Sashe 8
Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
A guje suka karaso parlour'n Mommy suna haki, ganin yadda suka shigo a hargitsi 'ya'yansu duk suka mike suna tambayar su me ke faruwa.
"Kada wani a cikinku ya sake yaje side d'in Fatima!."
cewar Mommy tana zama kan kujera gaba d'aya a firgice ta ke jikinta sai rawa yake..
Ajeemal ne yakaraso in da take yana fad'in
"Mommy wai mene ne kam naga duk kun firgice?."
"Ajeemal aljana wlh aljana ce ba mutum ba, mun shiga uku ankawo mana annoba cikin gida, wlh yarinyar can ba mutum ba ce aljana ce, Fatima takawo mana aljana gida, Hajiya Karima kinga abin da nagani kuwa?."
"Ni kuwa naga sihiri aljananci maitanci ido da ido, ko shakka babu 'yannan ba mutum ba ce."
Umma Karima da tsoro yakusa kasheta taja 'ya'yanta, suka koma side d'in ta, suka rufo kofa a kansu.
A b'angaren Mommy kuwa har ta d'aga waya zata sanarwa Hajiya abin da ke faruwa, ta tuna da gargad'in Daddy ta aje wayar jiki a sanyaye
tana ciza yatsa.
A b'angaren Umma Karima ma taso kiran Hajiyar sai dai tana gudun abin da zaije ya dawo, dan bata kaunar abin da zai gutsire mata igiyar aurenta, takan bi ko wace hanya wajen dakile faruwar hakan.
Bayan wata 5
Tun daga wancan ranar su Mommy basu kuma wani yunkuri a kan Feeryal ba,
Aunty kuwa ta dage wajen kula da rainon d'iyarta yadda ya kamata.
yarinya tana ta murjewa fatarta na dad'a kyau babu alamar maraicin uwa tare da ita, ta sami ruwan nono mai kyau da inganci.
tayi wayo sosai tayi mul-mul da ita.
har ta fara iya zama.
sosai Aunty ke kula da ita Daddy na bata gudumawa yadda ya kamata.
bata fita da ita ko ina ko side d'in Daddy zataje ba sosai take zuwa da itaba, takan barta wa Baba Rabi.
kaf fad'in gidan kuwa dama babu inda take shiga side d'in Hajiya Safiyyah ce kad'ai take d'an lekawa.
kowa na harkar gaban sa a gidan.
Yanzu duk wanda yazo gurin ta bata bari yaga Feeryal,
b'oyeta take a d'aki har sai ba'in sun tafi kafin tafito da ita.
sabo da gujewa maganganun da ake akan ta, dan duk wanda ya ganta sai ya ce wuuu a'ina ta samo wannan mai kalar aljanu sam batayi kama da mutane ba.
kyawun ta ya yi yawa.
Aunty ce tsaye cikin kichin bayan ta gama shiryawa Daddy abincin sa dan yau zai dawo gurin ta.
baba Rabi tana ta goge-gogen in da suka b'ata.
Aunty ta dubi Baba Rabi tana fad'in
"Bari naje nayi wanka kafin rikicacciyata ta tashi, idan kazarnan ta kara zafi a ciro ta kada ta kone."
"To Hajiya." Baba Rabi ta amsa tana maida komai wajen zaman sa.
Aunty ta fito daga kichin ta nufi bedroom d'inta, a hankali ta tura kofa cikin kasa da murya take fad'in
"Allah yasa bata tashi ba har sai na gama komai."
ta maida kofar a hankali ta rufe.
idanunta a kan inda bed d'in Feeryal yake,
tana fata Allah dai yasa bata tashin ba.
da d'an mamaki take kallon cikin d'akin, ganin babu gadon nata gaba d'aya a cikin bedroom d'in.
"Ta ina tayi ko ta tashi garin rarrafe ta fad'o a gado ne, to ina ma ganon yake?."
ta had'a tambayoyi wa kanta tana rarraba ido.
da sauri ta d'aga kafa tana kokarin karasawa cikin d'akin.
wani irin tsinkewa gaban kirjinta ya yi tayi baya da sauri, jikinta na wani irin cirawa tsoro da firgici suka dirar mata lokaci guda. gaba d'aya jikinta ya d'auki b'ari.
Hango gadon Feeryal ya tashi sama tamkar ana lilata gadon yana juyawa shi kad'ai sai kyakyata dariya take.
kamar yadda take mata wasa take b'allewa da dariya haka nan take yi, har tana mika hanu alamun a d'auke ta.
