← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 52

Sashe 50

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Umma karima ta ce
"Ke dalla tafi can, ko da wasa naji batun nan a bakin Daddy'n ku sai na sab'a miki,
kaf direbobin gidan nan banga diriban da ya kai Sule iya tuki ba,
tukunna ma ina direba na ne ba naku ba,
ko da wasa na sake jin kin masa rashin kunya sai na sab'a miki,
kiyi wa kowa rashin mutunci banda Sule dan shi mutumin kirki ne,
babu ruwanki da shi na gaya miki ke nan,
ni bari na tafi, ke Siyama bana ji kince anjima zaku fita da saurayin ki ba."
"Eh Aunty Karima yanzu ma mukayi waya ya ce min yana zuwa."
Umma Karima ta ce
"Wai har haka kika bashi dama ne Siyama karfa ya b'ullo da batun aure ya b'ata mana shiri."
"Ah haba ina ai shi wannan d'an hirar rage zafi ne kawai,
yaushe zan bashi dama ga dahir a kasa."
"Yauwa to yanzu naji batu zanje na dad'a jin nasarar da take tinkaro mu,
wai ke Bilkisu har yanzu Bilal bai kiraki ba?."
Bilkisu ta mara baki tana gyara zaman ta idanunta a kan wayar da take chatting ta ce
"Tun da ya tafi Japan sau biyu mukayi magana, yanzu ko na kira sa ma wayarsa baya tafi,
ni bazan ma kara niman sa ba in ya gadama ya neme ni,
ni na sami wani ma yana ma zuwa anjima."
"Dalla tafi can yaushe zaki jira har sai ya neme ki, kiyi ta nimansa har wayarsa ta shiga,
zan sami Daddy'n ku muyi magana a d'aura auren kawai a kaiki can Japan d'in a wuce gurin,
karki sake ki kunyata ni gaban kawaye na,
ni dana gama fad'a nima 'yata zatayi aure a kasar waje,
yanzu ki kawo min wani batu zanje har gida na sami maman Bilal d'in bari na je na dawo."

Ta fice waje tana sambatu.
burin ta ace itama d'iyarta tayi aure a kasar waje kamar yadda d'iyar Mommy Farida itama ta yi.
ta nufi parking lot d'in ta,
a jikin motarta ta dadda Sule direba yana gogewa yana magana.
yana ganin ta ya wani washe baki yana fad'in
"A'a hajiya barka da fito wa."
"Barka dai Sule yi sauri muje bar goge motar nan,
da wa kake surutu haka?."
fuska ya d'an had'e ya ce
"Da waccan yarinyar mana Nabila yanzunnan ta gama gwazamin rashin mutunci."
"Rabu da ita da'alla sai hakuri kasan har yanzu Nabila yarinya ce, kuruciya ke damun ta."
ya ce
"To ai shike nan adai rika gwada mata babba babbane,
yauwa ba dai gurin wancan Mali'n zamu ba, tun kan muje ki zazzage masa bakin jaka duka ina bukatar kud'i fa."
"Kai ka fiye korafi Sule, yaushe-yaushe ne na baka naira dubu d'ari biyar, kayi yaya da su wai kana nufin har ka kashe su,
a karshen watan da ya karen nan fa Alhaji ya baku albashin ku,
da abin da kowa zaici a gidan sa na tsawon wata guda,
yabaku baiyi da sati ba na baka kud'i dubu d'ari biyar d'in nan da karin kayan abinci,
matan ka d'aya da 'ya'yan ka uku me kakeyi da kud'i haka."
"Haba Hajiya kya tambaye ni abin da nake yi da kud'i,
kud'in haya na biya na siyi abinci na turawa tsoffi can Nijar, kin ga ko ai kud'i sun kare."
"Ni Sule kana bani mamaki, banga ammafin sai da gidan da Alhaji ya raba muku da kayi ba,
ko wani ma'aikaci yana zaune a gidan da aka bashi cikin rufin asirin shi, babu ruwanshi da batun wani kud'in haya,
amma kai ka tashi ka d'au gida ka siyar babu kud'i babu gida,
gashi kana kan damuwar kud'in haya."
"To ya ya za'ayi kinsan dai lalurar jinyan iyaye ce ta sani sai da gidan nan,
a ni ma min alfarma Alhaji ya kuma bani wani,
amma kafin nan dai ki bani wani abu a gurin ki kada muje ki juye masa kud'in duka."

