Sashe 5
Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai ya girgiza sannan ya ce
"Kiyi hakuri Hajiya shifa haihuwa na Allah ne kada muja da ikon Allah."
"To jamin aya tun kan a haifeka nasan wannan."
kai ya kuma girgizawa kana ya ce
"Dama Hajiya nazo ne na sanar miki zaki tafi umura ke da Bishira, daga nan zaku kuwuce Egypt kuga likitan idon ki, gobe da karfe 7 na safe jirkin ku zai tashi,
nasanarwa Bishira zata taho da daddare gobe sai ku wuce."
Hajiya Bishira kanwarsu Daddy ce autar Hajiya ke nan, tana zaune a gidan gadon 'ya'yan ta, mijin ta Allah yamasa rasuwa shekara d'aya daya wuce ya barta da yara biyu,
mace da na miji.
Baki Hajiya ta washe "Kai dama idon nan ya dame ni da kaikayi yanzo ko har ruwa yake idan ya fara kaikayin nan,
ko d'azu sai da nayi ta sosashi kafin naji dad'i."
"Hajiya shifa ido baya son hanu bakiji abin da likita ya fad'a miki ba, idan fa kika matsa da sosashi za'a sami matsala, ana sammanin ya iya rufewa ma."
da sauri ta ce
"A'ah a'ah ai kad'an na sosa ba da yawa ba,
kuma ina sa magani kullum,
ido na bazai makanta ba in Allah yaso, ni dama can ganin likitan muka fara zuwa kafin muje saudin, ai likitocin tacan sunfi kwarewa zasu bani maganin da zai warke da wuri, kai wannan ciwo Allah yaraba bawa da shi."
Gaba d'aya Hajiya ta rud'e, ba karamin razana take a duk sanda taji anyi mata zancen idonta zai iya rufewa ta makanta ta daina gani ba.
tana matukar taoron jin idonta zai iya rufewa bata kaunar makanta a rayuwar ta.
cike da fargaba ta dubi Daddy ta ce
"Amma dai zan warke bazan makanta ba ko!?."
kai Daddy ya gyad'a ya ce
"Insha'allahu zaki warke Hajiya babu abin da zai sami idanunki, amma dai kirika kiyaye wa ki rage sosa idon."
"To-to ai insha'allahu ma na daina da zarar naji kaikayin zan saka masa magani."
Kira ta kwalawa Kulu mai aikin ta
"Ke Kulu d'auko min maganin idon nan nasaka."
"Hajiya a ka'idance ake saka maganin ciwon ido ba ko da wani lokaci ba."
"Ai dai Abubakar yau ma ban saka ba ko sau d'aya, barni kawai nasaka yanzu."
kai ya girgiza ita da ta ce, d'azu ta saka da idon ya dame ta da kaikayi yanzu kuma ta ce bata sakaba, Hajiya ke nan ba'a kaunar abin da zai tab'a lafiyar jiki.
Ya mike yana fad'in
"To Allah ya sauwaka sai ayi miki shiri da wuri, zaku tafi da Kulu dan ku sami mai yi muku d'an wasu aikace-aikacen."
Hajiya kam gaba d'aya hankalin ta ya koma kan maganin da take ta afkawa idon ta, har Daddy ya fita.
Aunty na zaune tana shayar da Feeryal bayan tayi mata wankan yamma, kiran Daddy yashigo wayarta.
da sallama ta d'aga kiran; daga cijin wayar Daddy ya ce
"Ammien Feeryal ba'a bani abincin rana ba har dare ya soma yi."
kai ta dafe tare da fad'in
"Ya subhanallah ayi min afuwa gani nan zuwa insha'allah."
ta sauke wayar ta mike da sauri tare da gyara rukon Feeryal a kafad'ar ta, ta nufi kichin cikin hanzari.
Baba Rabi ta tarar tana ta goge-gogen kichin, Baba Rabi na ganin ta tayi saurin d'an risinawa tana far'in
"Barka da warhaka Hajiya."
"Yauwa barka dai Baba Rabi sannu da aiki, wai me kika dafa ne? gaba d'aya na mance da abincin Alhaji."
"D'aya daga cikin abun da kike so aka dafa Hajiya."
kyakkyawar tukunyar dake kan gas Baba Rabi ta bud'e, wani daddad'an kamshi ya bigi hancinsu.
lafiyayyen jalof d'in shinkafa da macaroni yaji kifi da nama yasha kayan lambu irinsu karas da fis.
Kai Aunty ta girgiza ba laifi girkin ya had'u, Baba Rabi kwararriya ce a fannin girki, tana daga cikin ma'aikatan da suke aikin girki a gidansu. shiyasa da tayi aure ta bukaci mahaifiyarta da ta bata ita su taho tare dan ta yarda da iya girkinta.
amma duk da kwarewar ta a fannin girki, bata lamunce ta girka mata abincin da mijinta zaici ba, ita da kanta take shiga kichin tayi masa girki a duk sanda yake gurinta.
Kai Aunty ta d'an dafe tana tunanin idan fa tace zatayi masa wani girki yanzu lokaci zai kure.
kuma tana da tabbacin baici komai ba tun bayan abincin safe.
da fuskar tausayi Baba Rabi take duban Aunty sanin dalilin da yasata mancewa da lamarin girkin maigidan nata.
sakamakon Hajiya data d'agawa kowa Hankali kan sai an maida Feeryal inda a ka d'auko ta.
cikin muryar tausasawa ta ce
"Kikara hakuri Hajiya."
murmushi Aunty tayi kana ta ce
"D'an rike min ita haka."
ta mika mata Feeryal, ta isa ta d'auki wani kayataccen kula mai matukar kyau da burgewa da ka ganshi kasan ba kirar nan bace, ta zaro wani farin karamin towel da suke a jere a ma'ajin su na musamman.
ta goge kulan ciki da waje, ba wai ko dan ya yi datti ba al'adar ta ce hakan.
sannan ta zuba abincin ta rufe kular.
kana ta d'au plt da cokali da sauran abubuwan da ake bukata wajen cin abinci, tasaka su cikin
Kyakkyawan basket na musamman.
