← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 52

Sashe 31

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy ce zaune a parlour tana waya da Hajiya'n Dubai wata kanwar su Daddy ce, wacce take da zama a can kasar Dubai.
takan zo Nigeria jifa-jifa dan mijinta yana nan Nigeria ita kuma tana can Dubai da 'ya'yan ta,
zaman ta yafi yawa a can.
Mommy dake rike da d'aya wayarta tana dudduba wasu arnan kayan d'aki da Hajiya'n Dubai ta turo mata,
ta gyara rukon wayar dake kare a kunnen ta tana cewa.
"Gaskiya Hajiya'n Dubai wad'annan set ukun duk sun min, duka za'a bada kud'in su a sako a jirgi a kawo."
daga cikin wayar Hajiya'n Dubai ta ce
"Wai dama Hajiya Halima ba wucewa da su can UK d'in za'ayi ba, Nigeria za'a kawo su?."
"Eh Nigeria za'a kawo su a zuba mata su a gidan ta dake nan, idan sun shigo kasar yazamana da suna da masaukin su mai kyau, a can UK kuma ai shi angon ma yagama shirya gidan sa da ke can yazuba komai babu abinda za'a tafi dashi daga nan,
idan kunje abinda kuka ga babu sai kuyi odan sa acan d'in kawai."
"Ah yayi hajiyar mu, ai harka ta jin kunya baiyi ba,ai ni sam bana son harkar karanta,
me za'ayi da jin kunya kana cikin kawaye karika kunyata, idan fa kikaga gidan da za'a zuba kayan nan ba wani na arziki bane, ba nagani a fad'a bane ,
kawai a basu gida, kada mushiga kunyar kawaye, ace kamar mu aga gidan 'yar mu bai taka kara ya karya ba,
d'iya ga Alhaji Abubakar Fiya guda ace gidan ta zubin na talakawa, haba ina bazamuji wannan kunyar ba, kawaye suzo daga nesa suna yi mana kallon kasa-kasa, kallon raini,
kai ina da wuri ma zan shigo Nigeria naje na duba gidan da kaina,
idan beyi ba gaskiya za'a basu gidan da za'a zuba kayan nan,
dan wlh ban yarda da harka ta jin kunya ba."

Mommy ta sheke da dariya tana fad'in
"Hajiyar Dubai tamu, ai duk in da za'ayi bazan bari aji kunya ba, ko kin mance wane ne mijin Farida ne, Faruoq-Al'Hussain ne fa, kin san naira kuka take a family'n Al'Hussain,
da kanta Farida ta zab'i gidan da take so a cikin gidajen da mahaifinsa, Al-Hussain ya ce ya zab'i wanda za'a d'auko masa amaryarsa a saka ta ciki kafin bayan biki da kwana biyu su bar kasar."
"Yauwa yanzu naji zance ai ni na ma mance da ko d'an gidan wa d'iyar tawa zata aura, ah gaskiya mun baiwa jin kunya baya, Faruoq-Al'Hussain kai ka dace da d'iya ta."
suka sheke da dariya.

A b'angaren amarya Farida ma fa ba zama, duk da ba a kasar nan zasu zauna da mijin nata ba,
a can UK in da yake aiki zasuyi zaman shekaru goma kafin su dawo Nigeria,
sabo da aikin sa da yake yi a can shekaru goma zaiyi ya gama ya dawo gida Nigeria.
ana ta shiga da fita.

Sai ana biki saura sati Daddy ya dawo.
aiko Hajiya ta dira a kansa ko huta gajiya baiyi ba, ta ce ya d'auki Feeryal ya mai da ita tun da ya dawon.
sai da ya yi ta lallab'a ta ya ce tayi hakuri a gama biki tukun zai mai da ita.
da kyar ta yadda.

Tuni gidan Alhaji Abubakar Fiya ya d'auki manya manyan baki na kusa da ma na kasashen ketare.
ciki kuwa harda Hajiya'n Dubai da iyalenta,
da kuma kayan d'akin da Mommy tasa akayi odan sa daga Dubai.

Tun ana saura kwana uku biki aka fara gudanar da shagulgulan biki,
a manya manyan Hall.

Amarya Farida ta amsa sunanta amarya dan kuwa dubbannin d'arurruwan mutane ne suka shaida d'aurin auren, Farida Abubakar Shitu Fiya da angonta Faruoq-Al'Hussain.

Bayan d'aura aure jama'a suka soma taruwa a Hall na musamman dake a cikin gidan ta can baya,
wan da aka tanade shi sabo da tarurruka, na cikin gida idan ya taso.
nan aka tanada domin gudanar da walima bayan d'aurin aure.

Aunty ce ke saukowa daga saman bene ta cab'a kwalli had'i da gwala-gwalai, tayi matukar kyau ta dawo yarinya d'anyiwa sharaf tammar ita ce amaryar,
sai baza kamshi take.
Aunty Hindu d'iyar baffan su Daddy ta saka gud'a tana fad'in
"Kaga Amarya a gidan Alhaji Abubakar Fiya, wlh babu wan da zai ganki ya ce shekarun ki goma da yin aure,
tamkar kece amaryar ai dole ki rika rikita yayan namu, tsaruwa iya tsaruwa."
dariya ta bisu da shi ganin yadda duk parlour'n suka rud'e da zu-zu-ta-ta.
Aunty Hindu ta d'aga wayarta tana cewa
"Tsaya dan Allah na d'auke ki na turawa Yaya nasan tukuicina na daban ne yau."
"A'a huta abin ki ai gani a zahiri yafi gani a hoto, yanzun nan ma gurin sa na dosa."

