Sashe 9
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mai matsifsr ƙamshi da saka natsuwa..... Wuraren 8:46 Abdulmalik ya shigo gidan, "Kaka ina kwana, " Lafiya lau Abdulmalik" " Kaka baƙin basu iso ba?" "Nunfashi Kaka taja kana ta fesar,"muma zaman jiran su muke Abdulmalik" "Gashi har 9 ta kusa ni zan waje kasuwa" wani irin Kallo Maryam ta watsa mishi" " Ai kam gaskiya ne ba'a san ranar zuwan su ba ga abincin kanan" " Nagode Kaka!" A tsanake ya soma cikin Abinci bayan ya kammala ya wuce, " Wai wannan fushi duk na miye haka cewar Kaka" turo ɗan ƙaramin bakinta tayi "Kaka ba Ya Maleek ba ne yaƙi tsayi ya ga su Haydar" Kaka tayi murmushi kana tace," to ai ba laifinshi bane sune basu iso da wuri ba kuma jiya Saida ya gaya Miki idon basu zo da wuri ba zai wuce kasuwa kike ce kin yadda to miye kuma abin ɓata rai" "Wallahi ba ruwa dashi bari ya dawo" dai dai lokacin sukaji tsayuwar mota a ƙofar gida, Kaka ta sauƙe sassanyan Nunfashi, can ƙasan maƙoshi tace "Alhamdulillahi Allah na gode ma da ka kawo su Lafiya" Cikin tsiwa Maryam tace Kaka wallahi sun iso" da sauri ta mike har tana batun faɗuwa, "Mamana kiyi a hankali karkiji ciwo!" A hankali ta Lumshe idanunta kana ta buɗe akan fusakarsa kyakkyawan dottijon dake tsaye a harabar gidan dogo ne fari sol da sauri Maryam ta iso wajensa tare da rungumeshi "Abba sannu da zuwa!" "Mamana! Kina lafiya!?" "Lafiya lau Abba!" A hankali ta janye jikinta daga nashi"Abba ina su Haydar!?" dai dai lokacin suka shiga cikin gida su Ukku sanye shedda mai matsifsr kyau da tsaya sosai kayan sukayi masu kyau, da sauri maryam ta iso wajensu ta rungumesu gabaƙi ɗaya tana faɗin ,"Ƴan ƙanne na! Mai ɗan girma cikin su ya harareta....... duka shekara nawa kika bamu? ya ƙara sa maganar cikin tsokana, " Koma dai nawa ne ai na girmeku...... A hankali ya nufi inda Kaka take zauna ya durƙusa har ƙasa cikin girmamawa ya gaishe ta,"Mun sameku lafiya Mama!" Cikin sanyi Murya tace ," Lafiya lau Alhamdulillahi" Haka suka zage Kaka gaba ki ɗayan su Kana suka Gaisheta, cikin tsananin farin cike ta bi su ɗaya bayan ɗaya tana shafa kansa tare da sanya musu Albaka, "Malam Gwani ya Makaran?" "Lafiya lau Kaka" "Masha Allah ya maman ku?" "Kaka Momy bata da lafiya! komai bata iya yi sai masu Aiki sunyi mata" da sauri Kaka ta maida Kallonta ga Abdullahi, murya a dishace tace ,"Gaskiya ne abinda Malam Gwani ya faɗa? Kai a sunkuye yace ," Jikin da sauƙi sosai" " haba Abdullahi me saya tun lokacin baka sanar dani ba!" " ki gafar ceni Mama" "Ya jikin nata yanzu mike da munta kuma?" "Cikon sugar ne Mama" "Allah ya bata lafiya" ga baƙi ɗayasu suka Amsa da Amin, "kira min Ita mugaisa ba musu ya kira, Kaka tayi mata ya jiki basu wani jima sukayi Sallama Kasan cewar ba shaƙuwa a tsakanin su, dai dai lokacin Atiku Direba ya shigo gidan dauke da ledoji niki niki, cikin girmamawa ya gaida Kaka kana ya fice daga gidan, "Maryam tashi ku kai mishi abinci gaba ki ɗaya su suka miƙe zuwa kicin suka ɗauƙi Abinci kana suka kai mishi. Koda suka dawo Kaka ta jera masu Abinci haka suka zauna cikin Abicin cikin natsuwa da kwanciyar, sai sontin Abinci suke, Bayan suka gama