Sashe 47
Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya ta ware ido tare da buga kirji
"Nashiga uku! Abubakar kasan me kake fad'a kuwa,
'yarda ta kai fitina can kake so ka kuma dawo mana da ita ta kawo mana fitanar nan,
Abubakar annobar da muka kakkab'eta agidan kake so ka kuma yayub'o mana ita ka dawo mana da ita,
kanka d'aya kuwa Abubakar,
to ka dawo hankalinka ko da wasa kada ka soma ban yarda ba Allah ma bai yadda ba,
kada ka sake ka kuma jajjab'o mana fitina a gida,
barsu su karata a can."
"Hajiya ki fahimce ni ba fa zata dawo gidan nan din-din-din bane zuwa na d'an wani lokaci ne zata koma, daga zaran an gama bincike,
zata zo ne a matsayin bakuwar da zata koma,
ba wani jimawa zatayi ba, daga zaran an kama sauran b'arayin zata koma."
"Oho kace kawai zaka kawo ta sabo da b'arayin su biyo ta nan, sai su had'a da jikokina su kwashe suyi gaba,
Abubakar ina rabaka da kiwon shanu kana ce kyalla ta b'ata, to ban amince ba kada ka soma, na gaya maka ke nan."
Shiru Daddy ya yi bai kuma ce komai ba, kana ya mike ya ce
"To shike nan, duk yadda kika ce hakan za'ayi Hajiya Allah ya huci zuciyar ki, a wuni lafiya."
ya d'aga kafa yana kokarin tafiya da sauri ya kai
hanu ya d'an dafe kirjinsa.
ya shiga d'an kananun tari yana dafe da kirjin nasa.
Hajiya ta mike da sauri tana bubbuga kafad'ar sa
"Kai Abubakar zauna zauna tukun, kana ma shan maganin ka kuwa, ko na kira abokin turawa ne ya rubuto wani maganin da zaka sha yanzu."
kai ya girgiza ya ce
"Kafin na fito ma sai da nasha magani, ba komai zai lafa."
Hajiya ta rud'e gaba d'aya tana jera masa sannu.
Daddy ya ce
"Bari naje na d'an kwanta nasan zai lafa zuwa anjima,
amma hajiya da an duba batun nan wanda ya taimaki wani Allah zai taimake sa, shifa d'a na kowa ne,
idan kaso ya yi kyau ka taimaki al'umma gaba d'aya ne."
Hajiya ta kwantar da murya, duk abinta sam bata so taga 'ya'yan ta cikin halin ciwo
"In ban da kai Abubakar ciwonka na kokarin tashi amma kana magana kan aljanar can,
ina mu ina taimakon aljana ai sai dai danginta aljanu,
duk in da zata zauna sai ta haifar da fitina,
sabo da ba jinsin mu ba ce,
kaje ka nutsu kada ciwo ya kayar da kai,
amma tun da ka matsa sai ta zo ai amma tayi harkarta karta shiga harkar jikokina,
ta zauna can kada ta rab'e su,
ana gama bincike kuma takoma can in da akayi gayyarta."
Daddy ya ce
"Nagode Hajiya."
"Jeka maza kaje ka kwanta ka natsu kirjin zai lafa."
ya ce to.
ya fita ya koma sashin Aunty.
Aunty na ganin sa ta tare sa da sauri tana tambayar sa ya dai dan taga alamar kamar da akwai abin da ke damun sa.
ya ce
Ba ko mai tun shekaran jiya yake jin kirjinsa yana masa zafi, sai da abunnan ya faru ya gane fargabar hakan ne ke bibiyarsa.
nan yake shaida mata Hajiya fa ta amince FEERYAL ta zauna kafin komai ya lafa.
Aunty tayi farinciki matuka sai dai kuma ganin kamar ciwonsa nason tashi sai duk ta shiga damuwa.
bata gusheba sai da ta tabbatar da yasami bacci.
