← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 52

Sashe 51

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma karima ta shiga masa godiya kamar zatayi masa sujjada.
kana ta d'aura da fad'in
"Allah ya ja kwanan boka ina batun kanwata Siyama da d'an mijina Abdurrahim ya kwana,
akwai wata 'yar kawar mamarsa da suke son had'asa da ita Kuraiba 'yar Hajiya Luba, kasan damuwata ai na wancan maganar ta baya,
to ina so a birkita masa lissafi daga zaran ya diro Nigeria yaji duk duniya babu wacce yake so sai Siyama,
tanan ne zamu dad'a samin nasarar wajen cimma burin mu,
sannan game da 'ya'ya na fa har yanzu babu wanda ya fito da niyyar aure,
ita babban 'yata ma Bilkisu da muka samu muka cafke saurayin yace za'ayi aure sutafi
can kasar Japan tare tun da yasa kafa yabar kasar ya dai na kiran ta ma,
babban burina boka ace nima ga d'iyata tayi aure a wata kasa kamar dai Farida 'yar mijin nan nawa,
shekara goma ke nan suna can ba me jin kansu,
boka abinnan na dami na su rai uku babu wani d'an
mai kud'in da yazo yace yana son su da aure,
idan suka zo suka yi hira idan suka tafi sun tafi ke nan,
yanzu maganar da nake maka har karamar su Nabila itama ta zamo budurwa,
boka a taimake ni a karkato da hankali Bilal ya dawo ayi auren nan,
sannan suma sauran a samo musu wasu 'ya'yan manyan suzo su aure su, kamar dai yadda aka karkato mana da hankalin Bilal d'in da dai."
ya ce
"Duk wannan ba matsala bace kin samu."
"Godiya nake boka."
ta bud'e jaka ta rika ciro kud'i tana tara masa a gabansa tana aikin zuba masa godiya da kirari.
har ta mike ta dawo ta zube kasa tana fad'in
"Boka ina ajiyayyen aikin mu?."
"Gashi can cikin tulu a d'ad'd'aure har yanzu kin kasa samo cikiton na karshen, kina kawowa shikenan matsalar ki ta kare."
ta mike tana fad'in
"Na ukun ma bazai gagara ba tun da aka samo biyu, zanje nacigaba da farauta, kannan duk wad'annan matsalolin sun kau."
ta fice cikin kogon tana ta zabga masa godiya.
ta fito ta d'au d'ankwalinta da mayafi da takalmi duk ta saka sannan ta nufi mota ta shige suka juya gida.

Zaraddin ne ya shigo parlour'n Mom d'in su yana magana cikin kunkuni.
"Ai an dad'e ana nuna mana wariya, wlh nayi kud'i babu wan da zan taimaka."
Mom da Shamsuddin suna zaune a parkour.
Shamsuddin ko kallon sa baiyi ba,
Mom ce ta d'ago tana duban sa ta ce
"Kai da waye kuma?."
ya ce "Daddy mana wlh tun ba yau ba yake nuna mana wariya bamu gene bane kawai,
in dai hidimar Ajmaal ne baya bincike zakiga ya bashi ko nawa ne,
wai yanzu naje ya bani wasu 'yan kud'in da basu kai sun kawo ba, amma ya tsaya bincike na wai me zan dasu,
kamar ni d'in nan wai sai an tambaye ni abin da zanyi da kud'i,
abokai na kaga kowa yana abinda yaga dama da kud'i amma wai ni baza'a bani kud'i nayi abin da naga dama da su ba,
in za'a banin ma baza'a bani na kirki ba kuma wai sai an tsaya yi min binciken me zanyi da su,
bawai babu kud'i ba gasunan baza'a bawa mutum ya yi abinda yake so ba,
wai yanzu naje ya bani 5 million zamuyi biki ya tsaya yana ta yi min wasu bincike,
ina gurin Ajmal yazo ya tambaye shi kud'i ya tura masa ba tare da wani bincike ba,
haka wancan karon naje ya bani 2 million ya d'auki million d'aya da rabi ya bani,
ina zauna a gurin ya turawa su Ajmal d'in abin da ya bani bayan ni na fara tambaya,
a fili yake nuna banbanci,
na rantse bazan sake zuwa tambayar sa kud'i bama,
bare a tsaya yimin bincike kamar b'arawo."