cikin Abinci suka tattara kayan zuwa kiciin, Kaka da Abdullahi suka ci gaba da hira yaushe gama, nan yake faɗa mata irin ciki gaban da yake samu a kasuwanci su dukiyar Maryam ma sai haɓa ka take, Kaka ta yi farin ciki sosai da wannan maganar, A ɓangaren su Haydar kam sai wasar su suke, gwanin burgewa, Ranar dai haka suka kasance cikin tsantsan farin ciki, sai gab da maggariba sukayi Kaka Sallama kana suka wuce, cike da kewar zuna, Kaka ta haɗa masu kayan tsaraba irin na kyauye, lokacin da suka wuce Maryam Hadda kukanta, har ga Allah tana son Kasan cewar da ƴan Uwanta, Har bayan Isha'i fusakar a tsuke, Koda Abdulmalik ya shigo gida Kaka na ɗaki, ko inda yake Maryam bata kalla ba, "Cikin sanyi Murya ya kira sunanta "Maryama ta!" Miƙewa tayi tare da barin wajen, a hankali Abdulmalik ya sauke sassanyan Nunfashi tare da fesar da Numfashi, A karo na biyu ya sake kiran sunanta "Maryama ta! Maryama ta!! Maryama ta!!!" tuni ta shige ɗaki , durƙu sawa ya yi a wajen cikin zazzaƙar Muryar shi mai cike da natauwa ya soma rare mata wakar Umar M Sharif ( Maryama) wanda duk lokacin da tayi fushi ita yake rera mata, 🎶" Ina kike Masoyiya! na duba gabas ban ganki ba na duba Arewa ban ganki ba naje kudu ban ganki ba naje Yamma ban ganki ba! Ehya ya ya oh yah yah yaushe zaki yaushe zaki zo! Yaushe zaki zo Masoyiya!...... naga ƴan mata iri kyawo baza su fiki ba! Kalaman so kashi kashi banji salo irin naki ba kyan halinki ba'a faɗa baki hanya wuce gaba gata nan tafe🎶gata nan tafe gata nan tafe Masoyiya 🎶gata nan tafe tana zuwa!🎶 Maryama zo Maryama zo Maryama zo Masoyiya!!! 🎶 Kinza ma Ni nazama ke komi zanyi done Saida ke banci abinci inbabu ke Nagode Allah daya bani ke! Maryama Maryama ta iya kalliya Maryama mai kyau da dariya Maryama!!! Lala lalaye Maryama zo Maryama🎶💖💋 Yana mai ƙarshe baiti ta fito ɗakin a guje ta faɗa ƙirjinshi ya rungumeta da karfi Ya runtse idanunsa "Ya rabb" ya faɗa a ƙasan maƙoshi, Kanta ta manya a ƙirƙijinsa tare da sa hannuwanta duka biyu ta zagaye ƙugunshi tare sakin sassanyan Ajiyar zuciya, Runtse idanu sukayi lokaci ɗaya tare da sakin sassanyan Ajiyar zuciya, "Maryama ta!" Kin Dena fushin? a hankali ta gyaɗa maishi kai, a hankali ya janye ta daga jikinshi, lokaci ɗaya suka sakarwa junansu Murmushi. "Ya Maleek kana fida su Abba suka iso ta karasa maganar cike da Shogoɓa, "Ayya Maryama ta Allah bai kadda zamu haɗu ba! Amman Insha Allah wata rana zamu haɗe a tare!" "Abdulmalik an dawo cewar Kaka, "Ehh Kaka na dawo ya baƙi" "Lafiya lau yanzu mukayi waya har sun isa gida" "Masha Allah, Allah ya wutar da hajjiya Allah kuma ya basu ladan zumunci" "Amin ya rabbi Abdulmalik" ga abin cinka nan, tare suka ci da Maryama suna ci yana tsokanar ta har suka kammala, kana sukayi Karatu, nan Kaka ta kawo musu kayan marmari da Abba ya kawo musu, Abdulmalik yana ci yana. Lumshe ido Allah ya sani yana son kayan marmari, bayan sun gama shan kayan marmarin ya wuce gida..... A hankali Rayuwa taci gaba da shuɗewa , tuni su maryam sunyi sauka aka haɗa musu gagarumar walima kusan komi Abba ne ya ɗau nauyi komi ranar walima Malam Gwani da iyayen Maryam sunsha Addu'a, Ranar