Sashe 43
Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 31-32* _______Murya a sanyaye tai sallama a ƙofar falon har kusan sau uku. jin shiru ba'a amsaba ya sakata tura kanta ciki da haushi. rashin amsa mata sallamar da ba'ayiba ne ya sakata ƙin kallon baƙon ma balle tasan wanene. murya a cinkushe batare data kallesa ba tace, "ina wuni". Sultan dake zaune yana dannar waya .ya ɗan ɗago kansa dan sam baiji sallamarta ba balle shigowartaba ma shi, sai gilmawarta kawai ya gani yanzu da take ƙoƙarin fita. Cikin tsautsayi ta bigi Center table da ƙafa. baya tai taga-taga zata faɗi cikin sa'a yayi saurin saka mata ƙafa dan son kareta bisa tsautsayi ta faɗa saman cinyarsa.. Daddan turarensa ta Shaƙa tayi tai azamar ɗagowa cikin tashin hankali da tsantsar takaici. Idanunsu ne ya shige cikin na juna, cike da firgici Sultana ta sake waro masa idanunta da kware baki zatai ihu saboda harga Allah ta tsorata da ganinsa. Saurin saka tattausan hannunsa yayi ya rufe mata bakin , tare da sake manneta a jikinsa sosai shima a cikin ɗan firgice. Wani irin mugun bugawa ƙirjinta ya sakeyi, jikinta ya hau ɓari tamkar mazari mutsu-mutsun ƙwace kanta tana kai masa duka a ƙirji.. "Oh my God!. Please calm dawn”. Ya faɗa yana janye hannayensa duka daga jikinta. Cikin rawar jiki hawaye na zirara ta miƙe, sake bigewa tai da kujera ƙafarta ta tuzguɗe ta sake yin gaba kuma zata kifa yayi saurin riƙo mata hannu ta sake dawowa jikin nasa. “Wayyo Kaka ɗan isk.........” ta wage baki da iya ƙarfinta zata faɗa yay azamar saka hannu ya sake toshe bakinta da manneta sosai a jikinsa yanda bazata iya ko motsawa ba. da ƙarfi Sultana ta janye jikinta Sultana dake ja da baya tana ja da baya da kallonsa tace, “Ɗan iska kawai, Allah ya isa ban yafeba. Wallahi daga yau ka sake ƙoƙarin taɓamin koda hannu sai na illataka. A hankali ya nufi wajen Sultana dake durƙushe har yanzu tana kukan tashin hankalin, Handkherchief ya ciro a aljihunsa tare da tsugunawa gabanta, murya ƙasa-ƙasa yace, “ Stop crying!”. A razane Sultana da batasan da isowar tasaba ta ɗago danjin maganarsa gab da ita. Kamo hannunta yayi, da sauri ta dawo da dubanta garesa tare da fisgewa da ƙarfi. Sai dai ko gezau baiyiba balle tai tunanin ƙwacewar. “Kai wane irin......” Yatsansa ɗaya ya ɗaura akan baki. “Shii!" ya faɗa cikin katseta da zazzaro mata idanunsa sosai. Tai saurin rufe bakin kuwa. Dan wani irin shakkarsa da tsoronsa da bata taɓa fuskantaba daga gareshine ya shigeta yau ɗin. Ga wani irin kwarjini mai bala'in cika idanu da yayi mata. Batare da yayi magana ba ya saka mata handkherchief ɗin cikin tafin hannunta tare da matso da fuskarsa gab da tata cikin wata irin raunanniyar murya yace, " It okey" daga haka ya fice daga palon Ya tabbata idan ya cigaba da zama a falon to lallai zai iya aikata abinda shi kansa bazai yafema kansaba. da kyar Sultana ta tattaro da duk natsuwar Kana ta wuce gida tana sauke Ajiyar zuciya, Palo ta tarar da Abba da Mami da Kaka. Sai faman kallonta suke, Kaka ta ce ,"Ina mijin namu yake?" Shine ya wuce ko gaksuwa babu?" Ciki reshin fahinta Sultana tace ,"Miji Kuma?" "Mamana! Sultan shine mijin da zaki Aure" Sultana dake jin jiri na neman zubar da ita ƙasa ta faɗa tana mai