Sashe 12
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *Page 9-10* ________ Nan take ta yenke jiki ta faɗi "Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n! Atiku Direba dake tsaye cikin ruɗu da tausayawa ya yi saurin ƙara so gaban Kaka, cikin tsananin tashin dake tattare re dashi murya a disashe ya soma magana ,"Mama suma tayi, Kaka tuni tayi suman zaune, "Doctor ku taimaka muna, da sauri Nurse suka ƙara so wajen tare da ɗaukar Maryam suka wuce da ita..... Cikin Wata irin dakakkiyar murya mai ɗauke da tarin raɗaɗi ta ƙuna tace," Abdulmalik ɗin ne ya rasu! Kallonta ta mayar ga Abdullahi dake zaune daɓas a ƙasa kaman wani yaro tare da wani likita Rungume da shi, dai dai lokacin wata nurse ta iso hannuta dauke da ruwan gora, Dr ya karɓa kana ya buɗe tare da yayyafawa Abdullahi ruwa dake kwance a jikinsa har so biyu sai a karo na Ukku ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, a hankali ya soma buɗe idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir ya sauke su akan Kaka, a hankali Abdullahi ya fara sakin Ajiyar zuciya kana ya shiga maimai ta Addu'oi sannu a hankali ya fara dawowa haiyacinsa A hankali ya sake ɗago da idanunsa ya kalli Kaka ya yi ƙasa da kansa cikin raunin Murya ,"Mama da gaske Kubra ta rasu!?" Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare da Kaka, ta kallesa Zuciyarta na bugawa da matsifar ƙarfi murya a disashe tace ,"Abdulmalik ya rasu! jiki a mace Abdullahi ya fara janye jikinsa, "Mama kubra ta tarasu!" Kai Kaka ta gyada mishi cikin tsananin tashin da ruɗu ta fashe da kuka mai tsuma zuciya murya na rawa tace ," Abdulmalik ma ya rasu!!!"Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n" cikin ƙanƙanen Lokaci Asabiti ya cika da mutane kasan cewar ɗaya daga cikin nurse ɗin kwai ƴar Uwar Kubra, ko wannen su damuwa fal a fusakar sa, koda aka fito da gwar Kubra da kyar Abdullahi ya iya mata kallon karshe, kana ya fashe da sabon Kuka, kasa cewa komi ya yi kawai ya fashe da matsanancin kuka cikin raunin Murya yace," Allah ya jiƙan ki Kubra! Allah ya ƙarɓi baƙunci ki!, Kaka ma tuni hawaye sun cika tab a Idonta, wani irin tausayin ne ya ratsa duk kan mutanen da ke tsaye a wajen, anan Asibitin aka shiryata kana akayi mata sallah tare da kaita gidanta na gaskiya, Jana'izar da tasamu halattar dumbin jama'a yan uwa da abon Azziki.... *ƘARAYE* tuni an iso da gawarwakin wayan da sukayi Hatsarin nan take gari ya hargitse da koke koke, kasan cewar sunyi dameji sosai bata ɓata lokaci akayi jana'izar aka gaisu gidan su na gaskiya,..... *KANO* Murya a disashe Abdullahi yace " Kaka Mutafi gida ko!" Cikin raunin Murya Kaka tace ," Abdullahi Maryam tana wajen likitoci!"Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n!" Cewar Abdullahi , *MARYAM* Likitoci ne suka duƙufa a kanta tare taimakon gaggawa koda wasa bata bata farfaɗo ba, ganin haka yasa suka ɗauko wata na'ura mai kama da iron suka fara dannan mata a ƙirji... haka suka ɗau tsawon lokaci Amman ina babu alamu rai a tare da ita.. haka likitoci suka kwace tsawon lokaci don ganin sun ceto rayuwarta, a karo na Barka tai suka sake danna mata na'urar a ƙirji ta ƙarfi, cikin ikon Allah Maryam taja wani dogon Numfashi sai kuma jikinta ya sake, a karo na biyu Dr ya sake danna mata