Shamsuddin ya harare sa yana fad'in
"Kai wlh baka da godiyan Allah Zaraddin, ai kuwa baka isa kace Daddy yana nuna wariya tsakanimu ba,
aiko kaf cikinmu bawan da yake yawan zuwa neman kudi masu yawa akai-akai ba sai kai,
bini-bini kaje neman kudi agun Daddy kuma ajmal
dakaga yanemi kudi yanzu abu me muhimmanchi zaiyi,
kaikumafa club zakaje dashi ko wancan karon ma daka nemi million biyu
akabamu million daya da rabi rabi mu hidiman karatu zamuyi dashi,
amma kai kumafa naka party kayi dasu."

Mom tace wa Shamsudeen
"Rufa min baki da'alla shikenan mutum bazai fad'i abin da ke damunsa ba,
ya huta sai yabar damuwa a cikin sa ta kasheshi,
ni wlh Shamsudden kana bani mamaki kai da d'an uwanka twins brother naka amma kafi fifita wasu akanshi."
Shamsuddin yagirgiza kai yace
"Mom wlhy Daddy yana iya kokarin shi akanmu,
ko Dad daya haifemu bayamana kokarin da Daddy yakemana,
shifa yadauki nauyin karatunmu harmuka gama yasamamana aiki,
kai kaki nutsuwa ka kammala karatun,
kullum kuma yana damuwa kan ka koma makaranta,
kuma dukda yasama mana aiki muna karb'ar albashi,
amma shi yake bamu kudin man da muke sawa a motocinmu idan zamu fita,
bai ware ba kuma har da kai yake baka."
dogon tsaki
Zaraddin ya yi
ya ce "Wannan duk lissafin ka ne baka san cikin sa ba."
Shamsuddin ya girgiza kai ya mike ya yi ficewarsa. Mom natafad'a shikenan ga gaskiya karara amma ahana mutum fada.

Tun daga dinning Aunty ke kiran Feeryal
"Yanmatan Ammie wai har yanzu ba'a gama wankan bane,
yi sauri ki fito ki karya mana, karfe 12 saura bakiyi breakfast ba?."
ta iso bakin kofarta ta tura d'an jim tayi a bakin kofar jin tana magana had'e da dariya.
tasan Miemie bata zo ba da kawayenta
Chuchu da Chulu take, sai ta janyo mata kofar ta koma da baya.
ta gama shirya breakfast kafin ta dawo
ta turo kofar Feeryal tana fad'in
"Ke Feeryal wai har yanzu baki yi wankan bane?."
Feeryal dake zaune gaban mirror tana murza mai a jikinta, ta langwab'ar da kai cikin siririyar muryarta mai fita da yanayin shagwab'a ta ce
"Ammie nayi fa yanzu zan sa kaya."
"To yi maza ki fito ki yi breakfast."
ta juya ta janyo mata kofa.
ta mike tana duban Chuchu da Chulu ta ce
"Idan nayi breakfast anjima zamuje gyaran gashi da Miemie,
ko zakuje?."
sukace a'a mu zamu tafi in kun dawo zamu dawo.
"Feeryal ki fito mana tun d'azu na zuba miki abincin sai ya yi sanyi ne."
"Nagi zuwa Ammie."
tayi parlour da sauri suma suka kama gabansu.

