawa, Maiwa, Rid'i, Agushi Gyad'a, farar Wake, Waken soya, Doya, Dankali, na hausa da kuma na surawa Rogo. da dai sauran nau'o'in kayan masarufi nayau da kullum.
ba a iya noman damina ya tsaya ba har da noman rani.
idan amfaninsa tayi bayan ya cire zakka.
zai aje wanda gida zai ci na tsawon shekara, kana ya cire wanda zai raba kyauta wa danginsa da y'an garinsa, san nan a kai sauran kasuwa.
Cikin kankanin lokaci yazamo shahararren mai kud'in da babu kamarsa a yankin.
a lokacin yakara iyali matansa suka zamo biyu, in da aka kuma samin karuwa bayan d'an wani lokaci amarya ta haifo d'anta na miji yaci suna Tukur.
Dukiyar Alhaji Shitu Fiya sai dad'a hab'aka take tamkar kullum dare ninka masa ake.
ya yi shaharar da kaf fad'in kasar nan ansan da zamansa a wannan gari na Yelwan Shandam.
dan yanzu manya-manyan y'an kasuwa ne suke shigowa cikin garin Yelwa suke sayan kayansa suna fita dashi zuwa jahohin kasar nan.
Amaryar Alhaji Shitu wato Luba batayi tsawon rayuwa ba, ta koma ga mahaliccin ta ,
tare da tsohon ciki na biyu a jikin ta, lokacin d'anta Tukur yana da shekaru uku.
nan fa mutane masu fama da cutar gulma suka shiga kai kawo suna yad'a jita-jita, aka d'aura alhakin mutuwar ta kan kishiyarta, wai ita ta kasheta dan ta zauna cikin daula ita kad'ai, dama da kyar ta bari akayi auren.
nan fa dangin Luba suka rungume zancen a kirjinsu suka yarda kan cewa ita ta kashe musu 'yar'uwar su, dan yanzu taga dukiyarsa ya ninka na da.
suka d'auki karar tsana suka sakawa uwargidan Alhaji Shiru, suka masa sai dai a basu Tukar kar shima ta kashe shi.
Alhaji Shitu Fiya bai yarda ya basu shi ba, ya ce yana da ransa da rufin asirin da Allah ya yi masa d'ansa bazai je agolanci wani gida ba.
Dayaki basu shi sai suka shiga zuwa suna d'aukarsa yana wuni a gurin su.
lokacin da yakara wayo kuma yashiga zuwa da kansa,
duk san da ya je, haka zasu zaunar da shi suna tambayarsa, me matar ubansa take masa, duk abinda ta bashi idan bai yarda da shi ba kada ya ci dan ita ta kashe masa mahaifiyarsa.
da ire-iren wad'annan abubuwan suka rika cusa masa ra'ayi suna dad'a masa hud'uba kan cewa,
ita abokiyar gabansa ce dan ita ta kashe mamarsa kada ya yarda da ita, da kuma ya'yan ta.
a lokacin Hanne wato uwargidan Alhaji Shitu takuma haihuwan 'ya mace taci suna Bishira.
ai kuwa gari yakuma d'aukawa dama ta kasheta ne dan ta tara ya'ya tasami gado.
Hannatu ta toshe kunnuwanta da jifan da magauta suke mata, baisa tayi wasi da rukon d'an mijinta ba, bata tab'a nuna masa bambanci sakanin sa da ya'yan da ta haifa ba.