Sashe 6
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
tsakanin da Kubra, rayuwar suke cikin kwanciyar hankali, Ranar da aka yaye Maryam suka shiya zuwa ƙauye kai maryam wajen Yaye a hanƴar su ta dawowa sukayi hatsari nan take suka rasu, A lokacin ba ƙaramin tashin hankali Kaka ta shiga ganin gawarwakin su a bangaren Abdullahi har akayi jana'izar baya cikin Haiyacinsa, duk sanda Maryam take kukan yunwa haka zasu saka ta a gaba suna kuka, tana kukan reshin Nono suko suna kukan tausayi ta, hakan ya sa suka ɗauƙi son duniya suka ɗorawa Maryam, bayan wata biyu da rasuwar su Abdullahi yaso Mama ta dawo ɓangaren Ibrahim da zama taƙi haka ya ƙukura ya barta a kyauye. Maryam nada shekara Biyu da Rebi Kubra ta haihu murna wajen Kubra ba'a ko magana, Ranar suna Yaro yaci sunan Malam Aliyu suna kiransa Haydar, Maryam tana son Haydar sam Kubra bata son Maryam ta raɓeshi, duk yanda Abdullahi yake iya ƙoƙarin sa wajen nuna mata Maryam da Haydar duk ɗaya ne, sam taƙi ɗaukar haka, daga ƙarshe ma ta ƙarar tsanar Maryam saboda irin son da Abdullahi da Kaka sukale~~~~ mata... Bayan ƙura ta lafa aka raba gado Kaka da Abdullahi duk suka barwa Maryam, sai a lokacin Kubra tasan dukiyar su a, haɗe take, Haka Abdullahi yaci gaba da juya Dukiyar maryam tare da tashi, Rayuwa naci gaba da huɗewa, zuwa Kurba ƴaƴanta Ukku Haydar, Khalil, Hauwa'u, suna kiranta Nana, zuwa yanzu Abdullahi Baida kowa sai Kaka da iyalinsa..... Haka Kaka taci gaba da kula da Maryam cikin kwanciyar hankali, Abdullahi baya babbata Marayam da ƴaƴan sa, lokacin da ta cika shekara Ukku Abdullahi ya matsa su dawo birnin saboda karatun Maryam ba yadda Kaka ta iya suka tattara suka dawo Birnin badon ta soba, zuwanda ya zame mata damuwa, tunda Kaka da maryam suka dawo birnin da zama, Kurba na kullum cikin Habaice Habaice take tana faɗin, tunda an raba gado an ba kowa nashi zaman me suke a gidan, ko so suke suga bayan dukiyar Abdullahi, tun Kaka na haƙuru har takaiga yiwa Abdullahi magana ya jawa Kubra kunne, hakan ya janyo tashin hankali tsakanin Kubra da Abdullahi har ya haifar da saki tsakanin su, Ganin haka yasa Kaka ta yenke shawarar suka koma ƙauye tare da Maryam, ranar da zasu Tafi Abdullahi da Hawayen shi, a ganin sa kaman bai riƙe Amana ba, nan Kaka tashiga lallashinshi kan yayi haƙuri karatun birni da ƙauye duk inda mutum yayi bazai wuce Azzakinshi, tunda suma a ƙauye sukayi karatu har suka kai matsayin da suke a yanzu, sosai maganar Kaka ta shigeshi bayan sun koma ƙauye ya gyara musu gida da duk wani abun buƙata, saboda Kaka ba mai son kyale kyale ba ce, sam zaka ce tana ɗaya mai kudin, duk da hakan gidan ta na ɗaya daga cikin gidajen masu kyau a ƙauyen kayan Abinci duk wata yake turo mata.. haka suci gaba da rayuwa cikin kwanciyar da walwala... tuni an saka Maryam makaranta... Abdul Maleek yaro ne na tsastse dawowar ƙaunyen bada jimawa Allah ya yiwa mahaifiyar shi rasu, haka suka ci gaba da rayuwa tare da Mahaifinshi, a lokacin shekarar sa goma, zuwan da yake gidan Kaka ɗibar ruwa nan Allah ya haɗa jinin shi da Maryam, wata irin shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, Ranar da ba makaranta idon ya zo gidan su Maryam baya koma sai dare, Mahaifinshi ɗan kasuwa ne yana sayarda dabbobi, duk lokacin da zaiyi tafiya a gidan kaka yake Barin Abdulmalik Kasan cewar Baida ɗan Uwan a garin Kaka ce ta zame mishi dengi, haka suke rayuwa tare da Mahaifinshi cike da kyaunar juna, Mahaifin Abdulmalik mutumen girki ne. Abdulmalik na jss3 Allah yayi wa mahaifinsa rasuwa a can garin da yake zuwa kasuwanci, lokacin da labarin mutuwar ta riski kaka da Abdulmalik sun shiga tsakanin tashin hankali, haka yaci gaba da rayuwar shi cikin kulawar Kaka da ta ɗokeshi tamkar jikanta, ba yan rasuwar mahaifinsa ba yadda Kaka batayi ba a kan ya dawo gidanta da zama ya ƙi a cewar shi baya son barin gidan saboda mallakin Mahaifinshi ne, da taimakon Kaka Abdulmalik ya kammala Secondary, Abdulmalik yaro ne mai son neman na kasan ka, bayan ya kammala Secondary yaci gaba da neman aiki duk da bai rasa komi ba duk abinda yake buƙa Kaka nayi masa, hakan yasa ya nemi aiki a kasuwa nan Allah ya haɗa shi Oga Kabiru da yake fake masa shago da ɗan aikace aikace duk sati yake biyan shi dubu biyar.. Kasan cewar Abdul Maleek yaro ne mai natsuwa da Amana hakan yasa Oga Kabiru ke ƙaunarsa duk lokacin da yake zuwa birnin sayen kaya da Abdulmalik yake zuwa Kasan cewar bai yai karatu ba duk cikin yaran shi ba kaman Abdulmalik... Maryam ƴarinƴa ce kyakkyawa fara Masha Allah don tana kama da mahaifiyarta sosai maryam ƴarinƴa ce mai shegen wayo ga reshin tsoro ga tsiwa ga miskilanci akwai shaƙuwa sosai tsakinin Abdulmalik da Maryam... wannan kenan....🤗 Bayan Isha'i suna zaune a tsakiyar gida, Abdul Maleek ya shigo gida da guda Maryam ta nufi wajensa ta rungumesa, tana faɗin "Sannu da zuwa Ya Maleek!" Sassanyan Nunfashi ya sauke cike da gajiya yace "yauwa Maryama ta!" "Barka da dare Kaka, "Abdulmalik An dawo lafiya?" "Lafiya lau Kaka" yana gama cikin Abinci sukayi karatu, kana ya kalli Kaka cikin sanyi Muryar yace "Kaka gobe idon Allah ya kaimu zamuje Birni sayen kaya tare da Oga, Nunfashi Kaka ta ja kana ta fesar, murya a sanyaye tace "Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya!" "Amin Kaka" cikin raunin Murya Maryam tace "Ya Maleek idon ka tafi yaushe zaku dawo!" Ajiyar zuciya ya sauke kana yace," Ban sani ba" Maryama kaman Zatayi kuka," Ya Maleek zan bika, "A'a, kana ya yi musu sallama ya wuce gida.... Washegari tunda safe bayan sun karya yayi Kaka Sallama kana ya wuce kasuwa... Yana barin gidan Maryam ta fashe da Kuka tana kiran Ya Maleek...✍️✍️ *More comments and share* *Sadeeya Ka'oje ce* *DR SULTAN* *( THE BEGINNING)*