A saman dinning ta tadda Aunty ta zauna tana fad'in
"Ammie ina cake d'in? shi zan fara ciki."
Aunty da ta kura mata ido har ta zauna ta ce
"Gashi nan cikin plt d'in can, ke Feeryal ya naga kamar babu bra a jikin ki?."
baki ta d'an cuno murya a shagwab'e ta ce
"Ammie zafi-zafi yake min kamar yana mistsina na."
hab'a Aunty ta rike
ta ce
"Au shiyasa kullum bana ganin ki da shi, na d'auka ai ko dun kina zaune a gida ne kawai,
har in zaki fita ma bazakisa bra ba, dubi kirjinki kallo d'aya za'ayi miki asan bakisa bra ba,
kina tafiya nono na motsi cikin riga,
hauka kike Feeryal ko ma me bra'n yake miki bazaki sakaye kirjinki ba,
ko da shike ba laifin ki bane laifin Maryam ce, da take ganin ki kina yawo haka,
idan Hajja Umma bata lura ba ita da kuke kwana tare ku tashi tasan sarai bakya sawa kuma bata nuna miki ki sa ba."
Aunty ta janyo wayarta dake d'aure saman dinning ta na cigaba da fad'in
"Ai ko a can Abuja da babu maza cikin gidan bayan ma'aikata da suke waje, zaki sakaye kirjinki bare kuma nan da muke da manyan kattin maza."
lambar Maryam Aunty ta kira bugu d'aya ana biyu ta d'aga.
daga cikin wayar Maryam ta ce
"Aunty Faty ina kwana ya Feeryal."
"Ba gaisuwa na kira kiyi min ba, dan tsabar rashin hankali kina kallon Feeryal tana yawo haka da kirji a tsastsaye suna motsi cikin kaya baki tab'a ce tasa bra ba,
kina da hankali kuwa Maryam."
"Ayya Aunty Faty ki tsaya kiji, Allah kullum idan zatasa kaya sai na ce ta saka bra,
ita ke kin sawa wai mistsinin ta yake, har Hajja Umma ma nafad'a mata ita tace na rabu da ita tun da yana damin ta."
"Da manyan nonuwa a tsastsaye suna rawa cikin rigar za'a kyale ta tana yawo haka,
nifa banga laifin kowa ba laifin ki kad'ai nagani, kuma zaki gamu da ni."
Aunty ta kashe wayar tana cigaba da fad'in
"Taya za'a bari ki rika yawo haka ai koma me bra yake miki haka zaki daure kirika sawa,
taso maza muje ki saka yanzu, da haka zaki koya har ki saba."
ta janyo hannunta suka nufi d'akin ta.

Aunty tayi mamakin ganin tarin bra cikin kayanta da suka kai kusan guda talatin, da yawa kuma sabbi ne bata tab'a sakasu ba.
ta d'au guda ta mika mata ta ce
"Maza ki saka ki fito yanzu ina jiran ki a parlour."
kamar zatayi kuka tana ta shagwab'ewa har da bubbuga kafa a kasa,
wai iti mistsinin ta yake kuma yana shaketa ya hanata numfashi.
Aunty ta ce
tasa haka maza ta fito yanzu ba da itaba ga kattin maza a gida tana yawo kirji na tsalle a cikin riga.

Ko da ta saka ta fito Aunty ta ce
"Ko ke fa bakiga abubuwan sun kama kansu sun zauna cif sun nutsu a cikin bra ba, ina amfanin kina motsi suna motsi suma."
"Allah Ammie cizona yake."
"Ai saboda baki saba sawa bane kina sabawa zai daina, maza ci abinci."
ta turo mata plt guda biyu gabanta dana cake dana soyayyen kwai da dankali.
tana gamawa kiran Miemie na shigowa wayarta ta d'a Miemie ta ce
"Feeryal fito mu tafi gani a bakin get d'in Aunty."
ta mike tana sanarwa Aunty abinda Miemie ta fad'a mata.
Aunty ta ce
"Ki kula sosai Feeryal kar ku dad'e ana gama muku kada ku tsaya ko ina ku dawo gida."
ta ce tom.
ta gyara rolling d'in gyalen abayar jikin ta, sannan ta nufi waje.
Aunty na ta yimata kashedin kada ta tsaya ko ina suna gama abin da zasuyi su dawo gida.
Chapter 51 · 0% Book details