na'urar,da ƙarfin gaske, ta sake jan wani Numfashi, still bata farfaɗo ba, Dr wata irin zufa ce ta riƙa tsastafo mishi, sauran Dr duk jikinsu ya yi sanyi, a hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe su a kan fuskarta Maryam, da kyar ya tattaro duk kan ƙarfinshi ya sake danna mata na'urar da karfi, taja dogon Numfashi tare da buɗe idanunta cikin raunin Murya tace," Ya Maleek!!!" Lokaci ɗaya likitoci suka sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar tare da fesar da Numfashi, Duk da bata cikin haiyacinta hakan bai sa ta Dena faɗin ," Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n!! da duk wata Addu'a data zo mata a hankali ta ɗago da kanta ta kalli Lokacin dake tsaye a wajen, "Ina ya Maleek!!?" "Ina Kaka!!?" "Je ki kira ƴan Uwanta" cewar Dr, tare suka shigo Abdullahi da kaka da sauri suka nufi wajen Maryam, Murya a dishace Maryam tace ," Kaka da gaske ya Maleek ya yarasu!?" Jinjina kai Kaka tayi cike da tausayawa cikin raunin Murya tace," Ki Dena kuka Maryam kiyi mishi Addu'a Kinji!" Girgiza kai tayi tare da cije lips ɗin ta kana ta runtse idanunta cikin wani irin mummunan yanayi mai wuya tace. ," kaka shikenan na rasa Ya Maleek! Kaka shikenan Ya Maleek ya tafi ya barni? Wayyo!! Allah ya Maleek me yasa zaka min haka?" Sai kuka ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, cikin wata irin raunan'nanyar murya taci gaba da kiran Ya Maleek!! a karo na Barka tai, Kallonta Kaka tayi cike da tausayawa yanin yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi kaman zata fasa ƙirjinta......da sauri ta runtse idanunta da masifar karfi Zuciyarta naci gaba bugawa da ƙarfi.... Mutsu mutsu ta kaman wata zautacciya hawaye Masu bala'in zafi na zubo mata.. "Ya Maleek me yasa ka tafi ka Bar....ni kasa ƙarasa Maganar nan take ta fashe matsanancin kuka a take Numfashin ya sake ɗauke...... Likitoci suka sake duƙufa a kanta suka shiga bata taimakon gaggawa da kyar da bone suka samu ta farfaɗo still tana ci.gaba da surutai haka yasa Dr ya yi mata Allurar Bacci nan take bacci wahala yayi a won gaba ta da ita.... Ajiyar zuciya suka sauke," ɗaya daga cikin nurse ɗin yace halam," Mahaifiyarta ne?" ba wanda ya kulashi , Ina ga tunda ta samu Bacci a barta ta huta Insha Allahu idon ta farka zata samu natsuwa, Jiki a mace suka fice daga dakin ," Abdullahi Ya kamata kaje gida Kodan masuwa gaisuwa," TOH Mama!!" kana ya wuce tare da Atiku, sai lokacin ya samu damar duba wayar shi Kasan cewar a silent take miss call ne ba a daɗi koda suka iso gida mu tane cike tam, ɗaya ba yan ɗaya suka riƙa jajanta mishi sai wuraren 10 ya samu damar shiga gida, tuni su Haydar sunyi Bacci koda yaje daƙinsa kwance suke suna Bacci hankalin kwance..... Ɗakin sa ya wuce ya watsa ruka ya canza kaya kana ya wuce Asbiti, har yanzu Maryam bata farka ba. Sosai Kaka tayi Mamakin ganinsa,"Abdullahi Meya dawo da kai? " Mama kona zauna gida ba bacci zanyi ba!" ga wannan nasan baki ci komi ba!" Kaza ce da Youngaut mai sanyi," Abdullahi ka koma gida kasamu ka huta, kaji Kaka ta faɗa cikin tausayawa," da kyar Kaka ta shawo kanshi kana ya wuce gida cike da damuwa, Ranar dai Haka suka kwana a zauna cikin ƙunci da raɗaɗin zuciya, A ɓangaren Abdullahi ma haka ya kwana cikin wani irin yanayi na kewar