dafe kanta,Da ƙyar ta iya kai hannu domin lalubar bango. Sai dai kuma ina bai kai ga bangonba wani duhu ya mamaye idanunta. a take ta zube ƙasa jikinta na karkarwa saboda wani bala'in sara mata da kanta yayi lokaci ɗaya, cikin tsananin tashin hankali suka nufi wajenta da sauri Abba ya zabura dan jin jikinta yayi sanyi ƙalau ya saki. Yayi saurin maida yatsunsa biyu wajen hancinta. tabbas bata numfashi’l ya ambata a zuciyarsa yana ɗagota gaba ɗayanta. Mami da Kaka duk sun ruɗe Cikin tashin hankali Kaka tace, "Abdullahi mike damunta "Ban saniba nima Mama, kinga miƙo ruwa dan bata numfashi" . da sauri Mami ta ɗakko masa ruwan , ya miƙa hannu ta tsiyaya masa. shafama Sultana yayi a fuska. sai dai ko motsi batayiba balle ai tunanun zata farko. Hankalin Abba ya sake tashi matuƙa. Ya ɗago idanunsa da sukai jajur ya kalli Mami dai dai lokacin Haydar da Khalil suka shigo palon, hankali a tashe suka nufi wajen Sultana dake kwance kaman babu a rai a cikinta, cikin raunin Murya Abba yace Haydar fito da mota, aiko da sauri ya ɗauke key mota ya wuce wajen jikinsa na karkarwa, Abba ya ɗauki Sultana suka wuce waje, Kaka ta bi bayansa da Mami kai tsaye suka wuce private hospital dake cikin Unguwar su, Tun isowarsu asibitin aka fara bama Sultana dake a sume taimakon gaggawa. tsawon lokaci bata farfaɗo ba Hakan sai ya sake ɗaga hankalinsu. musamman ma Kaka dake ta faman sharɓar hawaye. Cike da kulawa Abba ya zauna kusa da ita duk da kunyar ɗan fari dake tsakaninsu. Murya a tausashe da nuna ɗunbin kulawa da ladabi ya fara lallashinta da faɗa mata kalamai masu taushi da nutsuwa irin na masu ilimi. Ya nuna mata koda rasa Sultana sukayi su zama masu haƙuri da godema Allah . Dan lokacin da ya basu ita baiyi shawara da suba. A yansu kuwa idan ya karɓeta ya fisu bukatarta ne. Haka ya cigaba da mata nasiha harta samu nutsuwa tai shiru. Ya saka handkherchief ya share mata hawayen. Ana haka Doctor ya fito daga ɗakin da aka sanya Sultana. Ya buƙaci ganin ɗaya daga cikinsu cikin Abba da Kaka suka bisa Zuwa Office, A office ɗin likita kuwa ya nutsu ne wajen rubuce-rubuce a wata takarda kafin ya maida hankalinsa gasu Abba," Alhamdulillahi ta farfaɗo,.Sai dai kuma kamar yanda kuka sani raunin dake a cikin ƙwaƙwalwarta shine ya motsa mata. Kuma gaskiya a bincikenmu yarinyarnan tana matuƙar buƙatar son ganin babban likita. Idan ba hakaba a koda yaushe zata iya fuskantar gogewar komai na ƙwaƙwalwar ta. . A duk kuma lokacin data shiga ƙunci ciwon na mata kuɗa a cikin kanta, ba dan ma tana samun kulawa da kuma addu'oi ba da gaskiya bana zaton yarinyarnan zata kai wannan lokaci batare data tsinci kanta a ciwon hauka ba. Duk da komai na Allah ne, babu wani bawa daya isa canja ƙaddarar wani bawa daga yanda tazo a littafinsa. Amma a wannan karon ayi himmar sadata da likitan daya dace da matsalarta, munan taimako kawai muke bata na dakatar da raɗaɗin a gareta a lokacin daya taso. Amma matsalarta sake hauhawa takeyi gaskiya, Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare da Kaka ta kalli Abba cikin raunan'nanyar murya ta ce ," Abdullahi mike damun Sultana!!!? Naji likita na faɗin kwakwalwarta ta samu matsala yaushe hakan ya faru ban sani ba? Abdullahi mi kake