← Book details Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 54

Sashe 41

Dr Sultan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

nufi wajensa da saurin ya gaida shi cikin girmamawa, bayan sun gaida Daddy ya yi mai bayanin Sultan ba lafiya, Tare suka wuce can gida, koda suka iso Ana kiran Sallah, Saida sukayi sallah kana Daddy ya yi mishi jakora zuwa ɗakin Sultan, yadda Daddy ya barsa kwance haka suka tarar dashi. Dr Aryan ya fara dubasa. gyaran murya Dr Aryan yayi tare da cewa,"ciwon Mara ke damunsa,"Daddy Dr Sultan na fama da matsananciyar Sha'awa!" Yanzu ma itace ta motsa" idan har aka bar shi da wannan sha'awar zai iya zame masa matsala zata iya jefashi acikin damuwa. Daddy ko sai kallon Dr Aryan yake. A hankali Daddy ya sauke Nannauyan Numfashi kana sannan ya ce,"Miye mafita yanzu?" "Mafita ɗaya ce yanzu Daddy kawai yayi ƙoƙari yayi aure”. Nannauyan Ajiyar zuciya Daddy ya sauƙe tare da cewa. "In sha Allahu zamu yi ƙoƙarin mu" Magani Dr Aryan ya rubuta Mishi kana ya miƙama ,"ga wannan ya yi ƙoƙari yasha su kafin zuwa safe, a samu ruwan ɗumi a masa laimun tsami da zuma a bashi ya sha.. godiya sosai Daddy ya yiwa Dr Aryan har bakin mota ya rakashi..bayan ta fiyarshi Mommy ta kalli cike da damuwa tace ," mike damun sa?" "Je ki daɗo min Lipton da Lemun tsami ki saka zuma kaɗan" da sauri Mommy ta wuce Kicin, jim kaɗan ta dawo hannunta ɗauke da Mug sai tururi yake, Daddy ya ƙarɓa ya wuce ɗakin Sultan. da taimakon Daddy Sultan ya sha ruwan Lipton ɗin nan take Zufa ta riƙa tsastafo mishi, Atake yafara jin abinda ke damunsa na sauƙa kaɗan-kaɗan ahankali yaji lips ɗin sa ya daina rawan zamewa yayi ya kwanta akan gadon yana sakin Ajiyar zuciya.. ya kallesa ya yi Murmushi kana ya fice daga ɗakin. Sai wuraren ƙarfe ɗaya Sultan ya farki, da sauri ya nufi toilet ya watsa ruwa ya yi Alwala kana ya fito, Sallah Maggariba da Isha'i ya yi da bai samu damar ya ba. Washegari sosai ya ji sauƙi...wuraren ƙarfe Goma ya wuce Office, sai shidda ya dawo, haka suka ci gaba da wasan buya shida Sultana... Bayan Sati ɗaya, Bayan Isha'i Suna zaune a Palo Sultan na zaune kusa Mommy, Daddy ya yi gyaran Murya tare da kallon Sultan," My boy! Mun gama yanke shawara da nida Aminina, ya kuma mallakama Sultana halak malak don haka ku dai daita tsakinin ku" Tunda Daddy ya fara magana, gaban Sultan ke daɗuwa, Mommy ko sai murmushi take . "Ya Naji baka ce komi ba ?" "Duk yadda kace haka za'ayi Daddy" "Good haka neke son ji, mun riga da mun gama magana da Mahaifinta, ko wanne lokaci zaka iya zuwa, Allah ya tabbatar da Alheri," Amin Mommy ta faɗa cikin tsananin farin ciki... A ɓangaren Abba tuni ya sanar da su Mami da Kaka halin da ake ciki, sosai kuma sukayi farin ciki, musamman Kaka, saboda Sultan ya kwanta mata a rai sosai duk da bata taɓa ganin sa ba, Abba ya so A sanar da Sultana komi Amman kaka ta hana shi, a cewar a yiwa Sultana ba zata... Yau ta kasance Friend Tunda safe, Massege ɗin Nas ya tashi Sultana daga barci. *Aminci Allah ya tabbata a gare ki yake ma'abociyar kyau, da kuma kyawun sura burin zuciya ta kasance dake, duk wanda ya samu mace tamkar ya dace, kece mai ɗebin min kewa kece mai Shogoɓa Ni,kece farin ciki na, kin kasance komai a rayuwanah Sonki ya mamaye Zuciyarta cikikar burkina shine ki zamo uwar ya yana Sonki ya mamaye Zuciyarta ba zan iya rayuwa idon har ba keba ki riƙe min Alƙawari ki zamo jigo a rayuwata Good Morning my Hubby, I love you so much 💋👩‍❤️‍💋‍👩* Wani irn murmushi ta saki.tare da sumbatar wayar. *Kayar dani my Hubby Babu wani da zai kwace Zuciyata, domin Zuciyata ta kece har Abada Idanuwana kai kaidai suke kallo a matsayin Abokin rayuwata in son ka! Ina kyaunar ka da fatan ka tashi Lafiya Hubbyna i love you so much 💋* (Hmmm🤣🤣🤐) ★★★ tsananin mamaki ta kalli Mami da tuni ta bar wajen, Baƙo ta faɗa a hankali.. tsawon lokaci Sultana na zaune tana maimai ta kalmar baƙo a ranta,tana zaune a wajen har Abba ya fito," Wai zaman me kike anan,"firgit ta mike tsaye tare da barin Palon kai tsaye ta wuce palon Abba...✍️ ( Oh ni Halimatu ko ya za'a tarbi baƙo oh ho 🥲🤣🤣) _More Comments and share pls_ *Sadeeya Ka'oje ce*💋✍️ *DR SULTAN* (A heart touching love story)
Chapter 41 · 0% Book details