Duk suka sheke da dariya har suna tafawa.
"Da gaskiyar ki wlh je ki gwada masa ya gani a zahiri wannan irin wanka, ba shigar bane sukayi miki kyau ke ce kikayi wa shigar kyau."
ita dai dariya tayi musu tayi waje...........!

Mommyn Twins ce

🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺

*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*

( _Book 1_)

*~Free page~*

*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

Bismillahirrahmanurrahim

🅿�14

Side d'in Daddy ta nufa ta kofar baya, dan tasan ta ainahin kofar kam cike yake tam da mutane.
ai ko hakan take har cikin babban parlour'n sa ba'i ne maza ciki a ciki.

D'akin kwanan sa direct ta wuce, tana shiga ta kirasa a waya.
ganin mai kiran nasa yasashi mike acikin jama'a ya nufi bedroom d'in sa, domin amsa kiran.
ya tura kofar yana kokarin kuma maida kiran dan ya yanke,
sai ganin ta ya yi tsaye cikin d'akin.
ido ya bud'e da kyau ya kura mata su, itako murmushi take sakar masa.
a hankali ya tako ya iso in da take.
hannu ta mika ta sakalo wuyan sa, tana cigaba da aika masa murmushi.
cikin sanyin muryar ta mai kara masa kaunar ta.
ta ce
"Daddy tun d'azu nake son ganin ka mutane sun min fin karfi."
ta karasa maganar da kashe masa ido.
wani numfashi ya sauke, sai kawai ya rungume ta ya na fad'in
"Godiya ya tabbata ga Ubangijin daya mallakamin wannan kyakkyawar tsuffar."
ya d'ago ya manna mata kiss a goshi.
d'an zame jikin ta tayi tana fad'in
"Daddy ka fara tsufa fa."
"Ina da ke ai ita ma tsufar bata isa ta dumfaro ni ba, sai dai ta tsaya a iya shekaru."
dariya ta yi ta ce
"Yau fa ka aurar da 'ya tsufa ya dad'a bayyana ga furfuran ka sun karu."
ta karashe maganar da muryar dariya.
kumatun ta yaja ya ce
"To kar ki bari tsufar tai mana tasiri, ki san yadda zakiyi ki yake sa tun kafin a fara kiran mijin ki da tsoho, shi ke nan ke ma kin tsufa."
dariya duk sukayi wa junan su.

Ya matsa can jikin bedside drower ya danna ma dannin bud'e sa, gilashin jiki ya zuge, yad'auko d'aya daga cikin makullan motocin da suke ciki.
ya zo ya mika mata.
ta karb'a tana bin key'n da ido sannan ta ce
"Na mene ne wannan?."
ya ce "Naki ne tukuicin wannan kwalliyar."
wani lallausar murmushi ta sake ta rungume shi tana fad'in
"Godiya marar adadi, naji dad'i dad'in da bazai fad'u ba."
murmushi ya bita dashi, yana matukar jin dad'i ya yi mata kyauta yaga tana nuna yabawa da jin dad'in kyautar da ya yi mata.
yana daga cikin abin da yake dad'a kara girman fadarta a cikin birnin zuciyarsa.

Bata jin kanta ita wata ce dan mahaifinta yana da dukiya, ko min kankancin kyauta takan nuna jin dad'in ta mara misaltuwa.
akasin sauran matansa da iyayensu ba koman komai ba sai fad'in ran tsiya.

Da sauri Miemie ta shige side d'in Aunty, ta haura sama da sauri tashige d'akin Feeryal.
tana zaune sunata wasa da kawayen ta, wan da ita take ganin su.
Miemie ta ce
"Feeryal taso muje ayi mana kwalliya ga mai kwalli tana kan yi wa su Ameerah, a side d'in Hajiya,
muje gurin walima ke bazaki je bane?."
"Ni bazan je ba Ammie na ta ce nazauna nayi wasa na a nan kije kawai abinki."
"Dan Allah taso muje gasu Umaima'n Dubai ma sun zo zo muje ki gansu."
ta janyo hannunta suka fita.
tun kafin su karasa sauka daga stairs hankalin 'yan cikin parlour'n ya dawo kansu.
wad'an da dama sunsan Feeryal d'in tun tana jaririya,
suna ta mamakin girman ta da yanayin tsarin zubin halittarta.
wad'an da kuma basu santa ba suna binta da kallon rashin sani, kallon itama daga cikin ba'in da suka zo daga kasashen turai suke mata.

Har sun zo shiga parlour'n Hajiya,
Feeryal tayi baya da sauri a matukar tsorace.
Miemie ta ce
"Hajiya bazata miki komai ba zo muje, kar a gamawa Ameerah a kama yi ma wani."
hannu Feeryal ta d'aga baki na rawa ta ce
"Ga mage can ni dai bazan je ba."
"Baya komai fa ki zo mu shiga."
"A'a ni bazan shiga ba!."
tayi maganar tana ja da baya a mugun tsorace, tamkar zata shid'e.

"Ke Miemie me kike yi a nan ana can anayi wa su Ameerah kwalliya ke kina nan, gashi har an watse an tafi gurin walima, kiyi maza kije a yi miki."
cewar Hajiya data fito zata gurin walimar tana gyara zaman mayafin ta.
ido ta gwalalo kan Feeryal dake ja da baya da baya.
"Me zan gani haka me ya kawo wannan aljanar nan?
ke Miemie kifita idona na rufe, ban rabaki da wancan yarinyar mai kamata faran mayu ba,
kin d'auko ta zaki kaita cikin jikoki na ta lashe su da maita ko ta shige jikinsu,
kar ki sake ki shiga min b'angare mayyar banza mayyar hofi ko na had'a ki da karnuka su yayyaga min namarki anan."

Ai da gudu Feeryal ta juya tayi waje.
Chapter 31 · 0% Book details