← Book details Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 52

Sashe 1

Feeryal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🌺🌺 *FEERYAL* 🌺🌺

*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*

( _Book 1_)

~Free page~

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*Bismillahirrahmanurrahim*

🅿�1

Sassanyan iskar damina ne ke kad'awa ya yin da hadarin damina yayiwa sararin samaniya kawanya.
yadda hadarin ya yi bak'i ana sammanin ikon Allah ta kasance, a'iya yin ruwa mai tarin yawa.
katon teku da girman sa yawuci misali yacika ya tumbatsa.
ruwa na gudu na k'ugi ga dukkan alamu tuni ruwa ya sauka daga can nesa da in da kogin yake.
wani irin k'ara ne mai matukar firgitarwa tamkar saukar aradu,
yakarad'e ilahirin sararin samaniya.
ya yin da wasu irin halittu suka bayyana sukayiwa koginnan kawanya daga sama.
daga can tsakiyar halittun manyan aljanun da sukayiwa kogin nan kawanya,
wani irin haske ne tamkar gilmawar walkiya ya bayyana a tsakiyarsu,
wani aljani mai d'auke da fuffuke yana rike da wani kwando, a hanunsa yasaki kwandon cikin tsakiyar ruwan yafad'o cikin katuwar tekun nan,
ji kake banjammmm!.
kwandon ya lume cikin tekun can karkashin tekon, mai matukar zurfi.
dawasu abubuwan ban tsoro masu tsananin firgitarwa.

Akan wani katon babban kejin karfe kwandon nan ya fad'i akai.
nan da nan jaririyar da ke rufe cikin kwandon ta calla kara, dai-dai lokacin da kwandon ta bud'e tayi gefe jaririyar tafice ciki tafad'a kan kejin karfen nan, mai tabaibaya da wasu sarkokin karfe masu matukar karfi,
wanda ko da injin yanka karafu ne sai ya yi da gaske kafin ya iya fasa sarkokin da ke tabaibaye da jikin kejin karfen, ba mutum ba ko aljani sai ya shirya.

Kara jaririyar takuma callawa tana wutsil-wutsil da kafafunta,
d'isss! haka hawayen idanunta ya d'iga akan kejin karfen nan.
nan take kejin ya yi wani irin kara tare da tarwatsewa tamkar narkakkiyar dalma,
wacce taji wutan ziga ta cikin karkashin
kasa ta dawo tamkar roba, ba karfe mai tsananin karfi ba.

Nan wani dattijon Aljani ya bayyana d'aure da saurkoki a jikinsa dai-dai lokacin da hawayenta na biyu yakuma d'iga ajikin sarkokin dake tabaibaye ajikinsa, sarkokin suka tarwatse gaba d'aya daga jikin dattijon aljanin nan.
da sauri cikin azama yatari jaririyar datake kokarin dad'a lumewa cikin karkashen tekun,
da gaba d'aya tekun ya yi wani irin hargitsewa da abubuwa masu matukar ban tsoro da firgitarwa.

Wani irin tafarfasa koginnan yake tamkar ana tafasa narkakkiyar dalma.
tuni sassanyar iskar dake kad'awa agun yakoma zazzafa.
tashin hankali ba'a sa masa rana, a wannan lokacin ba iya yankin kogin ba duniya gaba d'aya ta girgiza.
tuni halittun dake cikin tekun nan suka fara mutuwa, dabbobin dajin da suke yanki da kewayen gurin.
wasu sun hallaka wasu kuma sun zube ƙasa suna birgimar mutuwa.
'yan bori matsafa bokaye malaman tsubbu mushirkai dake fad'in duniya gaba d'aya, wannan rana tazame musu bakar rana mafi tashin hankali a gare su.

Wani irin zabura boka Mali ya yi lokacin da
tukwanan tsafin sa suka fashe, suna fitta wani irin hayaki mai razanarwa had'e da sauti mai firgitarwa.
tsabar tashin hankali a take agun yafad'i sumamme.
hakan ne ta kasance ga ko wani mushirikin dake fad'in duniya.