Umma Karima ta shige mota ta zauna gaba shima ya shige mazaunin direba,
yana cigaba da fad'in
"Hajiya matsuwa ce adai bani wani abin."
ta zuge jaka ta ciro d'aurin 'yan dubu d'ai-d'ai guda biyu ta damka masa tana fad'in
"Ga wannan 200k ne sai ka lallab'a, bari mu dawo zan kara maka,
sannan zanyi wa Alhaji magana za'a kuma baka wani gidan,
yanzu dai muyi sauri ina da babban matsala so nake na ga Mali cikin gaggawa."
ya ja motar suka fice daga side d'in ta suka nufi babban get suna fita gaba d'aya a gidan ya juyo yana fad'in
"Ace wai ina gidan nan a karkashin Hajiya Karima,
sakani na da jirgi wai sai dai gani da ido idan na kai masu shiga cikin sa airport,
haba Hajiya wai ina batun tafiya ta makka ce ta kwana."
"Wannan shekarar zan biya maka hajji shike nan."
ya washe baki
"Shike nan fa Hajiya kin gama min ko mai wayaga Sule a hajji."
ya sheke da dariya.

Tafiya mai nisa sosai sukayi da ya kai awanni hud'u kafin suka shige dajin boka Mali.
sai da sukayi tafiya kusan na awa guda daga bakin dajin zuwa cikin dajin kafin suka faka a ginfin wata katuwar itaciya.
Umma Karima ta fito a cikin motar in da Sule direba ke zaune yana zaman jiran ta a cikin mota.
wani katon kogo dake gaba da itaciyar ta nufa.
a bakin kogon ta cire takalmarta da mayafin ta,
ta kunce d'ankwalin kanta duk ta had'a ta ajesu a gurin.
ta shige cikin doguwar kogon nan mai zurfi ba d'ankwali ba mayafi ba takalmi.
fad'i ta ke
"Gafara dai boka sannunka dai mai magance matsala ko wacce iri ce."
wani irin kazamin dariya aka kece da shi gaba d'aya cikin kogon yake amsa sautin dariya mara dad'in ji.
ya yin da ake fad'i
"Kinyi dogon nazari mu ke magance matsala, duk bukatar da kika zo da shi kin samu."
"Godiya nake boka godiya nake ubanmu maganin kukan mu,
tun da muka rike ka babu abun da muka rasa."
ta zube a gaban shi ta nad'e kafafuwa kamar mai niman gafara.
yana zaune a kan wata kujerar tsafi wani jan kyalle d'aure a jikinsa, yana rike da sandar tsafin sa.
suffarsa sam babu kyan gani.
ya mike tsaya yana cigaba da wannan kazamar dariyar mara dad'in saurara ya mika hannu ya d'aura a tsakiyar kanta da babu d'ankwali.
yana zazzare manyan idanuwansa munana masu ban tsoro.
zuwa can ya janye hannun nasa yakoma ya zauna kan kujerar sa yana fad'in
"Mun ga bukatar ki me kike so ayi musu?."

Ta gyara zama da sauri tana fad'in
"Yauwa boka Mali shugaban mu mai share mana kukan mu,
so nake a haukata Hajiya Fatima ta bazama duniya hauka na har abada babu warkewa,
da naso a kashe ta ne amma idan aka kasheta ai an mata gata ne a haukata ta kawai kada ta warke har a bada,
taje tayi ta wahala tana bin kwararo-kwararo bola-bola,
daga nan kuma ita yarinyar da take hannunta dole ta bar gidan,
dama zaman Hajiya Fatima a gidan shi ya zaunar da ita daga zaran ta haukace ta bar gidan dole itama ta bar gidan."
sandar da ke hannunsa ya bukashi kan wani kasa da ke tare a gaban sa,
yana jujjiya gwalagwalan idonunsa kan kasar sannan ya ke ce da dariya
"Kin samu bukatarki ta biya,
lallai tabbas Hajiya Fatima zata haukace,
hauka mafi muni,
zamu tura mata bakin aljani daga zaran sunyi ido biyu da ita to zance ya kare hauka tuburan zatayi shi mara warkewa;
sai dai wani hanzari ba gudu ba,
sashinta yana zageye da kariya irin na addu'o'in da take kullum safiya da maraice,
bakin aljani bazai iya tinkarar gurin ba zai iya konewa,
bari dai mu samo wata mafitar."
yakuma buga sandar sa yana juya ido can kuma ya d'ago yana cewa
"Mafita d'aya ce ta in da zaibi ya shige sashin nata,
dole ta sama zaibi bayan munyi masa shirin kariya daga konewa,
ya sauka a gurin najasa dole a band'aki zai sauka,
daga nan bazai iya matsawa ko ina ba, dole a gurin zai zauna yajirata har san da zata shigo bayi, daga nan kuma zance ya kare sai dai watan ta ba dai ita ba,
nan da kwanaki uku zamu tura bakin aljani bayan mun gama masa shiri daga kariyar konewa."
Chapter 50 · 0% Book details