walima su Haydar kaɗai suka samu damar zuwa, Abdulmalik ya taka muhimmiyar rawa a wajen walimar, haka tare ya tashi lafiya, A ɓangaren kubra ko jikin tana sai ƙara tsauri yake, wani lokacin har gado aka bata Asbiti, gabaƙi ɗaya Abdullahi baya cikin Haiyacinsa, kullum sai kaka ta kira taji yakinta..... Haka dai kwanaki suka ci Baga da shuɗewa..zuwa yanzu Maryam ta fara girma, Kwance a take a tsakiyar gida sai juyi take,"Kaka ƙirjina ciwo yake har yanzu Kaka wlh gobe idon naje makaranta sai na rama, "Kiyi Haƙuri tunda tace ba da saninta ta buge ki ba, daman idon ana ƙidan degin hake abu kaɗan saiya taɓa wajen, nidai wlh Kaka saina rama itama gidan dengi take taji irin zafin da nakeji!" "Ohni Mairamu" cewar kaka shegen jini nin tsiya ginga tafiya ta, a hankali Kaka ta nufi ɗaƙi, dai dai ya Abdulmalik ya shigo, da sauri ta mike zaune tana faɗin "Maleek kalli Ubaidah ta ɓararmi da ƙidan dengi na tayi magana tana ƙoƙarin buɗe gaban rigarta da sauri ya dakarta ita ta hanƴar daga mata Hannu, "Ya Maleek duba ka gani wlh ciwo suke min da sauri ya runtse idanu wansa cikin wani irin yanayi da shi kanshi ba zai tantance wani iri ne ba " ya Salam" da sauri ta maida rigarta cikin tsiwa tace ," Ya Maleek zafi suke min!" "Ina Kaka?" "tana ɗaki" kai tsaye ya nufi ɗakin ya gaishe Maryam ta bishi da Harara, bayan sun gaisa tare suka dawo Tsakiyar gida suka zauna kana yaci Abinci, bayan ya gama ta kalli Kaka cikin sanyi Muryar yace "gobe zamuje Kano tare da oga" " TOH Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya" Amin Kaka, dai dai lokacin wayar Kaka tayi Ringing a hankali ta ɗaya wayar "Abdullahi Ya gida lafiya? Ya nayi muryar a haka? Ya jikin Kubra? Daga can ban ɓangaren Abdullahi ya sauƙin Nannauyan Ajiyar zuciyar murya a dishace yace ," Kaka jikinne ya kara tashi sosai yanzu haka muna Asbiti, "Subuhalillah Allah Ubangiji ya bata lafiya "Amin" "Gobe ka aiko Direba yazo ya kaimu na ganata, "TOH Mama sai kushirya da wuri Allah ya kawo ku lafiya, " Amin ya rabbi, kana sukayi Sallama, kaka ta sauke Ajiyar zuciya kana ta fesar da Numfashi mai Zafi, "Abdulmalik gobe muna zamuje Kano matar baban Maryam ce ba lafiya yanzu haka suna Asbiti, "Allah ya bata lafiya Kaka yaushe zaku dawo kenan goben zamu dawo Insha Allahu, Nima ina tunani kwana ɗaya zamu kana mudawo, " TOH Allah ya dawo damu lafiya Amin Kaka" Maryam ha kawai gabanta ya riƙa faɗiwa, Murya a dishace tace "Kaka Nikam Bazan je ba,"saboda me? "Bakomi Kaka" "Aiko dole kije" Jiki a Mace Abdulmalik yayi musu sallama ya wuce gida, Nan Kaka tashi haɗa .musu kayan su, Washe gari tunda sassafe Abdulmalik ya shigo gidan tuni su kaka ma sun shirya direba kawai suke jira tare suka karya kana Abdulmalik ya yi musu Sallama ya wuce har ya kai baƙin ƙofa ya dawo "Kaka yau kike zaku dawo ko?" "in sha Allahu Abdulmalik yau ko gobe duk yadda hali ya yi bazamu jima ba kodon makarantar Maryam koda ka dawo baka gobe baku da woba zan a jema makulli kodon dafa abinci " Toh Kaka Allah ya tsare" "Amin" "Maryama ta! Bazaki min rakiya ba cikin mutuwar jiki saba ta san namiye ta rakashi har ƙofar gida har ya tafi ya kira sunan sa "Ya Maleek"