Ta dubi Baba Rabi tana fad'in
"Yauwa bari naje na kai masa, ki kula da ita kafin na dawo."
"To Hajiya." Baba Rabi ta fad'a tana mamakin yau abincin data girka zata kaiwa Alhaji, sai dai taga sauri tattare da ita, wan da shi yahanata tsayuwa girka masa wani abincin.
Sai da Aunty ta koma bedroom ta d'au mayafi kafin ta fita ta nufi sashin Daddy.......!
Mommyn Twins ce
🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ?*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇ðŸ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Bismillahirrahmanurrahim
🅿�3
Direct bedroom d'in sa ta wuce, a zaune ta taddashi kan wani lafiyayyen dogon kujerar da ke sakiyar katafaren d'akin nasa, mai matukar kyau da tsaruwa.
yana zaune yana duba wasu takardu ya yin da gefe guda yake lasa laptop d'in sa.
gefe da shi ta zauna tana yi masa barka da warhaka, kana ta d'aura da fad'in
"Ayi min afuwa a gafarce ni."
murmushi ya yi sannan ya ce
"Ina Feeryal data kwace min ke?."
itama murmushin ta yi kana ta ce
"Tana gurin Baba Rabi."
kai ya jinjina. ta zubo abincin ta janyo karamin table ta d'aura kai, sannan ta mike ta isa in da fridge ya ke ta bud'e ta ta ciro lemon da yafi so; had'e da kunun ayan da take masa na musamman take aje~ masa cikin fridge in sa, ta dawo ta zuzzuba masa cikin cups.
ta zauna a gefen sa yana ci tana had'a masa kan takardun daya wargaza su.
"Insha'allah ko mai yazo karshe na shiryawa Hajiya tafiya umura gobe, daga nan zasu wuce Egypt taga likitan ido, zasu zauna a gida na dake can nad'an wani lokaci kafin su dawo, insha'allah daga nan komai zai dai-dai ta."
duban sa Aunty ta yi tare da sauke numfashi ta ce
"Allah ya sa."
"Amin amin." Daddy ya fad'a yana kurb'an kunun ayanta mai sashi santi.
yana ci tana d'an janshi da hira cikin sigar jan hankali ta in da zai ci abincin sosai.
Yana kammalawa ta had'a kan kayakin cikin basket.
ya ce taje ta tuba Feeryal kada ta yi kuka, sukayi sallama ta fito, dan yau ce ranar da zai bar d'akinta.
shiyasa ma ya dawo side d'insa.
dan idan itace da kwana sashinta yake tarkasawa ya koma, har sai ya yi mata kwana biyun kafin yadawo side d'in sa da yamma.
sauran matan kuwa nan suke zuwa su same sa, sunyi fad'a har sun gaji kan suma sai dai yarika biyo su,
ya ce dasu duk wacce bazata iya zuwa ba ta zauna abinta baiyiwa ko wa dole ba.
A kofar parlour'n sa suka had'u da Umma Karima tana kokarin shigowa.
kallon banza tabi Aunty da shi tare da yamusa fuska cikin gatse ta ce
"Uhum iyayen jaraba har ya gudo ya dawo ma ba'a kyalesa ba, me yakawo ki nan a wannan lokacin, bakida hurumin zuwa nan yanzu, sai ayi gaggawar fita a bamu guri, in ba satar kwanan za ayi ba da ma an saba,
kada kuma ki sake ki ce zaki rika shigo mana da aljanar nan nan, ya'yan da ya haifa sune kad'ai ke da hurumin shigowa side d'insa, ba agolar aljanar ruwa mayya ba."
Murmushi Aunty tayi kana ta ce
"Ni da mijina har sai an iyakanta min san da zan zo inda yake?
a duk san da na bukaci zuwa in da yake zanzo; ko da kuwa a d'akin barcin ki yake, har a yanzu yana cikin lokaci na daga nan har zuwa fad'uwar rana,
ba ke ba ko wacce zai koma gurin ta yau bata da ikon dakatar da ni, zuwa in da mijina yake."
Aunty na kaiwa nan ta rab'a gefenta tayi gaba abinta, bata kuma bi ta kanta ba.
dan bata fiye biye musu ba idan suna haukansu, manna musu hauka take tabarsu suyita haushin su.
Umma Karima tabi bayan ta da harara da basket d'in da ke hannunta, tasan abinci takawo masa yaci.
hakan ma bakaramin kona su yake ba, dan ba kasafai yake cin abincin su ba.
a kufele ta karasa ciki, tun kan ta karasa cikin bedroom d'in sa tasoma mita
"Alhaji abinda kake mana fa baka kyauta mana, mu masu ya'ya mu ne abun wulakantawar ka, mu mukasan zafinka mu yakamata ka daraja mu."
hannu yad'aga mata kana ya ce
"Yanzu ni kin daraja ni da kika fad'a min d'aki kai tsaye babu ko sallama bare gaisu,
babu tausasa lafazi, me nayi muku na rashin kyautatawa?."
fuska ta yamusa tana cika tana basewa ta tsaya a tsaye a kansa tana fad'in
"Shekara nawa baka cin abincin mu tun da ka auro waccan matar ka ya ye cin abincin mu, a nan duk ran kwanan ta side d'inta kake tarewa, kana gurin mu ma tana biyo ka da abinci."