Su Aunty na parlour bayan sunyi breakfast, FEERYAL na kwance jikinta tana ta zuba shagwab'a,
Aunty na taje mata gashi wai dan ta ce zata kira mai kitso tayi mata kitso, take ta birgima a jikinta wai ita bata so yana mata zafi.
Aunty tarike hab'a tana fad'in
"To kawai a aske gashin tunda bakya son kitso,
kinfi so kiye ta nad'e gashi, ai ko tace gashin ma kad'ai ya ishe ki,
in kikayi kitso fa ai zaki huta na kwana biyu,
kafin aje a sake wankewa."
da sauri ta ce
"Allah a aske Ammie damina yake."
dungurin kanta tayi ta.
zatayi magana kiran Ammah ya shigo wayarta
ta d'aga da sallama bayan sun gaisa Ammah ta ce
"Hajiya Fatima ban samu na shigo da safen nan ba,
ya dai kika sami labarin jikin FEERYAL."
Aunty ta yi murmushi ta ce
"Ai gani ga FEERYAL jiya Daddy ya d'auko ta."
"Dan Allah da gaske ikon Allah FEERYAL anzo amma dai jikin nata da sauki ko, bari na gama na shigo."
Miemie dake zaune can gefe tana dane-dannen waya jin Ammah ta ce FEERYAL tazo.
ta jifar da wayar tana fad'in
"Ammah FEERYAL tazo?."
kai Ammah ta gyad'a, aiko da sauri Miemie ta mike da gudu tayi waje........!
Mommyn Twinc ce
🌺 *FEERYAL* 🌺
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
*~Free page~*
*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'SâœðŸ?*
*🇦SSOCIATIONðŸ¤ðŸ»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇ðŸ»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
🅿�21
Da gudu Miemie ta shigo parlour'n Aunty tun daga bakin kofa ta ke fad'in
"Aunty ina FEERYAL wai da gaske tazo, FEERYAL FEERYAL kina ina?."
FEERYAL dake kwance kan kafar Aunty ta mike tsaye da sauri.
Miemie ta karaso ta tsaya suna kallon-kallo.
yayin da dukkanin su kamannin yarantar su yake zuwar musu cikin kwakwalwa,
duk da kamannin su dukansu ya canza a yanzu bai hana amintakarsu tasiri wajen gane junan su lokaci guda ba.
a tare suka nuna junan su da hannu tare da kiran sunan junan su a tare.
"FEERYAL!."
Miemie ta fad'a.
FEERYAL ma ta ce
"Miemie!."
wani irin rungume junan su sukayi cikin mashahuriyar murna da farinciki, suna dariya.
Miemie ta janye jikinta tana duban ta da mamaki take fad'in
"Wai FEERYAL ke ce haka?."
FEERYAL tayi murmushi ta ce
"Miemie kema ke ce haka? ga yadda kika zamo wata katuwa da yawa."
"Kee da ma na girme ki, ko ba haka ba Aunty, amma dubi yadda kika zama har kin fini fa."
cewar Miemie tana zagayata da duba gaba da bayan ta.
Aunty dai dariya take ta binsu da shi, kaunarsu tun na yarinta abin yana ta burgeta.
Miemie ta b'ata rai tare da hararar FEERYAL ta ce
"Ko tuna ni ma bakyayi ni ce kad'ai mai damuwar tunaki, nifa da tunanin ki ma na girma,
ki tambayi Aunty kullum sai na zo part d'innan,
sanda na mallaki hankalin kaina kuwa nakarb'i lambarki wajen Aunty amma ko na kira ki bakya d'agawa,
kusan kullum sai na kiraki bazaki d'aga ba, sai na hakura kawai na daina kiran naki amma ban iya cireki cikin raina ba."
"Miemie nimafa ban cireki a raina ba, kina raina,
bakuwar lamba ce bana d'agawa da kinzo kin kirani da lambar Ammie'na."
"Ai nazo ranar nasa Aunty ta kira min ke aka ce bakya gida kin tafi school,
da yamma kuma nayi ta kiran lambar ki yana shiga baki d'aga ba."