ɓoyemin akan Maryama!!? A iya sanina Maryam lafiya kau aka haifeta bata da wata matsala!!" Abdullahi da gabaki ɗaya jikinsa ya yi sanyi, irin wannan rana yake gudu da tun lokacin da abin ya faru ya yiwa Kaka bayani da han bata baruba.. Abdullahi ya sauke Nannauyan Numfashi kana ya kalli Kaka cikin sanyi Murya mai cike da lallashi ya ce ," Mama ki gafarceni akan reshin faɗa Miki gaskiya da banyi ba, Mama shekara Takwas da suka wuce Sultana tana fama da wannan matsalar Sanaɗiyar Wannan yaron da ta rasa Abdulmalik dake ƙayare, saboda so da shaƙuwar dake tsakaninsu jin labarin mutuwarsa a bazata shine ya haifarda wannan matsalar!" Kaka ba baki ɗaya jikinta Ya yi sanyi, duk abinda aka ce mata ya faru da Sultana sanaɗiyar rashin Abdulmalik ba zayi musu ba, saboda tafi kusanshi dasu tafi kowa sanin irin shaƙuwar dake tsakinsu, cikin raunin Murya tace ,"Allah ya jikanka da Rahama Abdulmalik!! Allah yasa ka huta" "Amin Abba da Dr suka amsa mata. Abba da duk jikinsa yay sanyi godiya sosai sukaima Doctor Tare da tabbatar masa insha Allahu a wannan karon zasuyi abinda ya dace. Yaji daɗin hakan sosai. Ya sake ɗan musu wasu bayanan da suka dace akan yanayin kula da Sultana. Godiya sukai masa sosai, sannan suka fito. Ɗakin da aka Kwantar da Sultana suka shiga Sultana dake barci suka bar Kaka, sanin halinta koda Ance taje gida bazata yadda ba, hakan yasa suka wuce gida, koda suka iso gida Haydar Meena Khalil Nana duk suna zaune a Palon kallo ɗaya zaka musu ka fahimci suna cikin damuwa, lokacin da Abba ya shigo ya tabbatar musu Sultana tana cikin kwacin lafiya, hakan yasa suka wuce ɗaki.. ___________★★★ Sultan dake kwance idanu a lumshe, hannunsa har yanzu dafe yake da kansa. Yama rasa wane kalar tunani ya dace yayi akan matsalarnan . Abinda ya aikatama Sultana. awannan dare haka ya kwana cikin mawuyacin hali saboda wani azabebben yanayi dake damunsa sai. Wajajen ƙarfe Huɗu wani irin bacci mai shegen daɗi ya ɗauke sa. Washe gari tunda safe Abba ya wuce Asbiti tare da Breakfast ɗin su, Alhamdulillahi koda ya shiko ɗaki jikinta da sauƙi sosai, Office ɗin Dr ya wuce, bai jima ba ya dawo. ya maida hankali ga Sultana da Kaka take lallaɓawa taci abinci amma sai shagwaɓa take ita ta ƙoshi. Ya ɗan murmusa tare da kamo hannunta cikin nashi. “Mamana daure kici ko kaɗanne kinji, inba hakaba fa kinsan Doctor yace allura zai miki, idan kuma kin fison allurar to sai a kirashi kawai”. Da sauri ta shiga girgiza kanta idanunta cike da ƙwalla. “Abba dan Allah a'a banaso”. "To ki daure kici abincin sai kisha magani ki kwanta ki huta. Kinga kince dama kanki na ciwo har yanzu, Doctor kuma yace kina buƙatar hutune sosai" Kanta ta sake jinjina masa. kaka da batace musu komaiba taci gaba da bata Abinci Batafi spoon huɗu ba su tace ta ƙoshi, kwanan Sultana Huɗu a Asbitin aka sallamesu... Alhamdulillah jikinta yayi ƙyau sosai, sai dai haɗarin da Doctor ya tabbatarma iyayenta tana a ciki akan iya fuskantar loosing mamory shine ya jefasu a cikin tsananin damuwa. a ɓangaren Sultana sam bata son mike faruwa ba, Lokacin da suka dawo Mami ta taimaka mata tayi Wonka, saboda Kaka ma na bukatar Hutu, taci abinci da magungunanta ta kwanta danta huta. Sosai Sultana ta yi barci Kiran