← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 54

Sashe 54

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

mata a kumatu, ta kwantar da kanta bisa cinyar Kaka tana jan ajiyar zuciya a jajjere. Dauriya kawai Kaka keyi dama, taja ɓoyayyen ajiyar zuciya da girgiza kanta tana kallon Sultana. “Ke kuma me ya sameki? "Kaka don Allah ya gaya Abba bana son Auren, A aura masa Meena ko Ihsan harda Jidda ma idon yana so!" Sosai abin ya basu dariya, cukuykuye ƙafafunta tana kukanta, "Kaka wallahi banaso Sultan!" Hawayen da tun ɗazun take haɗiyewa ne suka silalo saman kumatunta a hankali. Ta sake matso hawayen masu zafi tana jan ajiyar zuciyar da har jijiyoyin wuyanta saida suka miƙe “Haba Sultana kukan ya isa haka mana, ko an miki wani abune?”. Kanta ta girgiza tana sauke ajiyar zuciya a jajajjere. Hannu tasa ta share hawayenta, cikin rawar murya tace, “Mami wallahi bana son Auran, "Sultan ɗin ne baki so!!" kanta ta girgiza mata tana haɗiyar zuciya dajan numfashi. Mami ta sauke Nannauyan Numfashi tana girgiza kai, hannu ta ɗaura kan haɓarta ta ɗago fuskarta. “Kalleni Sultana”. A hankali ta ɗago manyan idanunta da launinsu ya koma Jaa, gashi sun kumburo saboda kukan data sha ta saukesu akan Mami ”. “Kukan ya isa haka kinji Mamana, kicire komai a ranki babu abinda zai faru sai alkairi, duk wani tsanar sa da kike ci zai koma Soyayya ki cire tsanar Sultan a zuciyarki, kiyi farinciki dan gobe ranarki ce idan Allah ya kaimu, fatanmu Allah ya sanya albarka a al'amarin ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, Allah yasa wannan haɗi ya zamewa family ɗinmu alkairi duniya da lahira”. faɗawa jikin Mami Sultana tayi tana kuka, sake fashewa da wani sabon kukan, “Mami Wallahi ina sonshi, idan baku auramin shiba mutuwa zanyi, wallahi saina kashe kaina idon ba'a autamin Nas ba, Mami wallahi Nas nake so....! Ta fashe da wani irin kuka tana zamewa zata faɗi ƙasa jikinta na rawa. Da wani irin kallo Kaka ta bita harta zube ƙasan yaraf, taɗanja jikinta baya tana jan tsaki zata raɓata ta wuce. Saurin tashi Sultana tai zaune ta riƙo hannunta. Kaka Wallahi inhar baku aura masa niba saina gudu na bar muku gida!. Mami da Meena da Jidda gabaki ɗaya jikinsu ya yi sanyi, basu taɓa tunanin ƙiyaryar da Sultana take wa Sultan takai haka ba. Run gumeta Mami tayi Cikin hikima da wayo Mami ta riƙa yi mata nasiha da ƙara ƙarfafa mata gwiwa harta daina kuka, cikin wani irin yanayi ta nufi ɗakinsu ta kwanta,cikin raunan'nanyar murya ta soma faɗin" Ya Allah ina mai ƙara roƙonka ka bani haƙuri da juriya tare da wadatar zuciya a kan dukkan a binda zanci karo dashi cikin rayuwata na jin daɗi ko a kasin hakan ka kuma bani ƙarfin Zuciya da zan iya tafiyar da ita akan hakan.... Ranar dai da kyar Sultana ta iya yin Bacci,.... Washegari Tun kiran sallar farko wasu daga jama'ar gidan da makusantansu suka tashi aka fara ƙaƙainiyar ɗaura abinci. kaka ta nufin Ɗakin su Sultana ta tada ta don tayi Wonkan lalle,a hankali ta buɗe ɗakinsu Sultana. Babu wanda ya tashi a cikinsu, dan mafi yawansu basuyi barici da wuriba, Kaka ta kunna fitilar ɗakin tana kiran sunan "Sultana ki tashi kiyi Wonkan lallen ki, Meena ce ta fara farkawa saboda bata da nauyin barci sam, ta tashi zaune da ƙyar tana murje idanunta, "Ina sultana?" "Kaka ƙila tana toilet? Bakin toilet ɗin Kaka ta nufa tana ƙoƙarin buɗewa taga ƙofar a buɗe, "bata ciki fa? Fita kaka tayi daga ɗakin, bakin ƙofa taci karo da Mami ," Kulsum kodai Sultana tana ɓangaren ki?" "A'a Mama bata can" Lungu da saƙo na gidan Mami da Kaka suka shiga namen Sultana, Sosai hankalin Abba ya tashi lokaci da Kaka take sanar dashi Sultana bata gida.... Yanzu kam dai kowa ya tabbatar Sultana bata gidan, Kamar wasa saiga ƙarfe 10:30 babu Sultana babu labarinta, kowa jikinsa ya yi sanyi.. Meena ta nufi ɗaki tana hawaye, a hankali ta zaune saman gado karab Idanunta suka sauwa kan takarda,.ta ɗauki ta kartada ta nufi wajen su Abba, Assalamu alaikum Abba!! Kuyi haƙuri da abinda zaku wayi gari da shi daga taskar kuskurena, wallahi Abba bana son Auran Sultan Nas zuciyata keso. Nasan babu wanda zan faɗamawa a cikinku ya fahimceni balle akai ga yarda, amma wallahi ina masifar son Nas fiye da yanda kuke zato da tsammani. Banason na wahalar daku wajen ɗauramin Aure da wanda bana so! Abba bana son na zama sanaɗiyar rugujewar zumunci ku kaida Daddy, ga Meena nan da Ihsan da Jidda duk wanda yake so A aura masa, Na muku alƙawarin idan komai ya lafa zan dawo gareku ku ɗaura mani aure da masoyina Nas. Na barku Lafiya!!!, Daga ɗiyarku Maryam Ibrahim Gwani...... Tsit palon yayi babu wanda ya iya ko ƙwaƙwaran motsi, Abba sai faman kaɗa kai yake "Wallahi ni dai ban yardaba, sai dai idan wani Azzalumi ne ya sacemin jikata". Kaka ta faɗa tana fashewa da kuka. Tashin hankali, 🙆 *SHIN WA SULTANA ZATA AURA??* *SHIN WANI HALI SULTAN ZAI SHI GA??* *SHI WAYE NAS??* *SHI WANNE IRIN MA FARKINE SULTAN YA KE DA MEENA??* *SHIN WANE IRIN RUƊANI NE KE TATTARE DA RAYUWAR SULTAN??* *SHIN YAUSHE SULTANA ZATA GANE ABDULMALIK SHINE SULTAN??* *SHI WANNE IRIN MATAKI ABBA ZAI ƊUAUKA A KAN SULTANA??* *SHI YAU SHE KAKA ZATA HAƊU DA ABDULMALIK??* *SHIN WANNE MUTUM NE SULTAN YA GANI A UMMURA?* Amsarku na a cikin Littafin DR SULTAN. A nan na kawo ƙarshen Book 1, sai mun haɗu a book 2 in sha Allahu Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗

     
Chapter 54 · 0% Book details