Ganin diramar nasu Aunty tayi dariya ta ce
"Ai wayar FEERYAL kam na buga game ne, na mance ne ma da lamban Hajja Umma ko na Maryam na baki, shine zaki same ta."
Miemie ta ce
"To sannu biloniya wato bakuwar lamba ce bakya d'agawa, gudun kada ace ki kawo kud'ad'e ko."
dariya FEERYAL tayi
cikin tsiririyar muryarta mai fita da yanayin shagwab'a ta ce.
"Ke ba haka bane ina d'agawa sai ace FEERYAL mun had'u a waje kaza dama wata ce ko wani ne ya bani lambar ki,
to ya yanzu in zo ne,
niko sai in kashe wayar daga nan na daina d'aga bakuwar lamba."
dariya duk suka fashe da shi harda Aunty.
Miemie ta ja hannunta tare da d'aukar d'an karamin gyalen ta dake kan kafar Aunty ta mika mata ta ce
"Zo muje Ammah ta ganki."
Suna tafe Miemie tana ta zuba mata surutu,
FEERYAL ba gwana ce a iya surutu ba, sai dai tayi ta binta da murmushi had'e da dariya.
wani bin kuma ta amsa mata ba mai tsawo ba.
Miemie taja ta tsaya ta d'an waro ido da damuwa ta ce
"FEERYAL karkiga yadda hankalina ya tashi da akace
an sace ki, ranar ko abinci banciba nayi ta kuka."
kafin FEERYAL tace wani abu suka hango su Ameerah sun fito daga side d'in Hajiya.
Miemie ta ce
"Yauwa tsaya gasu Ameerah can bari naga ko zasu gane ki taho muje."
ta janyo hanun ta suka karaso gurin su.
Tun daga can suka kafe FEERYAL da kallo suna son sanin wace bakuwa sukayi a gidan.
suna isowa inda suke Sumayya ta ce
"Wow see beautiful Miemie wannan fa? a ina kika zamo balarabiya haka."
"Dan Allah Sumayya baki gane ta ba?."
cewar Miemie tana dariya.
Ameerah ko hanci sama ta d'aga tana yamutsa fuska ita a rayuwar ta ta tsani taga wacce ta fita.
ta ce
"Sai wani rawar kafa kike ta ya za'ayi ta santa bata tab'a ganin ta ba, kasarsu ba d'aya ba."
"Laa Ameerah ke ma baki gane ta ba, Sahla Nabila kuma duk baku gane ta ba, to ku bani goron albishir na fad'a muku ko wace ce ita."
Miemie ta miko musu hanu tana dariya.
Sumayya ta zuba mata tafi a hannun tana fad'in
"To an baki."
su Nabila da Sahla dai murmushi sukayi.
Ameerah ko fuska ta yamutsa, ita haushin ganin yadda Miemie'n ke ta rawar kafa.
Miemie ta ce
"So surprised! FEERYAL ce."
Sumayya ta ce
"What!.
"Yes of course ita ce dai."
kai Sumayya ta girgaza tana kare mata kallo sai kuma ta ce
"Ba laifi."
Ameerah Sahla Nabila a tare suka bud'e ido da baki suna kallonta.
Ameerah ta ce
"Tabd'i jam! annoba ta kuma dawowa gidan mu,
wai ke baki da gidan uba ne kam sai dai ki rika yawo gidan mutane kina addabar rayuwar su,
idan da kin zauna lokacin muna yara yanzu kam baki isa ki zauna da mu ba, mayyar aljana,
mttsss dalla kuzo mu tafi,
akan wannan aljanar kika tsayar da mu har dawa ni wai Surprised aikin banza."
Nabila da Sahla suka ce
"Ai kuwa bara da bana ba d'aya ba ki karanta hakan da kanki."
Ameerah
ta janyo hannun Nabila da Sahla, da suke aikawa FEERYAL harara, Sumayya ta biyo bayansu sukayi gaba.