Sashe 49
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 35-36* ________ Washe gari, Wuraren ƙarfe Huɗu sakon Sultan ya iso, kai tsaye ya wuce Airport ya karɓi saƙon Ya nufi ɗakin da Sultana take ya nufa. Dr Sadiq na biye da shi ɗauke da wata madaidaiciyar bag. A ciki ya samu Nurse ɗin data gama gogema Sultana jiki. Da girmamawa ta gaida shi, Dr Sadiq kuma ya ajiye bag ɗin ya fice. Matsawa yay gaban gadon lumsassun idanunsa akan Sultana da fuskarta tai wani irin fayau. ta ƙara haske sosai Ya kafe Laɓɓanta da sukayi wani irin jajur gwanin sha'awa, gashi taɗan tsuke bakin ya sake komawa ɗan mitsitsi, Ajiyar Zuciya sauƙe kana ya janye idanunsa daga kallonta, ’ ya gyara kujerar gefen gadon ya zauna tare da ɗaukar bag ɗin da Dr Sadiq ya ajiye ya buɗeta. Madaidaicin abu ya fiddo cikin kwali mai kama da kula, ya buɗesa sai ga ƙanƙara a sama tanata huci. a ƙasan ƙanƙarar ya zaro kwalaben alluran kusan guda guda bakwai ƴan ƙananu, zaune da ƙafafunsu. Sai da ya gama duba takardar dake a cikinsu kafin ya maidasu ciki ya fiddo ɗaya kawai. Miƙama Nurse ɗin dake a ɗakin yayi, murya a daƙile yace “Kiyi mata allurar nan yanzun nan”. Amsa tayi da girmamawa. A gabansa ta buɗe syringe ta kwashe ɗan ruwan allurar da ko ganinsa bama ayi sosai cikin syringe ɗin. Shine ya nuna mata a inda zatayi. Nan take wani irin mahaukacin zufa ya fara tsatstsafowa a kowacce ƙofar gashi ta jikin Sultana Kafeta da kallo Sultan dake zaune ƙafa kan ɗaya ya harɗe hannayensa a ƙirji yayi. Yanda take wani irin mutsu-mutsu ya sakin wani tattausan murmushi daya ƙawata cikar haibarsa da kwarjinin Ya ɗan lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta yana jan ajiyar zuciya. Bayan Isha'i Su Abba suka zo gabaki ɗayan su, kamar ko yaushe basu duka aka bari suka shigaba. Abba ne kawai . Sai Kaka da Mami. Basu jima a asibitinba suka dawo gidan, cike da tausayin Sultana. Bayan ta tafiyar su bada jimawa Jidda ta iso, da kyar ta shawo kan Dr Sadiq ya barta ta ga Sultana, sosai Hankalin Jidda ya tashi ganin halin da Sultana take ciki... Bayan kwana Biyar, tsawon kwanakin nan Daddy bai san mike faruwa, Abba bai sanar dashi ba, Sultan ɗin ma bai gaya Mishi ba, Abba ya yi hakan ne saboda ya san halin Daddy yanzu sai yace sai an fitar da Sultana waje don nema mata lafiya..... Alhamdulillahi cikin hukuncin Allah Sultana ta farfaɗo. cikin hankalinta, sai dai ramar da tayi dolene ta baka tausayi, hancin nan ya sake tsaho. Haka ma ta ƙara haske idanun sun fita da ƙyau masha Allah . Ramarma sai ta sake fiddo mata da ƙyawun nata. Ba ƙaramin farin ciki ahalinta suka tsinci kansu ba. Dan tunda farar safiya aka fara tururuwar zuwa ganinta. Washe gari Sultan ya basu Umurnin sallamarta..dan insha Allahu ya tabbatar ta dawo cikin hayyacinta. Zata kuma lallaɓa jikin har lokacin da za'a fita da ita ai mata aiki a ƙwaƙwalwarta ɗin... Suna isowa gida Kaka ta sakata ta shiga wanka da ruwan data haɗa mata mai ɗumi. Yanda take jin jikinta wani irine yasata nutsuwa sosai tai wanka mai ƙyau, dan ta kwashe tsahon lokaci a ciki kafin ta fito, Abinci na musamman Kaka ta haɗa mata bayan ta gama ci ta bata maganinta kana ta kwanta nan take bacci ya yi a won gaba da ita.... Sai bayan la'asar Sultana ta tashi. Wanka ta sakeyi da ruwa mai zafi tai sallah. Su Mami sai nan nan suke da ita duk