Cikin kad'uwa da firgici Aunty takuma yin baya da karfi ta furta
"Innalillahi'wa inna'ilaiihirraji'un!."
ai ko kamar jira ake tayi magana.
a hankali godon yashiga saukowa har ya diro kasa tamkar an dai-dai ta zamansa a gurin zaman sa.
Karaf Feeryal ya saukakan Aunty,
ganin Aunty tafara mika hanu ta d'auke ta, Aunty kuwa cikin hanzari ta bud'e kofa jiki na b'ari tayi waje cike da d'inbin tsoro.
Tana jiyo kukanta bata ko waiga ba,
a parlour ta tsaya tana maida numfashi, tare da dafe kirjinta dake dukan tara-tara!.
addu'a tafarayi wanda duk yazo bakinta yi take tana saukewa.
a matukar tsorace tashiga kwad'awa Baba Rabi kira.
"Baba Rabi Baba Rabi!."
da sauri Baba rabi ta fito tana amsa kiran, ganin yadda gaba d'aya ta rasa nutsuwarta Baba Rabi tashiga tambayar ta ba'asi.
bata iya magana ba sai nuna kofar bedroom d'inta take da hannu.
da sauri Baba Rabi ta nufi kofar bedroom d'in jiyo kukan Feeryal daga ciki.
dan tagama tsinkewa wani abun ne ya sameta, ganin yadda gaba d'aya Aunty ta firgice.
Tana shiga d'akin ta hangoto zaune a kan gadon ta tana kela kuka da mika hanu tana niman mai d'aukarta.
da sauri ta karaso gareta ta sa hanu ta d'auke tana fad'in
"Me ya same ki Feeryal Ammie'n ki ta shiga firgici? kuma dai gaki lafiya lau nagan ki, to ko wani abun tagani cikin bayi?."
Tayi waje da ita tana jijjigata.
ta taho in da Aunty take tsaye zuwa yanzu nutsuwa yafara shigarta da taimakon addu'o'in da take ta yi.
ta mika mata ita tana fad'in
"Hajiya wani abin kika gani ne cikin band'aki akirawo security suzo su cire?
dama da an fara zafi wad'an nan muggan igiyoyin kasan zasu fara niman gurin sanyi su rika fitowa daga mab'uyarsu suna shigewa ramuka ta baya suna shigowa mutane ta cikin toilet."
Ido Aunty ta kurwa Feeryal da tsoron ta ya kamata
batare da ta karb'e ta ba, itako sai zillo take tana mika hanu tana so ta taje gurinta.
"Rike ta naje na kirawo su suzo su kashe kada ya shige wani gurin a rasa shi."
Baba Rabi ta kuma fad'i tana dad'a mika mata ita.
Ja da baya tayi idon ta a kan ta tana kallon cikin kwayar idanunta farare soll masu sananin farin haske, kwayar idanunta madadin fari da d'igon ash, shi fari ne tas da d'igon green da d'igo-d'igon gold and ash a had'e.
yanzu kuwa yadda'a sauyawa har wani kore'kore yake ga duk wan da yaga yanayin sai ya bashi tsoro.
Ido Aunty ta rumtse tana kuma bud'e su a kanta, sai taga kalar ya ragu ya koma irin kalar idanunta.
"Baba Rabi bakiga komai cikin d'akin ba?."
"Babu komai cikin d'akin nan hajiya, sai dai naje na kirasun suzo su bincika kin san igiyar kasa basa tsoron mata."
kai Aunty ta girgiza ta ce
"Kar ki kirasu babu komai kawai na tsorata ne."
Baba Rabi zata kuma magana Daddy ya shigo.
Da sauri ta d'an rusna tana miko gaisuwa.
ai ko Feeryal na ganin sa tafara miko masa hanu tana wage baki.
ya karb'e ta yana amsa gaisuwar.
da sauri Baba Rabi ta wuce kichin domin kammala aikin ta.
Daddy ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun parlour'n yana yi wa Feeryal wasa sai b'arkewa da dariya ta ke.
har lokacin Aunty na tsaye jikinta a sanyaye.
"Ya dai Ammie'n Feeryal wani abin ne?."
cewar Daddy yana duban ta.
kai ta girgiza jiki a sanyaye ta ce
"A'a." ya jinjina kai yaci gaba da yiwa yarinyar wasa.