Sashe 10
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
a hankali ya juyu suna fusakar zuna da sauri ta faɗa jikinsa ta rungumeshi, "Ya Maleek Allah ya kaika Lafiya ya dawo dakai lafiya" "Amin ya Allah Maryama ta! Kinga bari na tafi lokacin na ƙarewa, " Ya Maleek Allah ya sadamu da Alheri! Nan take jikinsa ya yi sanyi, murya a dishace yace ," Amin" tana tsaye a wajen har ya ɓace mata kana ta wuce cikin gida, Jikin a mace ya wuce kasuwa tsawon Awa guda kenan da isawarshi sai yanzu Oga Kabiru ya iso Kana suka wuce..... Bayan tafiyar Abdulmalik baifi minti goma Atiku Direba ya iso kana suka wuce, tafiya suka hankali a kwance kar suka iso Kano kai tsaye ya wuce dasu Asbiti.... Isowar su ya yi dai da likata na sanarda Abdullahi rasuwa Kubra Haka kaka taji maganar kaman saukar Adaru nan take jikinta ya soma ƙarkarwa cikin wani irin mummunan yanayi da tashin hankalin murya rana ta kira "Abdullahi da gaske Kubra ta rasu Abdullahi da tunu ya baya cikin Haiyacinsa sam baiji me kaka ka faɗi ba, Maryam gabaƙi ɗaya a ruɗe take....... Nan take Kaka Abdullahi ya yenke jiki ya fadi a sume, Maryam ta kwalla wata irin ƙara mai razanarwa, tare da ƙamkame Kaka jikinta naci gaba da ƙarƙarwa........ *ABDULMALIK*💔😥 Tunda suka dauki hanyar suna tafiya ba abinda yake ji a zuciyarshi kamar kewar rabuwa da Maryam ya rasa abinda yasa bugun zuciyarshi take tsananta a kowani dakika na bugun agogo dake cikin motar,lokaci zuwa lokaci zufa ke tsatsafo masa yana gogewa ji yakeyi kamar tafiyar da zaiyi bazai dawo ba,wata zuciyar Kuma na raya masa sun rabu da Maryam kenan rabuwa ta har abada,addu'a yakeyi indan yaji irin wanan tunanin ya fado masa har suka Yi nisa sosai a tafiyar tasu. Bayan yayi addu'ar ya samu nutsuwa ba'a mintuna kalilan ba yaji kamar yanayin tafiyar motar ya chanza,bae samu cewa komai ba ya dinga sauraro a tsanake chan dae yaji kamar motar na kara wani irin kara, da sauri ya ce "Anya baza'a faka a duba motar nan ba kuwa dri......" Ko karasa abinda zaifada baiyi ba motar ta kwace a hannu driver ta shiga junjuyawa har zuwa jeji sosai yake son rike sitiyarin motar abin ya ci tura,Wani babban dutse motar ta daka da karfin tsiya ,a take bangaren da maleek yake qofar ta bude kamar wanda akayi wurgi dashi ya fada cikin dokar daji kansa ya bugi katon dutse nesa da inda hatsari ya afku. haka motar taci gaba da junjuyawa cikin hunkici Allah ya tsaya cak...... Bayan wani ɗan wani lokaci mutane suka taru a wajen tare da basu taimakon gaggawa, tuni labarin mutuwar ya kewaye garin ƙaraye cikin tsananin tashin hankali, daga daga cikin maƙotan Kaka ta kiranta kusan sau ukku gab da kiran zai tsinke Kaka ta daga murya a dishace tace"Iya! "Kaka ya mukaji da haƙuri Abdulmalik ashe lokacin Yayi! cikin tsananin tashin hankali da ruɗewa "Kaka tace wanne Abdulmalik!"Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n!" Kasan cewar wayar a hand free take nan take Maryam ta yanke jiki ta faɗi.....✍️✍️✍️ *More comments and share* *Sadeeya Ka'oje ce💋✍️* *DR SULTAN* (A heart touching love story)