Sashe 39
Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Suna fita can suka hango Haulat tsaye bakin get d'in gidan su, suka tsaya ta karaso, ta shiga baya ta zauna tana fad'in
"Haba Maryam wlh akwai ki da lezi da duntuni mun tafi, duba time fa ki gani, har yaushe ne za a yi mana gyaran gashi, nifa har da gyaran jiki nake so na jima ba'a turarani an goge ni ba, har wani nauyi jikina yake min,
kuma da naso mu biya ta gareji na duba motata,
amma mu wuce kawai time ya tafi da yawa."
"To uwar 'yan mita yanzu dai gashi mun hau hanya,
wai tun shekaran jiyan nan ba'a d'auko miki motar a gareji ba?."
"Ina aka d'auko ni na ma fa gaji da ita so nake a canza da ma, jira nake Alhajin mu ya dawo da umurar nan a sake min wata."
"Aunty Haulat nima fa za'ayi min gyaran jikin nan,
shi yasa tun d'azu nake ta cewa Aunty Maryam ta yi ta gama mu tafi."
FEERYAL tayi maganar idanunta a kan waya tana ta aikin buga game.
ido Haulat ta waro ta ce
"Nashige su, wani jikin za'a goge, jikin naki? fata kamar audugar, ta ina za'a fara goge shi,
ai na rantse idan aka gogeki sai kin fitar da jini, ai ke a gogen ki Allah yayiyo ki, mune masu fama da damuwar gyaran jiki."
kai ta langwab'e cikin muryarta mai kamada shagwab'a ta ce
"Ni kam dai ina so ayi min nima."
Maryam ta ce
"Haha barta taje a d'aye fatar da dirza, zakiyi bayani, yarinya."
bata kuma magana ba idanunta yana kan game.
su Maryam kuma suka shiga hirar samarukansu.
Har suka isa bata ma san sun iso ba, sai da Maryam ta fisge wayar ta d'ago taga sun iso.
kyakkyawar lips d'inta ta turo ta karb'i wayar suka fito, suka nufi shagon.
Suna shiga suka tadda ana yi ma wata budurwa gyaran gashi, saurayin ta da ya rako ta yana tsaye a gefen ta, yana ta aikin yaba gyaran da ake mata.
FEERYAL ta isa inda kujera yake ta d'an ja rigar abayar jikinta da yake jan kasa sannan ta zauna.
tun daga yatsun kafafunta har zuwa sharab'arta masu kama da nunannen gwanda mai taushi,
ya kafe shi da ido, gaba d'aya ya mace a kallon ta.
wanda ita bata ma san yana yi ba tana ta sana'ar ta wato bugu tame.
sosai ya tafi a kallon ta.
budurwar tasa ta d'ago jin ya yi shiru da hirar da suke, ganin gabad'aya hankalin sa yayi nisa wani wajen, ta juya da sauri in da hankalin nasa ya tafi.
ganin wa mace ya kurawa ido, ta had'e rai.
ta mike dama an rigada an gama mata ana gyara mata pakin ne.
ta ce
"Malam biya kud'in mu tafi."
firgigit ya dawo da nutsuwar sa, sai kuma ya shiga kame-kame ya saka hannu a aljuhu ya zaro kud'i bai tsaya kirgawa ba ma ya direwa mai gyaran kan table, ta sakashi gaba sukayi waje.
Maryam da Haulat suka had'a ido, suka fashe da dariya suka tafa.
"Tana zaune ta had'a fad'a bata ma sani ba."
cewar Haulat tana dariya.
dariyar su ce ya sa ta d'agowa, suko guri suka samu suka zauna.
Aunty Jessica mai shagon itama dariya ta yi cikin hausarta da bai gama nuna ba ta ce
"Kefa Feer duk lokacin da kikazo sai kin had'a fad'a,
batere da kin san kinyi ba, wai dan ma kin rufe rabin fuskarki ke nan."
FEERYAL ta waro ido cikin tsitiriyar muryar ta mai fita da yanayin shagwab'a ta ce
"Ni kuma Aunty Jessica, su wa na had'a su fad'a?."
"Saurayi da budurwar da yanzu suka fita, yanzu haka nasan suna kan tirka fad'a a hanya,
da ganin ki duk ya rud'e, ke d'in ce ai ba ga na miji ba ko mace ke abin kallo ce a gurin ta,
itama d'in dai yanzu kishi ne ya rufe mata ido da sai ta tsaya ta kuma kallon ki,
Feer you're very beautiful."
"Aunty Jessica Feeryal ba Feer ba."
"Oh ni 'yasu your name is so difficult."
dariya duk sukayi.
FEERYAL taso ayi mata gyaran jiki, Aunty Jessica ta ce bada ita ba bazata tab'a jikin ta jini ya fito ba, fatarta a wanke a kuma goge yake basai an goge shi ba.
gyaran gashi kad'ai akayi mata, aka nad'e mata shi kamar gammo.
a dawowa FEERYAL ce ta tuko motar dan ta iya yanzu sosai.
suna shigowa ta zube kan kujera,
Hajja Umma tana ta mata tsiya wai raguwa kamar a kai ta d'auko matar.
shafaffen cikin ta ta shafa ta ce
"Hajja Umma yunwa."
