← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 54

Sashe 27

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

gidan su, kana Sultana ta kalleta,"Allah kika ƙara min maganar Shi a mota zai dai na sauke ki a hanya, "haba Daughter Meya yayi zafi haka gama Insha Allahu da mota na zanjo daman ɗazu koda na fito aba'a wanke taba, "Nadai gaya Miki" yana kai ƙarshen Maganar ta wuce, a hankali Jidda ta sauke sassanyan Nunfashi kana ta nufi cikin gida... Tunda suka baro cikin Asbitin ɗin ya kwantar da kansa jikin kujera yayi shiru idanunsa dake da cikar baƙin gashi da gira a sama suna a lumshe. Sai faman juya zoben hannunsa dake a hannunsa na dama. Duk abinda ya keyi drivernsa na kula ta cikin mirror, Haka dai suka cigaba da tafiya kowa da abinda yake saƙawa a cikin rai. Gashi mahaukacin gudu yakai Tunda 6pm tayi kiran Mommy da Daddy ya fara shigowa a wayarsa, sai dai ko sau ɗaya bai amsa masu ba ya share, sai ma kwanciya daya gyara cikin lallausar kujerar motar ya cigaba da latse-latsen laptop ɗinsa har yanzu da takaicin Sultana a ransa. Ƙarfe 7:20 suka iso gida Tunkan su gama dai-daita parking idanunsu suka sauka akan Mommy da Ihsan dake ta faman kai kawo ta barandar saman bene. Sai dai ganin shigowar motocin tuni tabar wajen da alama zata fitone. Tare suka iso wajen harda su Salma da gudu suka rungumeta tare da faɗin,"Sannu dazuwa Ya Sultan" Ihsan ko wani irin kallo take binsa dashi, a hankali ya janye su daga jikinsa ya nufi wajen Mahaifinyarsa, "Sultan ya Aiki?" "Alhamdulillahi Mommy Ina Daddy?" "Yana masallaci" "Ya Sultan sannu da zuwa Ihsan ta faɗa cikin sanyi Muryar, "Lafiya" yaba Amsa, kana ya wuce cikin gida, yana zame baƙar jacket ɗin jinsa tunkan ya buɗe. Ya riƙeta a hannu ɗaya sannan ya ƙarasa ya murda handle ɗin ƙofar ya tura ya shiga. Fes ɗakin yake shima, yanata tashin ƙamshin fresheners data haɗe da turaren da yake amfani da shi. Jefa jacket ɗin yayi saman gadon ya ƙarasa gaban mirror yana ajiye wayoyin saman mirrorn. Zama yay a stool ɗin gaban madubin yanata faman yamutse fuska dan yunwa yakeji, sai da ya cire takalman ƙafarsa da safar, farar ƙafarsa dake fes ta bayyana kafin ya miƙe kansa tsaye ya nufi toilet Yana shiga aka fara knocking ƙofar falonsa, amma sai ya share ya cigaba da abinda yake a ciki. Anyi kusan sau uku sannan aka bari. Ya ɗauki tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe Milk color. Hannunsa riƙe da ƙaramin towel yana tsane sumar kansa da kallo ɗaya zakai mata ka fahimci tana masifar lasar kuɗaɗe kodan ƙyawun da take dashi ga mai kallo a ido balle kuma wanda ya taɓa. “Sultan! Buɗe min ƙofa”. Ya tsinkayo muryar Mommy tana faɗa cikin yaren fulatanci da tun zuwansa gidan ta fahimci yanaji da ɗan buga ƙofar yanda tasan bazai takurasa ba. Gefe ya karyar da wuyansa yana yamutsa fuska da yarfar da hannayensa duka alamar shifa an takura masa. Fuskarsa cike da takaici yaje ya buɗe mata tare da juyowa a binsa batare da ya tsaya saurarenta ba. Ƴar dariya tayi abinta, dan ko ɗan hakan bai dametaba, tasan ya gajine matuƙa, shikuma idan ya gaji to lallai sannan baƙin ransa ke ƙara hauhawa, kowa kuma yimawa yakeyi har ita da Daddy. Ƙarasawa tai inda yake tsaye a gaban mirror yana cigaba da tsane kansa. Kama hannunsa tai ta zaunar, ta amshi towel ɗin ta cigaba da goge masa kan tana kallonsa ta cikin mirror fuskarta washe da murmushi. Shiko ya ciskule tasa kamar zai fasa ihu. Sai da ta tsane masa kan tas kafin tajawo hand dryer ta jona a jikin soket ta fara busar masa da shi. Ajiye dryer ɗin tayi da jan hancinsa tana faɗin, “Nasan wannan fushin bana komai bane sai yunwa da gajiya Taso kaje kaci abinci ka kwanta ka huta. "Mommy bari nayi sallalolin" ya faɗa fuska a tsuke, Mommy tai Murya kana ta fice daga ɗakin, Saida ya yi kana ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ya wuce palon duk suna zaune a palon, Daddy L "Ma sha Allah" "Taso muje kaji Abinci, karkamin Kuka, cewar Mommy,gabaki. Suka wuce Darning a tsanake suka soma cikin Abinci.... tun kafin ta iso mai gadi ya buɗe mata gate cike da kwarewa ta danna hanci motar cikin gida tana gama Parking ta fito, mai gadi na rufe gate wani yaro ya yi knoking, "Gashi a ba Sultana, ba musu ya karɓa ya nufi wajen Sultana dake ƙoƙarin shiga cikin gida, "Madam gashi akace a baki 🎁abinda ke hannunsa yamiƙamata Ido.Sultana tazaro waje, "Baba nifa?. "Eh ked'in, cewar Baba. Karɓa Sultana Tayi tabud'e, 💐filawa ce mai k'amshin tsiya aciki, saikuma turare mai masifar kyau da ƴar ƙaramar takarda ta zaro anrubuta. _for you! my Sweetheart_....✍️✍️ _More Comments and share_ *Sadeeya Ka'oje ce* 💋✍️ *DR SULTAN* (A heart touching love story)
Chapter 27 · 0% Book details