Da sauri dattijon aljani Matip ya gyara rikon jaririyar nan, kana yayi saurin durkusawa kasan tekun ya burma hanunsa cikin karkashin kasa da karfi irin na jinnu.
nan take jikinsa yashiga kakkarwa ilahirin jikinsa yashiga fidda hayaki tamkar ana zuba masa garwashi na wuta.
ya yi wani irin kara tare da zaro hanunsa, ya dunkule abunda ya ciro daga karkashin tekun na, da karfi cikin hannunsa.
jikinsa nawani irin jijjiga, cikin karaji da amon sauti irin na jinnu yake fad'in
"Ni kad'ai zaku cutar kada ku zalinci wad'anda basujiba basu gani ba, meye laifin bil'adama salihai da dabbobi? meye laifin aljanun da basu taka mukuba,
har idan ina numfashi bazan tab'a bari kucutar da kowa ba, ku da kanku zaku zalunci kanku da bil'adaman da suke biye muku kuna b'arna a doron kasa, babu wanda zan kyale shi cikin ku!!."

Ya matse tulun daya ciro daga karkashin kasan tekun wanda cikinsa sai tafasa yake yana fidda bakin hayaki har sai da ya fasashi da hannunsa, ya tarwatse wan da hakan yayi sananiyyar haifar da ambaliya nan take.
Aljani Matip ya zube kasa jaririyar dake rike a d'aya hanunsa tasub'uce tafad'a karkashin kasan tekun.
yana kallonta sai dai ina baya da ikon iya ceton ta dan ba karamin galabaita ya yi ba,
duk jikinsa sunyi rad'a-rad'a ya kokkone da wutar tsafi dake ruruwa cikin tulun tsafin daya fasa.
ido ya rumtse a wahalce yana kallon yanda wacce tasanadiyyarta yasami tsira da kub'uta daga zalincin da akayi masa tsowon shekaru masu yawa, yake d'aure a karkashin tekunnan.
tazo ta ceceshi sai gashi yana ji yana gani zata halaka bashida ikon iya taimakon ta.
muryoyin yaran biyu Aljani Matip yaji a kunnen sa suna fad'in
"Shugaba yakub'uta shugaba ya kub'ata."
dakyar ya iya furta
"Ku ceceta kada ku bari ta halaka."

Cikin kankanin lokaci tekunnan yafara dai-daita, dabbobi da halittun da suka suma kowa yadawo cikin hayyacinsa.
duniya ta dai-daita daga firgici da ban tsoron da tashiga cikin kankanin lokaci,
iska mai sanyin dad'i daya juye yakoma zafi yadawo sassanya mai dad'in gaske komai ya dai-daita tamkar komai bai faruba.

Gudu motor take ga dukkan alamu wad'anda suke cikin motar sauri suke su isa gida, gudun kada ruwa ta tare su.
wani kamilallen dattijo ne mai cikar haiba da cikar kamala, ke zaune a mazaunin direba, ya yin da gefen sa wata farar mata kyakkyawa wanda a kalla shekarunta zasu iya kaiwa 30.
ke zaune cikin nutsuwa da kamala.
Alhaji Abubakar Fiya kenan shahararren d'an kasuwa ne mai tarin dukiya, wanda ya ke d'aya daga cikin nagaba-gaba a masu kud'in kasarmu.
shi da kansa yake jan motar,
al'adar sa ne har idan da abar kaunarsa Hajiya Fatima zaifita.
idan har ba tafiya mai nisa zasuyi ba to da kansa yake jansu a mota, baya bukatar direba a sakanin su.
duk da kuwa yau tafiyar tasu mai nisa ne bai sashi sanyo diteba cikin tafiyar tasu ba.

Yankin tekun Matip yamma da kogin hanyar tsako gajeren hanya, sakanin yankin da babbar tekunnan Matip tafiyar kimanin kilomita dubu ne.
daga cikin dajin tekun Matip da hanyar mota da akayi ta saman kogin daya shigo har ta gefen gari yasami hanyar wucewa,
inda akayi masa gada motoci suke wucewa idan hanya tabiyo dakai ta gurin.
ko yanzu ma hanya ce tabiyo da Alhaji Abubakar Fiya da matarsa Hajiya Fatima.