"Sai iya fad'ar yunwa kamar da gaske abincin take ci, d'azu ma na duba naga saura abincin naki kad'an ya kare, nasa a sake miki wani, gashi a kichin da zafin sa ma kuwa,
nakuma kara miki wasu yourght d'in a fridge."
ai ko da sauri ta mike tayi kichin.
jim kad'an ta fito rike da plt da cake 'yan madaidai guda uku cikin plt d'in,
sai gorar yourght mai sanyi a d'aya hanun ta.
ta karaso ta haye kan kujera ta nad'e kafafun ta da sauri ta d'au cake d'aya ta kai bakin ta ta gutsira, ta wani lumshe ido tana tauna."
Hajja Umma ta ce "Ikon Allah mutum bazai ci abin kirki abu mai nauyin da zai rike mishi ciki ba, sai dai ya zauna shiririta."
murmushi ta sake idanunta a lumshe, sai da ta kuma gutsira kafin ta bud'e idanunta hankali.
tana tauna tana sakin murmushi wa Hajja Umma.
Maryam kam ta je ta shako plt da abinci ta zauna tana fad'in
"FEERYAL kam ai kamar ba hanji acikin ta, ina cake zai iya rike ni, ai in banci shinkafar nan ba ban ganewa."
ita dai tana jin su tana ta cin cake d'in ta tana santi.
Baba mai gadi ya yi sallama daga bakin kofar parlour ya gaida Hajja Umma sannan ya ce
"Hajiya Maryama wai ana sallama da ku."
Maryam ta d'an waro ido ta ce
"Mu kuma sai dai FEERYAL ita ke mana janye-janyen mutane duk sanda muka fita,
amma wayace maka shi d'in?."
"Ya ce ayi masa magana da 'yammatan da suka shigo yanzu a mota."
"Mance da shi Baba me gani ka ce baka ganmu ba wata kila mun fita ta d'aya kofar ne."
ya juya ya fita domin isar da sakon.
Hajja Umma ta ce "Idan Nasiru ne yazo fa."
"Umma ba Nasir bane ai da ya kirani, kuma baba mai gadi ai yasan Nasur bazai ce wani ba,
na san FEERYAL ma suka gani suka biyo mu."
Hajja Umma ta lakaci goshin FEERYAL tana cewa
"Ki dai na mana jaye-jaye, in ba haka ba na aurar da ki wa mai gundumar shira."
baki ta cuno tana taunar cake, batayi magana ba.
dariya Maryam tayi ganin yadda ta cuno lips d'in ta, bata fasa taunar cake d'in ba.
murmushi Hajja Umma tayi ta girgiza kai ta wuce babban kichin gurin masu aiki.
Karatu sosai FEERYAL ake yanzu babu zama anata kokarin barin secondary, ba ita ba ga duk wanda yake ajin karshe a secondary School anata shirin ban kwana.
ranar da zasu bar makaranta, kwarya-kwaryar biki akayi na musamman dan makarantar yawancin na 'ya'yan masu hannu da shuni ne.
iyayen d'alibai sun nuna bajinta, a ranar kuwa wad'an da suka bayyana soyayyarsu ga FEERYAL suna da tarin yawa,
ciki kuwa harda malamansu da ba'in da suka zo domin tayasu murna har da ma iyayen wasu d'aliban.
sai dai babu wanda ta saurara cikin su.
ya yin da malamai suka sallami d'alibai cikin karramawa.
bayan anyi ciye-ciye da shaye-shaye dasu d'aukar hotuna.
ko wani d'alibi ya kama gaban sa.
Bayan an dawo gida kuwa liyafar cin abinci Abba ya shirya duk saboda murnar zuwan wannan rana.
aka sallami mutane da kyaututtuka na musamman mai d'auke da hoton FEERYAL ajin ko wace gifts.
Bayan kwana uku
FEERYAL da Maryam suka tafi gidan Aunty Zainab, sai yamma suka baro gidan.
FEERYAL ce ke jan motar, da sauri ta taka burki sakamakon shan gabansu da wata mota tayi.
ta dafe kirji jikin ta na b'ari, dan batayi aune ba taga motar a gaban ta.
cike da jin haushi Maryam ta ce
"Amma wannan anyi mara lissafi so yake ya jaza mana fitina."
ta kalli FEERYAL ganin yadda gaba d'aya jikinta ya d'au b'ari, ta fashe da dariya.
"Ke kam anyi babban matsoraciya anan, sai kace munyi karo, da'alla dawo nan na jamu dan wannan tsoron naki zaki iya jefar damu anjima."
Tun kan ta karasa fad'a da sauri FEERYAL ta b'alle marfin motar ta fito,
dan a yadda ta tsoratan nan bazata iya driving d'in ba ma.
yana ganin fitowarsu ya zoge glass d'in motar sa.
idanunsa a kan FEERYAL.
Maryam ta hararesa tana fad'in
"Wannan wani irin hauka ne sai kace baka gani, zakazo ka sha gabanmu da moto, idan baka son taka rayuwar mu muna son tamu."
FEERYAL kam bata iya cewa komai ta zaga ta shige
gefen da Maryam ta fita.
Gyara zaman gilashin fuskarsa ya yi sannan ya yi sama da gilashin motar,
yaja motar batare da ya ce komai ba.
Maryam tayi tsaki ta shige mazaunin direba, taja suka tafi.