abinda take so shi aka mata, Hakan yasa jikinta keta ƙara warwarewa. Bata fita ko ina, ko yaushe tana ɗakin Kaka . Sai dai taci ta ƙoshi tasha magani tayi barci. Wani lokacin Meena da Nana kan shiga su tayata hira. Bayan sati ɗaya, Still Abba ya sake tunkar Kaka da maganar Auren Sultana... Sultana na toilet Nana ya shigo ɗakin Su,"Anty Sultana Abba na kiran ki. Da Sauri Sultana ta fito da wanka ta zura dogon hijjab akan zanin wanka ta fita kiran da Nana sake zuwa tai mata. Ta iske kowa ya hallara ita kawai ake jira, zuciyarta cike da mamakin taron ta ƙarasa garesu. Kusa da ƙafafun Kaka ta zauna tana gaishe da iyayen nata. Duk suka amsa mata da kulawa suna sake tambayarta ƙarfin jikinta. "Alhamdulillahi Naji sauƙi sosai!" A kusan tare suma sukace Alhamdulillah "Allah ƙara sauƙi, "Amin Abba" Abba ne ya buɗe taron da addu'a kamar yanda shari'a ta koyar da mu. Bayan sun kammala Kaka ta fara magana akan abinda ya tarasu. "Sultana! Har yanzu dai muna kan maganar Aurenki da Sultan, Wani irin faɗuwa gaban Sultana yayi, ta dubi Abba. Nan Kaka ta soma yi mata Natsiha cikin ruwan sanyi, ta yadda Abun zai zo musu da sauƙi.. Zuciyarta na wani irin harbawa ta sake duban su Abba Yanda duk suka zuba mata idanu cike da tashin hankali sai itama suka sake ɗaga nata hankali ƙololuwa. Saurin maida kanta ƙasa tai tanajin anya kuwa zata iya?. A take rauninta ya sake bayyana bisa fuska tamkar yanda suma duk suke a raunane zukatansu na rawa da barazanar son faso ƙirazansu su fito......... "Mamana ke muke saurare daure ki faɗa mana abinda ke a ranki kinji, Kuka Sultana ta fashe da shi, bakinta na sake rawa tace, “Abba Abbah ni Nas nake so!!!.. "Sultana Abba ya kira sunanta da ƙarfi. Bayan ta ɗan zabura kaɗan ta ƙara mannewa da jikin Kaka . Sai ɗan girgiza kanta take hawaye na zubo mata da sauri-sauri... Cikin sanyi Murya Mami tace ," Abban Haydar Abita a hankali kasan matsalar dake tare da ita" "Sultana ki kwantar da hankalinki kinji, cewar Mami, Kanta ta jinjina tana share hawayenta. Ta ɗago a hankali ta zubama su Abba dake kallonta idanun. Kowannensu a kallo ɗaya zaka fahimci roƙonta sukeyi da idanu ta zaɓesa. Hakanne ya sake saka zuciyarta sake raunana. Cikin rauni Murya tace Abba na Amince zan Au..... Sai kuma ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Fusakar su ɗauke da murmushi, suka shiga sanya mata Albarka... "tashi kije mun gama da ke. Ki kuma share waɗan nan hawayen ki kwantar da hankalinki, dan munsan abinda mukeyi”. Kai kawai ta jinjina mata tana miƙewa. Batare da ta sake duban inda su Abba suke zaune ba ta fice a falon jikinta duk a sanyaye. Zuciyarta kuwa wani irin zafi take.. Sultana na zaune a ɗakin kaka tana sharɓar kuka, ahaka Kaka tashigo ta isketa. Da sauri tak'arasa gareta tajawota jikinta ta rungume, tana mai lallashinta. Kiyi hak'uri Sultana, nima bazan yarda a cutarmin dakeba, Sosai Kaka ta lallesheta tare da Kwantar mata da hankali... _______★★★★★_______ Sultan Komai yinsa yakeyi cikin wani yanayi, kokad'an babu alamar d'igon walwala tattare dashi, ga d'unbin kasala daya tashi da ita ayau, hakan tafarune saboda k'arancin barci dabai samuba a kwanan nan , saboda Feshin lafiyar Sultana, siririn tsaki tareda yaye towel d'in dake kugunsa bayan yasaka boxer, yad'an Mirza mai kad'an ajikinsa tareda feshe ko ina Na