← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 52

Sashe 16

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy da kansa ya ja mota, batare da ya bukaci direba ba.
security bakin get sun sha mamakin ganin sa batare da direba ba, sannan bada Hajiya Fatima suka fita ba, dan idan suna tare da ita baya bukatar direba.
sai dai ga yadda suka ga yake jan motar sunsan akwai wata matsala.
dan haka security uku suka shiga mota suka bi bayansa.

Daddy na isa makarantar yafito yaruko hannun Feeryal tun daga bakin get d'in makarantar yashiga kiran duk sunayen malaman da suke koyarwa a makarantar.
da sauri duk suka fito da son ganin mai kiran nasu ganin Alhaji Abubakar Fiya ne da kansa, kowa ya fito ya yi cirko-cirko.
headmaster makarantar ya iso in da yake da sauri yana fad'i
"Ranka shi dad'e kai ne da kanta, Allah dai yasa lafiya?."
Daddy ya ce
"Ba lafiya ce ta kawo ni ba, babu kuma lafiya ga duk wanda ya nimi cin zarafin d'iyata, wane ne shi yana ina!?."
"Allah ya huci zuciyar ka Alhaji, wani abun ne ya faru? wlh bani da masaniya kan komai."
ya juya ya dubi sauran malaman ya ce
"Wai me yake faruwa ne wani abun ya faru yau she kuma ban sani ba?."

Malama Hauwa ce ta d'an matso ta ce
"Ni dai ban san ko mai ba amma d'azu naganta tana kuka na tambaye ta meya same ta ko bata da lafiya ne ta ce min Eh, kuma ni nasa direba ya maida ita gida."

Daddy ya dubi malaman d'aya bayan d'aya kana ya maida dubansa kan Feeryal ya nuna su da yatsa ya ce
"Acikin su wane ne yake cire miki wando!,
wlh duk sai na d'aure ku sai na sa an rushe makarantar nan an shafe babin ta."

Wani irin fad'uwar gaba ne ya ziyarce su duka.
a tare suka had'a baki gurin cewa
"Cire wando kuma!?."

Headmaster ya ce
"Subhanallahi wa'iyazubillah acikin makarantar nan."
ya dubi malaman ya ce
"Wane ne a cikin ku ke son b'ata mana sunan makaranta, ina sauran Teacher's d'in kowa ya fito."
Anty Hauwa ta ta waiga ta ce
"Duk muna nan sir Uncle Samir ne kad'ai baya nan yana office kwance bashi da lafiya."
"Tun yaushe ne baya jin dad'in, da ciwon yazo ko anan ya same shi?."
"No sir a nan ya same shi, ko d'azu lafiyar sa lau."
"Shima ya fito yanzun nan!."
ya karashe maganar da tsawa.
ta juya da sauri ta shiga ta kirawo shi.

Da kyar ya iya mikewa yana tallafe da abun cikin wandon sa, da yake jinsa kamar an tsinka shi fad'uwa yarage ya yi, yana tsoron ya sake wandon nasa abin ya fad'o.
sai da yafito yaga mutane sannan ya sake yana taune baki.
acikin abin da baifi awa d'aya ba gaba d'aya yagama fita yayyacinsa yana karb'ar azabar da baisan ta ina yake zuwar masa ba.

"Wane ne acikin ku yake shirin ketawa yarinyar can mutuncinta, yakuma b'ata mana sunan makaranta!?."
Headmaster ya yi musu maganar cikin tsawa.
gurin ya kacame da hayaniya kowa sai fad'i yake ba shiba.
Daddy ya nuna su d'aya bayan d'aya sannan ya ce
"Wane ne acikin su ke sa miki hannu cikin wando Feeryal!."
bin ko wannensu tayi da ido idanunta yatsaya kan Uncle Samir, ta d'aga hannu ta nuna shi.
ai kuwa kowa idanunsa ya koma kansa ana sallallami.

Daddy ya saki hannunta ya tako gabansa, Uncle Samir kansa a sunkuye, bawai ko dun jin kunyar abin da ya aikata ba.
sabar azamar da yake ji ne shi ya hana shi ko da iya kyakkyawar motsi,
a yanzu zafin azabar ta fiye masa jin kunyar.
"Kai d'angidan uban waye ne a kasar nan da kake shirin lalata min d'iya ta."
ba'a ankara ba sai ganin Daddy akayi yana aika masa da maruka ta ko ta ina a fuskarsa.
yakuma cewa security su tafi da shi.

Hakuri malaman suka shiga bashi, bai saurare su ba ya ce
suma bincike zata zo ta kansu, kuma zai cire yayan sa duka a makarantar dan sai ya yi Shari'a da mai makarantar gaba d'aya.
ya ja Feeryal ya ce da su Ameerah suzo su tafi ya kwashi yayansa duk ya yi gaba da su.

Aunty na zaune a parlour har lokacin har su Daddy suka dawo.
tana ganin su ta mike tana tambayar
"An same shi ko ya b'oye yaki bayyana kansa?."
Daddy ya ce
"Zauna Fad'imatu."
ya nuna mata in da ta tashi ta zauna jiki ba kwari idanunta akan sa.
kai ya girgiza mata ya ce
"An same shi da kanta ta nuna shi kuma nasa an tafi da shi, kuma da bakinsa ya amsa laifinsa ya ce bai yi mata fyad'e ba hannu kawai ya sa mata."
numfashi ta sauke tana fad'in
"Alhmdulillah, d'an iska zai iya sawa 'yar cikin sa ma, Allah ya kare ki Feeryal."
Daddy ya d'aga kiran da akayi masa yanzu a waya ya yi waje.