matarshi..... Kiran farko na Assalatu a kunnen Maryam, a hankali ta fara buɗe idanunta da suyi bala'in hauyi ta sauke su kan Kaka dake zaune a wajen hannuta rike da tazzabaha idanunta a bushe alamar ko runtsawa bata yiba, Cikin wata irin raunan'nanyar murya tace ," Kaka!" Kallonta Kaka tayi cikin ƙarfi hali da danne damuwar ta tace," Na'am Maryam" ya yinda Zuciyarta ke ci gaba da bugawa da matsifar ƙarfi tace ," Ya Maleek!" cike tausaya Kaka tace ," Maryam kiyi haƙuri Kinji" kiyiwa Abdulmalik Addu'a kinji, Jinjina kai tayi tare da sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar, tashi muyi sallah Kinji kiyiwa Abdulmalik Addu'a!" tare da taimakon Kaka Maryam tayi Alwalla kana sukayi salla a tare bayan ta sallame sallah ta daga hannayen ta sama ta soma Addu'a tana Kuka, Kaka ma Hawaye ne taf a Idonta cikin dubara tasa hannuta ta goge Hawayen..... Wuraren karfe 8:30 Dr ya shigo, " Masha Allah jikin da sauƙi zaku iya zuwa gida, ƴan rubuce rubuce yayi kana ya miƙawa Kaka ,"Ga wannan a saya mata maganin zai taima kamata sosai Allah ya bata lafiya," Amin likita mun gode," ba komi Mama!" "Bari na kira Abdullahi Azo a ɗauke mu, nan Kaka ta nemi wayar ta rasa, cikin tsananin tashin ta fara neman waya a ɗakin ba wata ba madadinta, sai yanzu ta tuna tunda Iya ta kirata ta sanar da ita Amrasuwar Abdulmalik wayar ta faɗi Ƙasa bata koma binta kanta ba, tana tsaka da tunanin Atiku ya shiga hannusa dake da Basket mai matsifar kyau, " Mama ina kwana ya mai jiki," Cikin sanyi Murya Kaka tace ," Jiki Alhamdulillahi har an sallame mu" Mutafi gida kwai"ba tare da ɓata lokaci ba suka wuce gida,ƙofar gida cike tab da jama'a, ya yi parking Abdullahi ya nufi wajen su ," Ina Kwana Mama!" " Lafiya lau Abdullahi ya ƙarin Ha ƙuri" " Angode Allah, Mamana ya jiki!" Murya a disashe Maryam tace ," naji sauƙi Abba!" Nan Abokan Abdullahi suka shiga yiwa Kaka gaisuwa, kana suka wuce gida da gudu su Haydar suka sheƙo tare da Rungume Kaka da Maryam, Kaka ta kallesu cikin tsananin tausai yaro kenan, mutane ne cike cikin palon matan Abokan Abdullahi ne sai masu aiki, da ƴan uwan Kubra, cikin girmawa suka gaida kana Haydar yaza Hannuta suka wuce ɗakin su, nan suka tarar da a kwatin su, Wonka Kaka tayi, bayan ta fito Maryam ta shiga sosai taji daɗin jikinta koda fito a shirya musu Lafiyanyen Breakfast, Kaka kam ruwan tea kwai tasha, Maryam haka, Ranar dai Kaka suka yini har zuwa dare ba wata walwala a tare da su kawo da abinda ke damunsa, bayan Isha'i kowa ya watse ƴan gida dai aka bari, Abdullahi koda ya shigo yaran duk sunyi Bacci Hadda Maryam saboda cikin maganinta ta akwai na bacci ciki, Kaka ce kwai zauna ta saka yaran a gaba tana kallo, " Mama bakiyi bacci ba?" Abdullahi ya faɗa cikin sanyi Murya," Ajiyar zuciya Kaka ta sauke kana ta kalli Abdullahi, " Banyi ba Abdullahi"ya kamata kikwanta ki kuhuta," Abdullahi kona kwanta Bazan iya yin Bacci!" Abdullahi ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, " Mama wannan yaro dake zuwa gidan ki shine ya rasu!?" "Shine Abdullahi!" "Baida lafiya halam?" "Lafiya lau yake jiyama kafin mu ta so tare muke dashi, hatsarin mota sukayi nan Kaka ta shiga bashi labarin Abdulmalik tun farkon haɗuwarsu" " Ya Salam! Mama me yasa tun lokacin baki sanar dani ba na ɗauƙi nauhin