jikinsa da body spry d'insa mai dad'in k'amshi, yasaka farar vest sannan yasaka Shuit , yayi k'yau sosai, Wani turaren yakuma d'an fesawa kad'an, sannan yajawo takalmansa da safa yazauna kan sofa yana k'ok'arin sakawa. Knocking d'in k'ofarsa da akeyi yasakashi jan tsaki, da k'yar yabud'e baki yace ashigo. Ihsan ce d'aukeda tire Wanda aka shirya masa break d'insa. "Ina kwana Ya Sultan Cigaba yayi da saka takalmansa batareda yad'ago ya kalletaba. Taja table ta ajiye."Ina kwana" Yanzunma bai d'agoba ya amsa da lafiya. Duk atsorace take, jin alamar tana tsaye akansa yasakashi d'ago jajayen idanunsa yazuba mata, cikin daburcewa tace dama um..um.... Mommy ce tace akawo maka break fast naka, . Baice komaiba yamaida kansa yana k'ara gyara igiyar takalminsa. Da sauri Ihsan tabar d'akin, Koda yagama bai kalli abincinba, yak'arasa gaban madubi yad'auki agogonsa yasaka, sannan yad'auki jakkar lap-top nasa yanufi k'ofa. Sai kuma ya dawo, tareda jawo table d'in da Ihsan ta ajiye break fast d'in gaban sofa. Tea kawai yahad'a kad'an yasha, Dan bayajin cin komai ayanzun. Yana gamawa yamik'e yafice. Babu kowa afalon, yana ƙoƙarin haurawa Sama Mommy ta fito daga Kicin riƙe da Basket ɗinsu Salma da Salim, dai dai lokacin suka suka fito daga ɗakin su, riƙe da School bag ɗin su, "Ya Sultan Good Morning!" "Morning kun tashi lafiya?" "Lafiya lau Ya Sultan" "Ya Sultan jiya na ganka a mafarki kaida Anty Sultana kuna riƙe da baby tana kuka, kace Anty Sultana ta goya taƙi wai tagaji bayanta ciwo yake, shine kai kuma ka goya Baby! Ya Sultan ina son Baby tana da kyau sosai!" Tunda Salma ta fara magana Mommy ta kafeta da kallonta tana Murmushi, Sultan ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe a kan fuskar Salma dake Murmushi har yanzu.... "Mommy Ina kwana?" "Lafiya lau Ya Babba!" Ina fatan kayi breakfast ɗin ka?" Kai ya gyaɗa mata. Kana yace "Ina Daddy?" " Ya tafi wani jana'iza wani Makwoƙocin mune ya rayu a tsuhuwar Unguwarmu."Ayya Allah ya jikan musulmi!" ",Amin" "Zan wuce Mommy! "Allah ya kiyaye,"Amin yana fita bada jimawa Su Salma suka wuce School... __________★★★★_________ Saida Kaka tayima Sultana jan ido sannan tad'an saki jikinta, Duk Wanda yaga halin da Sultana take ciki tun ajiya zai tabbatar batason aurenne?. Amma tasan yanda zata ɓulloma lamarin kodan ta kuɓtar da kanta.... Sultana wayarta ɗoka takoma can Ɗakin su ta rufe , Number Jidda takira, babu dad'ewa tad'aga. Tana d'agawa tasaki kuka, cikin mamaki Jidda tace Daughter! Lfyarki kuwa? Ko wanine yarasu?. 'a, Sultana tafad'a cikin shashshekar kuka. Tomiya faru?. Sultana Na kuka ta zayyanema Jidda komai, a mamakin Sultana saitaji Jidda ta daddage ta rangad'a gud'a. Da sauri Sultana ta janye wayar daga kunnenta, saida ta tabbatar Jidda tagama sannan tamaida wayar tana kuma rushewa da kuka," Mommy na wallahi bana son sa!, daga can ɓangaren Jidda ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciya kana tace ,"Ha ba Daughter Miye aibun Dr Sultan! Ni fa wallahi na jima ina fatan Allah yasa yazamo mijinki, baki yadda kuyi matuƙar dacewa ba!, " Mommy yanzu kema kina goyon bayan shi?," Sosai ma! Daughter" "Shikenan daga haka ta katse wayar tana share hawaye.. _________★★★ Sultan zaune agaban Daddy da Mommy, kansa ak'asa yana sauraren iyayen nasa. Abba yayi garan murya irintasu