Aunty ta mike ta ruko hannunta suka shige bedroom bayi ta kaita sai da ta kuma duddubata ta dad'a tabbatar da babu ko mai dai, iya d'an karcewar nan ne dai ta gani, da ya yi mata da yatsunsa.
kana tagasa mata gurin da ruwan zafi.
tana yi tana godewa Allah da yasa a iya haka ya tsaya bai kara gaba ba.

Kan kace me gaba d'aya gidan ya d'auki zancen anyiwa Feeryal fyad'e.
dan 'yan kaho rahoton su Ameerah Sahla Nabila fyade suka ce Uncle nasu ya yi mata.

Mommy da Ameerah ta gama shirya mata zance wan da rabin sa karya ne.
ta rike hab'a ta na fad'in
"Tabd'i jam da ma ashe dukan kun da yake idan kun tab'ata yasan me yake samu a jikinta, 'yar kwal uba tun tana 'yar karamar ta tasan iskanci, ai da ganin da ma ta jima tana yi yanzu ne asirin su ya tonu,
to shi Alhaji da yasa atafi da shi beyi tunanin idan b'era da sata daddawa ma da wari ba."

A b'angaren Umma Karima kuwa tsistsinewa Feeryal d'in tayi,
ta ce "Dama tambad'ad'd'iya ce tun can nagode Allah ya kara na gobe, naso naji ance an garzaya da ita gadon asibiti, yamata kaca-kaca ya wargaza ta gaba d'aya,
shegiya tambad'ad'd'iyar yarinya,
mai zuben mayun aljanu, ko da shike aljanar ce da ma."

Hajiya Nafisat wato Mom ta d'unguma tayi side d'in Mommy a can suka had'e duka Mommy da Umma Karima da ita Mom d'in.
suka cigaba da tofin ala tsine wa Aunty da kuma Feeryal.

Hankali tashe Hajiya Safiyyah mahaifiyar Miemie Ammah kenan ta tafi sashin Aunty
suka shiga jajanta lamarin
Ammah ta ce
"Allah Ubangiji ya dad'a bawa 'ya'yan mu kariya, badun Allah ba kam da bamusan meyau zata haifar
ba, su kuma masu aikata hakan Allah ya cigaba da tona musu asiri, su kunyata a idon nuniya wata
kila ta sanadin hakan su shiryu,
idan kuma ba masu shiryuwa bane Allah kayi gaggawar kawar mana da su a ban kasa."
Aunty ta ce
"Amin ya Allah wlh Ammah'n Miemie kar kiga yadda na
shiga tashin hankali Allah kar ka kawo mana abin da bazai wuce."
haka sukayi ta jajantawa Ammah tajima
sosai a sashin kafin ta koma nata sashin.

Da daddare Mommy na side d'in Daddy dan yau ita ce da shi.
tun shigowar ta take ta sako maganar Feeryal d'in yaki kula ta ne, dan ya fuskanci kamar murna suke
da faruwar abun.
dan d'azu Umma Karima ta gama kalar nata.
d'an muskutawa Mommy ta yi ta ce
"Alhaji wai kuma fisabilllahi an kama yaron nan
anje an rufe shi, ba'ayi tunanin in b'era da sata daddawa da ri ba, karfe fa bata kara ita kad'ai dole
sai da abokin had'i, itama yarinyar ai tana da laifi, idan bata biye masa ba ai bazai sami kofa ba."
a fusace Daddy ya ce
"Haba Hajiya Halima 'yar wannan yarinyar me ta sani da zata beye wa wani na miji,
ku dai ji tsoron Allah kuma kuna da ya'ya matan nan,
musamman ita Karimatu ya'ya mata rai hud'u gare ta, babu wacce ta wuce kaddara,
ke ma kina da ya'ya mata uku,
ina tayi muku gargad'i ku fita a hurumin Allah babu ruwanku;
Feeryal ba fyad'e akayi mata ba, ya dai so ya keta mata haddin Allah kuma ya kare ta."

Baki Mommy ta tab'e ta ce
"Namu a wanne ana ta wani b'oye mana, fyad'e kam anyisa yana nan a zane baya gogewa watarana zai bayyana, mu ai 'yan kallo ne,
akan wata tsintacciya kake yi wa ya'yan cikin ka mugun fata,
to in Allah ya yarda bazamu gani a kan ya'yan mu ba, ehe."
kai Daddy ya girgizar ya mike ya shige bayi yabarta nan zaune.

Kwana biyu da faruwar lamarin mai makarantar da kansa ya yi tattaki zuwa gurin Daddy.
ya yi ta bashi hakuri da ban baki, yakuma ce zasu saka tsastsauran tsaro a makarantar insha'allah hakan bazata sake faruwa ba anyi na farko anyi na karshe.
sannan kuma ya kori uncle Samir a makarantar, ya aika masa da takardar kora a can ofishin 'yan sanda da ya ke a tsare a can.
Daddy ya ce ya hakura amma bazai mai da ya'yan sa makarantar ba.
da kyar dai ya hakura a bisa roko da ban hakurin da ya cigaba da yi masa.
washegari kuwa yasa direba ya kaisu makaranta.

Satin Samir guda a tsare a hanun 'yan sanda, sai da iyayen sa sukayi ta sintiri suna niman afuwan hukuma da kuma na Daddy,
da kyar Daddyn ya hakura dan dama yasha alwashin sai ya yi zaman gidan yari.
duba da iyayen nasa bamasu karfi bane,
sanadin hakan yasa a sake shi,
daga nan kuma a ka garzaya da shi gurin magani, dan abin cikin wandon sa ya daina aiki ya koma kamar lagwani.........!

Mommyn Twins ce

🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺

*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*

( _Book 1_)

*~Free page~*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

🅿�8
Chapter 16 · 0% Book details