Ido Hajiya Fatima ta zubawa katuwar kogin nan dasuka zo daf dashi zasu wuce tasaman gada, yana wani irin haniniya, yana ƙugi yana wani irin tsalle tamkar zai haura saman gadar.
daga can gefen gab'a, wani irin haske ne ya bayyana a gurin, daga bisani hasken ya disashe.
da sauri ta dubi mai gidan nata tare da fad'in
"Daddy kalli can ka gani."
tayi masa nuni da hanu ta bakin gab'a.
ido ya zubawa gurin sosai jaririya acikin kwando tanata zabga kuka ga ruwa yana d'an tafiya da ita, sai shure kafafu take.
da sauri Hajiya Fatima ta ce
"Daddy ruwa zai tafi da ita tsaya dan Allah mu taimaka mata kada ta mutu acikin ruwan nan, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un me yakawo jariri cikin wannan ruwa kuma,
kai duni ina zaki da mu."
da sauri ya gyara parking a gefen titi har suna rigi-rigen fitowa.
da gudu hajiya Fatima tayi bakin ruwan ganin kwandon yana cigaba da tafiya cikin ruwan tana fad'in
"Daddy duba kaga ruwa zai tafi da shi."
"Dakata Hajiya kibi a sannu wannan ruwa yana da had'ari bai kyale 'yan gari bama bare ba'i."
suka jiyo muryar wani matsinci a bayan su.
da sauri ta waigo tana fad'in
"Dan Allah ku riketa kada ruwa ya tafi da ita."

Alhaji Abubakar ya ce
"Ki nutsu Fad'imatu kin ji ance ruwannan yana da had'ari kibari y'an gari su shiga,
bawan Allah taimaka dan Allah kaciro sa yana bukatar taimako."
yakarasa maganar yana duban matsincin nan.
kai matsincin ya gyad'a kana ya aje abubuwan kamun kifinsa ya fad'a ruwan ya d'auko kwandon yafito.
dasauri har suna rige-rige wajen karb'ar kwandon.
dukkaninsu ido suka kafawa jaririyar dake cikin kwandon tana ta mutsu-mutsu da y'an kananun kuka,
da mamaki dukkanin su suka kalli junansu har da matsincin nan, ganin halittar dake cikin kwandon.
kyakkyawar jaririya wacce kyanta bazai tab'a misaltuwa ba kyawun da duk wanda yagani sai ya firgita shi.
murya na rawa
dasauri Hajiya Fatima ta dubi mai gidan nata ta ce
"Mutum ce kuwa?."
Alhaji Abubakar da shima yashi tantama sosai ya ce
"Ni ma dai tunanin da nake ke nan, kawai mu maidata cikin ruwa tayi tafiyar ta, wata kila ma tana tare da iyayenta ne."
yad'aga murya da karfi yana kallon cikin ruwan tare da cigaba da fad'in
"Kuna dai gani ba da niyyar cutar da d'iyarku muka d'auko taba sai dan tunanin ko jinsin mune ita, gudun kada rayuwarta ya salwanta,
yanzun nan zamu maida muku abunku ku gafarce mu."
Alhaji Abubakar ya dubi matsincin nan ya ce
"Taimaka ka maida musu da ita ka kuma basu hakuri bada niyya mukayi ba."

Kai mutumin ya girgiza sannan ya ce
"Alhaji bana tunanin aljana ce wannan dan kuwa da lokacin dana shiga d'auko ta danaga wasu alamu,
a nan wurin ansha samin yara irin haka suna tafiya a kan ruwa sai dai yawanci ba a samin su da rai,
wad'anda ake samu da ran basufi a kirgaba, nafi tunanin wannan mutum ce,
Allah ne ya ketar da ita dai kawai, ko had'arin jirgi ko masu raba iyaye da y'ay'ansu."

Alhaji Abubakar ya girgiza kai cike da tausayawa ya ce
"Allah ya saka miki idan har makiya ne suka rabaki da mahaifanki, idan kuma rabuwar ta Allah ce sanadin had'ari Allah yajikan mahaifanki, idan kuma suna raye to Allah ya bayyana su cikin gaggawa."
Chapter 1 · 0% Book details